{"id":2213,"date":"2025-01-08T20:12:00","date_gmt":"2025-01-08T20:12:00","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2213"},"modified":"2025-01-08T20:12:00","modified_gmt":"2025-01-08T20:12:00","slug":"za-a-yi-gyaran-cibiyoyin-kiwon-lafiya-144-a-jihar-zamfara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/za-a-yi-gyaran-cibiyoyin-kiwon-lafiya-144-a-jihar-zamfara\/","title":{"rendered":"Za A Yi Gyaran Cibiyoyin Kiwon Lafiya 144 A Jihar Zamfara"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar sauran abokan hulda za su fara aikin gyaran cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 144 a fadin jihar domin inganta harkar kiwon lafiya.<\/p>\n<p>Shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jihar, Dakta Husaini Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyar lafiya\u00a0 ta Yandoton a karamar hukumar Tsafe.<\/p>\n<p>Dakta Yakubu ya ce makasudin ziyarar tasa ita ce duba halin da cibiyar ke ciki, domin inganta kayan aiki, da fadadata.<\/p>\n<p>A cewarsa, aikin gyaran cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko zai kasance na hadin gwiwa ne, yana mai jaddada cewa, shirin\u00a0 zai gyara cibiyoyin kiwon lafiya 62, yayin da hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Zamfara za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 4, sannan za a gyara cibiyoyi 18 a karkashin aikin mazabu na jihar.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa, hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa (NPHCDA) za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 11 da sauransu.<\/p>\n<p>Dakta Yakubu ya yi gargadin cewa ba za a amince da rashin zuwan ma\u2019aikata ba, yana mai cewa duk wanda ba zai iya bi ba to ya yi murabus, saboda mutane da yawa suna sha\u2019awar shiga aikin gwamnati.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa, daga yanzu duk jami\u2019in da aka samu da sakaci zai fuskanci hukuncin ladabtarwa.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da jami\u2019in yada labarai na ma\u2019aikatar lafiya ta kasar Sulaiman Isah ya fitar, ya mika godiyarsa ga Gwamna Dauda Lawal bisa goyon bayan da yake baiwa bangaren kiwon lafiya na jihar sannan ya yabawa kwamishinar lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun bisa jagorancinta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Aminu Dalhatu<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Gwamnatin Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar sauran abokan hulda za su fara aikin gyaran cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 144 a fadin jihar domin inganta harkar kiwon lafiya. Shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jihar, Dakta Husaini Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyar lafiya\u00a0 ta [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":2214,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[644,115],"class_list":["post-2213","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-cibiyoyin-kiwon-lafiya","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/New-Project-2022-06-07T161104.246.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2213","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2213"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2213\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2215,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2213\/revisions\/2215"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2214"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2213"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2213"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2213"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}