{"id":2358,"date":"2025-01-22T14:40:17","date_gmt":"2025-01-22T14:40:17","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2358"},"modified":"2025-01-22T14:41:19","modified_gmt":"2025-01-22T14:41:19","slug":"gwamnatin-jigawa-za-ta-bada-lamunin-sama-da-naira-biliyan-3-ga-hukumar-alhazan-jihar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jigawa-za-ta-bada-lamunin-sama-da-naira-biliyan-3-ga-hukumar-alhazan-jihar\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jigawa Za Ta Bada Lamunin Sama Da Naira Biliyan 3 Ga Hukumar Alhazan Jihar"},"content":{"rendered":"<p>Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da bukatar hukumar Alhazai ta jihar na naira biliyan uku da miliyan dari uku da sittin a matsayin lamuni daga gwamnatin jihar.<\/p>\n<p>Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al\u2019adu na jihar Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, bayan kammala taron majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa,\u00a0 majalisar ta amince da hakan ne don bai wa hukumar damar ajiyar kujeru 400 na maniyyatan jihar Jigawa domin gudanar da ayyukin\u00a0 Hajjin shekarar 2025.<\/p>\n<p>A cewarsa, amincewar ta biyo bayan\u00a0 gamsuwar da Majalisar ta yi, bisa yadda hukumar Alhazai ta Jiha ta mayar da bashin Naira biliyan biyu da miliyan dari biyu da gwamnatin ta bata a shekarar 2024.<\/p>\n<p>Haka zalika Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce majalisar ta amince da shigar da dukkan masu rike da mukaman siyasa a cikin shirin kula da liyafa na jihar, kamar yadda hukumar kula da lafiya ta jihar Jigawa\u00a0 JICHMA ta tanadar\u00a0 a doka mai lamba. 02 -2024, da nufin inganta harkokin kiwon lafiya a jihar da ma Najeriya baki daya kamar yadda sakataren gwamnatin jihar ya gabatar.<\/p>\n<p>Ya ce majalisar ta kuma bada goyon baya ga amincewar da Gwamna Umar Namadi ya yi, na sakin Naira Miliyan Dari Biyu da Hamsin a matsayin wani asusun hadin gwiwa da hukumar UNICEF domin siyan kayan abinci mai gina jiki ga kananan yara marasa lafiya.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa, amincewar kuma wani bangare ne na kokarin gwamnatin Namadi na yaki da matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara a jihar, kamar yadda ma\u2019aikatar lafiya ta gabatar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da bukatar hukumar Alhazai ta jihar na naira biliyan uku da miliyan dari uku da sittin a matsayin lamuni daga gwamnatin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al\u2019adu na jihar Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, bayan kammala [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":2360,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[118,59,620],"class_list":["post-2358","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hukumar-alhazai","tag-jigawa","tag-majalisar-zartaswa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250122-WA0003.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2358","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2358"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2358\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2361,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2358\/revisions\/2361"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2360"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2358"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2358"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2358"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}