{"id":2124,"date":"2025-01-02T21:26:46","date_gmt":"2025-01-02T21:26:46","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2124"},"modified":"2025-01-02T21:26:46","modified_gmt":"2025-01-02T21:26:46","slug":"an-kaddamar-da-kwamatin-inganta-ayyukan-samar-da-jini-ga-marasa-lafiya-a-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-kaddamar-da-kwamatin-inganta-ayyukan-samar-da-jini-ga-marasa-lafiya-a-kano\/","title":{"rendered":"An Kaddamar Da Kwamatin Inganta Ayyukan Samar Da Jini Ga Marasa Lafiya A Kano"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin kwararru na jihar kan batun karin jini domin magance gibi da kalubalen da ke tattare da ayyukan karin jini.<\/p>\n<p>Babban manufar kwamitin ita ce tabbatar da yin \u0199arin lafiyayyen jini fa marasa lafiya a jihar.<\/p>\n<p>Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya kaddamar da kwamitin, inda ya bayyana cewa kafa kwamitin na da matukar muhimmanci wajen kare kamuwa da wata cuta sakamakon karin jini.<\/p>\n<p>Ya kuma jaddada cewa an zabi \u2018yan kwamitin ne bisa cancanta da kwarewarsu.<\/p>\n<p>Kwamitin yana da alhakin samar da kwararru masana kula da lafiyar jini, da masu bada shawarwari kan lamarin, da ha\u0257in gwiwa tare da masu ruwa da tsaki don ha\u0253aka ayyukan \u0199arin jini.<\/p>\n<p>Kwamitin ya \u0199unshi wakilai daga cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban, wa\u0257anda suka ha\u0257a da Hukumar Kula da Asibitoci, da\u00a0 Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya Masu Zaman Kansu, da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko, da Hukumar Samar da Magunguna.<\/p>\n<p>Hakavkuma akwai wakilai daga cibiyoyin ilimi, kamar Jami\u2019ar Bayero Kano da Asibitin koyarwa na Aminu Kano.<\/p>\n<p>Sakatariyar kwamitin, Dokta Hauwa Ibrahim, kwararra kan al&#8217;amuran da suka shafijini, za ta kasance mai bada shawarwari ga kwamitin.<\/p>\n<p>Kwamitin yana da &#8216;yancin yin ha\u0257in gwiwa tare da \u0199arin masu ruwa da tsaki kamar yadda ake bu\u0199ata.<\/p>\n<p>Kaddamar da kwamatin wani muhimmin mataki ne na inganta ayyukan samar da jini a jihar Kano, tare da tabbatar da tsaro da jin dadin majinyatan da aka yi musu karin jini.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daga Khadija Aliyu<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin kwararru na jihar kan batun karin jini domin magance gibi da kalubalen da ke tattare da ayyukan karin jini. Babban manufar kwamitin ita ce tabbatar da yin \u0199arin lafiyayyen jini fa marasa lafiya a jihar. Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya kaddamar da kwamitin, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":2125,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[39,616,615],"class_list":["post-2124","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-kano","tag-karin-jini","tag-kwamati"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250102-WA0014.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2124","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2124"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2124\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2126,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2124\/revisions\/2126"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2125"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2124"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2124"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2124"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}