{"id":2355,"date":"2025-01-22T12:26:44","date_gmt":"2025-01-22T12:26:44","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2355"},"modified":"2025-01-22T12:26:44","modified_gmt":"2025-01-22T12:26:44","slug":"an-tsinci-gawar-wani-mutum-a-cikin-rijiya-a-karamar-hukumar-gezawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-tsinci-gawar-wani-mutum-a-cikin-rijiya-a-karamar-hukumar-gezawa\/","title":{"rendered":"An Tsinci Gawar Wani Mutum A Cikin Rijiya A Karamar Hukumar Gezawa"},"content":{"rendered":"<p>Al\u2019ummar kauyen Babawa da ke karamar hukumar Gezawa a Kano sun shiga cikin firgici bayan da aka tsinci wani mutum mai kimanin shekaru 45 a cikin rijiya.<\/p>\n<p>Saminu Yusif Abdullahi jami\u2019in hulda da jama\u2019a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa hukumar ta samu kiran gaggawa daga ASP Kabiru Lawan na rundunar \u2018yan sandan Gezawa.<\/p>\n<p>Saminu ya yi nuni da cewa, tawagar ceto ta yi nasarar zakulo mutumin daga rijiyar kuma daga bisani jami\u2019an lafiya suka tabbatar da mutuwarsa.<\/p>\n<p>Sai dai, ya jaddada cewa, har yanzu ba a san ko wanen ba, saboda shugabannin al\u2019umma da mazauna yankin sun ce ba su gane shi ba, ba su kuma san daga inda ya fito ba.<\/p>\n<p>Hakazalika, mutane uku sun makale a lokacin da suke aikin hako rijiya a kauyen Gargajiga da ke karamar hukumar Minjibir.<\/p>\n<p>Saminu ya kara da cewa hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto mutum biyu da ransu, yayin da aka dauko mutum na uku Yusuf Nadabo mai shekaru 50 da haihuwa, a sume, daga bisani kuma aka tabbatar da mutuwarsa.<\/p>\n<p>Jami\u2019in hulda da jama\u2019an ya yi nuni da cewa, wani iftila&#8217;in ya sake afkuwa a Kano inda wata mummunar gobara ta kona shaguna da dama a kan titin Ibrahim Taiwo, inda aka ciro wani mutum a sume, yayin da aka yi asarar dukiyoyi na miliyoyin naira.<\/p>\n<p><em>Daga Khadija Aliyu<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Al\u2019ummar kauyen Babawa da ke karamar hukumar Gezawa a Kano sun shiga cikin firgici bayan da aka tsinci wani mutum mai kimanin shekaru 45 a cikin rijiya. Saminu Yusif Abdullahi jami\u2019in hulda da jama\u2019a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin. Ya bayyana cewa hukumar ta samu kiran gaggawa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1648,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[699,700,39],"class_list":["post-2355","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-gezawa","tag-iftilai","tag-kano"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Kano-Map.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2355","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2355"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2355\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2356,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2355\/revisions\/2356"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1648"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2355"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2355"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2355"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}