{"id":219,"date":"2024-02-29T22:31:23","date_gmt":"2024-02-29T22:31:23","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=219"},"modified":"2024-02-29T22:31:23","modified_gmt":"2024-02-29T22:31:23","slug":"an-kashe-jagoran-yan-adawar-chadi-yaya-dillo","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-kashe-jagoran-yan-adawar-chadi-yaya-dillo\/","title":{"rendered":"An Kashe Jagoran &#8216;Yan Adawar Chadi Yaya Dillo"},"content":{"rendered":"<p>Hukumomin kasar Chadi sun tabbatar da mutuwar daya daga cikin shugaban \u2018yan adawa Yaya Dillo bayan wani samame da jami\u2019an tsaro suka kai ofishin jam\u2019iyyarsa a jiya, wanda ya jefa mazauna birnin Ndjamena cikin fargaba da tashin hankali.<\/p>\n<p>Mai gabatar da kara na gwamnatin Chadi Oumar Mahamat Kedelaye ya tabbatar da mutuwar shugaban \u2018yan adawar a yau Alhamis, bayan artabun da akayi jiya.<\/p>\n<p>Mutuwar Dillo na zuwa ne bayan da gwamnatin kasar ta zargi jam&#8217;iyyarsa da kai wani mummunan hari kan hukumar tsaron kasar, lamarin da ya musanta shi kai tsaye a jiya Laraba.<\/p>\n<p>Harin da aka kai kan hukumar tsaron ya zo ne bayan da aka kama wani \u2018dan jam\u2019iyyarsa ta PSF tare da zargin sa da yunkurin kisan shugaban kotun kolin kasar.<\/p>\n<p>A jiya Laraba ne aka ji karar harbe-harbe a kusa da hedikwatar jam\u2019iyyarsa da ke N&#8217;Djamena babban birnin kasar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan na zuwa ne kwana guda da gwamnatin Chadi ta sanar cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 6 ga watan Mayu, inda shugaba Mahamat da Dillo za su fafata da juna.<\/p>\n<p>Mahamat dai ya dare kan karagar mulki ne bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno wanda ya rasa ransa a yayin fafatawa da &#8216;yan tawaye a 2021, yayin da ya shafe kimanin shekaru 30 yana mulkar kasar kafin ajalinsa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Har ya zuwa wannan lokaci mazauna babban birnin kasar na cikin fargaba dangane da abin da ka iya je ya komo, sakamakon arangamar ta jiya da kuma mutuwar shugaban \u2018yan adawa<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumomin kasar Chadi sun tabbatar da mutuwar daya daga cikin shugaban \u2018yan adawa Yaya Dillo bayan wani samame da jami\u2019an tsaro suka kai ofishin jam\u2019iyyarsa a jiya, wanda ya jefa mazauna birnin Ndjamena cikin fargaba da tashin hankali. Mai gabatar da kara na gwamnatin Chadi Oumar Mahamat Kedelaye ya tabbatar da mutuwar shugaban \u2018yan adawar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":220,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,12],"tags":[81,82],"class_list":["post-219","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-ketare","tag-chadi","tag-kisan-yaya-dillo"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/000_9937KV.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/219","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=219"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/219\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":221,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/219\/revisions\/221"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/220"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=219"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=219"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=219"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}