{"id":1937,"date":"2024-06-18T19:42:27","date_gmt":"2024-06-18T19:42:27","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1937"},"modified":"2024-06-18T19:42:27","modified_gmt":"2024-06-18T19:42:27","slug":"karamar-hukumar-kauru-ta-raba-kayayyakin-abinci-na-miliyoyin-naira-ga-marasa-galihu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/karamar-hukumar-kauru-ta-raba-kayayyakin-abinci-na-miliyoyin-naira-ga-marasa-galihu\/","title":{"rendered":"Karamar Hukumar Kauru Ta Raba Kayayyakin Abinci Na Miliyoyin Naira Ga Marasa Galihu"},"content":{"rendered":"<p>A kokarin da take na inganta rayuwar al\u2019umma, Majalisar Karamar Hukumar Kauru da ke Jihar Kaduna ta raba kayayyakin abinci na\u00a0 miliyoyin Naira ga marasa galihu.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da jami\u2019in yada labarai na majalisar Alhaji Sani Yahaya ya fitar, ya ce an shirya wannan karamcin ne da nufin rage matsalolin tattalin arziki da mazauna yankin ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi a baya-bayan nan, wanda ya haifar da tashin gwauron zabin farashin kayayyakin abinci.<\/p>\n<p>Shugaban karamar hukumar Alhaji Bashir Tanko Dawaki ne ya kaddamar da rabon kayayyakin a hukumance a Kauru.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa an zabo wadanda suka ci gajiyar shirin ne daga sassan kananan hukumomin domin tabbatar da ganin wadanda suka cancanta ne suka amfana, tare da yin rabon bisa adalci.<\/p>\n<p>Alhaji Bashir Tanko Dawaki ya bukaci masu ruwa da tsaki wajen rabon kayan abinci da su tabbatar da adalci, don ganin tallafin ya isa ga wadanda suka cancanta a gundumomi\u00a0 goma sha daya da ke yankin.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-1939\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240618-WA0017-300x169.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"169\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240618-WA0017-300x169.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240618-WA0017-1024x576.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240618-WA0017-768x432.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240618-WA0017.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ya kuma yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, bisa kokarin da ta yi wajen bullo da shirye-shirye da ayyukan da ke da tasiri ga rayuwar aal\u2019umma.<\/p>\n<p>Shugaban ya shawarci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kayan abinci yadda ya kamata, ya kuma yi kira ga wadanda ba su samu ba a wannan karon da su yi hakuri, domin za a\u00a0 kara wani rabon nan gaba kadan.<\/p>\n<p>Wadanda suka ci gajiyar shirin sun nuna jin dadinsu ga majalisar karamar hukumar bisa wannan karamci.<\/p>\n<p>Sun yi alkawarin bayar da goyon bayansu ga gwamnati mai ci, tare da yi mata addu\u2019ar samun nasara.<\/p>\n<p>An raba buhunan abinci daban daban guda 886 da suka hada da masara, gero, da dawa, inda aka bada fifiko ga mata da masu rauni a cikin al&#8217;umma.<\/p>\n<p>Wannan kokarin da karamar hukumar Kauru ta yi ya jaddada kudirinta na tallafa wa marasa galihu domin rage radadin matsin rayuwa da ya addabi al&#8217;umma.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Yusuf Zubairu<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A kokarin da take na inganta rayuwar al\u2019umma, Majalisar Karamar Hukumar Kauru da ke Jihar Kaduna ta raba kayayyakin abinci na\u00a0 miliyoyin Naira ga marasa galihu. A cikin wata sanarwa da jami\u2019in yada labarai na majalisar Alhaji Sani Yahaya ya fitar, ya ce an shirya wannan karamcin ne da nufin rage matsalolin tattalin arziki da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1938,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,10],"tags":[553,552,59,554,555],"class_list":["post-1937","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma","tag-burtalai","tag-dazukan-gwamnati","tag-jigawa","tag-karamar-hukumar-kauru","tag-tallafin-abinci"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240618-WA0016.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1937","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1937"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1937\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1940,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1937\/revisions\/1940"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1938"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1937"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1937"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1937"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}