{"id":216,"date":"2024-02-29T13:21:49","date_gmt":"2024-02-29T13:21:49","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=216"},"modified":"2024-02-29T13:21:49","modified_gmt":"2024-02-29T13:21:49","slug":"zulum-ya-kaddamar-da-rabon-kayan-abinci-ga-iyalai-dubu-dari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/zulum-ya-kaddamar-da-rabon-kayan-abinci-ga-iyalai-dubu-dari\/","title":{"rendered":"Zulum Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Abinci Ga Iyalai Dubu Dari"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kaddamar da rabon kayan abinci ga iyalai musu rauni sama da dubu dari daya a kananan hukumomin Maiduguri\u00a0 da Jere.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An yi rabon ne da nufin rage wahalhalun\u00a0 tsadar kayan abinci da sauran muhimman kayayyakin amfanin yau da kullun.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A jawabinsa yayin kaddamar da rabon kayayyakin a cibiyar wasanni ta Maiduguri, Gwamna Zulum ya ce kowane gida zai sami buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25 da buhun masara shi ma mai nauyin kilogiram 25.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa ta ba da fifiko ga jin dadi da walwalar jama\u2019a, musamman wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.<\/p>\n<p>\u201c<em>Mun kaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta dubu dari ne daga birnin\u00a0 Maiduguri da kewaye. Kowa a Najeriya ya san irin wahalhalun da mutane ke fuskanta dangane da karancin abinci,\u201d In ji Zulum<\/em>.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewar Gwamnan, za a raba kayayyakin ne ga masu karamin karfi a cikin al\u2019umma domin rage radadin tsadar rayuwa da ake fuskanta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a kara yawan rabon tallafin daga iyalai dubu dari zuwa sama da iyalai dubu dari biyu a kananan hukumomi bakwai dake kudancin jihar kafin karshen azumin watan Ramadan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kara da cewa, \u201c<em>Muddin ni ne gwamnan jihar Borno, za a ci gaba da rabon kayayyakin jin kai. Duk da haka, ina so in jaddada cewa yayin da ake ci gaba da rabon kayan abinci, za mu ci gaba da bada tallafi harkar kasuwanci da noma\u201d.<\/em><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bukaci al\u2019ummar jihar da su himmatu wajen aikin noma don bunkasa samar da abinci, tare da ba da tabbacin samar da karin ababen more rayuwa da suka hada da shiga motocin bas kyauta, da kayan aikin gona da tallafin kudi don farfado da tattalin arzikin jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daga Dauda Iliya<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kaddamar da rabon kayan abinci ga iyalai musu rauni sama da dubu dari daya a kananan hukumomin Maiduguri\u00a0 da Jere. &nbsp; An yi rabon ne da nufin rage wahalhalun\u00a0 tsadar kayan abinci da sauran muhimman kayayyakin amfanin yau da kullun. &nbsp; A jawabinsa yayin kaddamar da rabon [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":217,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[53,80,79,78],"class_list":["post-216","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-borno","tag-iyalai-dubu-dari","tag-tallafin-kayayyakin-abinci","tag-zulum"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/IMG-20240229-WA0003.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/216","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=216"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/216\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":218,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/216\/revisions\/218"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/217"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=216"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=216"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=216"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}