{"id":1871,"date":"2024-06-08T11:59:15","date_gmt":"2024-06-08T11:59:15","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1871"},"modified":"2024-06-08T11:59:15","modified_gmt":"2024-06-08T11:59:15","slug":"mahajjata-sun-yabawa-gwamnatin-borno-da-hukumar-alhazai-bisa-basu-abinci-mai-inganci","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/mahajjata-sun-yabawa-gwamnatin-borno-da-hukumar-alhazai-bisa-basu-abinci-mai-inganci\/","title":{"rendered":"Mahajjata Sun Yabawa Gwamnatin Borno Da Hukumar Alhazai Bisa Basu Abinci Mai Inganci"},"content":{"rendered":"<p>Alhazan Jihar Borno\u00a0 sun yabawa hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) da gwamnatin jihar Borno bisa kyakkyawan tsarin shirin ciyarwa\u00a0 a\u00a0 Makka da Madina.<\/p>\n<p>Alhazan da a halin yanzu suke shirin fara aikin Hajji a ranar Juma\u2019a ta makon gobe, sun bayyana gamsuwarsu da inganci da wadataccen abinci da ake basu a kullum.<\/p>\n<p>Wakilinmu Dauda Iliya wanda yanzu haka yake a garin Makka ya ruwaito cewa Alhazai 1,646 daga cikin 1,815 daga jihar sun kammala zamansu a Madina bayan sun yi ziyara a muhimman wurare.<\/p>\n<p>Daya daga cikin mahajjatan\u00a0 Hajia Fatima Usman ta ce ana basu abincin\u00a0 mai gina jiki kuma irin wanda suka saba da shi.<\/p>\n<p>\u201c<em>Abincin da muke samu tun daga Madina zuwa nan Makka yana da kyau kwarai da gaske, muna jin dadin yadda ake bamu abincinmu na gargajiya da muka saba da shi, muna godiya ga Hukumar NAHCON da Gwamnatin Jihar Borno da suka tabbatar mana da samun wadataccen abinci a wannan lokacin<\/em>.&#8221; in ji Hajiya Fatima.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-1872\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240608-WA0007-300x135.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"135\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240608-WA0007-300x135.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240608-WA0007-1024x461.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240608-WA0007-768x346.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240608-WA0007.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Wani Alhaji mai suna Malam Abba Kyari, ya yabawa jami\u2019an kwamitin ciyar da abinci da masu ba da abinci bisa kwarewa da kuma kula da Alhazai.<\/p>\n<p>Kyari ya ce &#8220;<em>Ma&#8217;aikatan da ke kula da abinci suna matukar bibiyar bukatunmu da korafe-korafenmu, idan akwai. Suna tabbatar da cewa an ba mu abinci a kan lokaci<\/em>&#8220;.<\/p>\n<p>Shugaban kwamitin ciyarwa\u00a0 na tawagar Amirul Hajj Dr Ibrahim Adam ya bayyana jin dadinsa bisa yabon da Alhazan\u00a0 ke yi, yana mai cewa hakan ya nuna irin jajircewar da gwamnatin jihar ta yi na kyautata rayuwar jami&#8217;ar ta da suke gudanar da aikin Hajjin.<\/p>\n<p>Dangane da korafin da wasu maniyyatan ke yi na rasa abincin, Dr Ibrahim ya ce kwamitin ya bukaci masu kula da abincin da su kara samar da wadataccen abincin a lokacin karin kumallo da kuma abincin dare domin tabbatar da cewa\u00a0 kowa ya samu.<\/p>\n<p>\u201c<em>Abin da muka sa a gaba shi ne tabbatar da kula da mahajjatan mu a yayin wannan tafiya ta ibada. Yabo daga alhazan Borno ya nuna cewa muna kan turbar da ta dace, kuma za mu ci gaba da hada hannu da NAHCON wajen tabbatar da wannan tsari,<\/em>\u201d in ji Dokta Ibrahim.<\/p>\n<p>Wakilinmu ya ruwaito cewa, ana sa ran za a yi jigilar alhazan jihar Borno na karshe a kasa mai tsarki nan da kwanaki biyu masu zuwa.<\/p>\n<p><strong><em>Dauda Iliya<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Alhazan Jihar Borno\u00a0 sun yabawa hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) da gwamnatin jihar Borno bisa kyakkyawan tsarin shirin ciyarwa\u00a0 a\u00a0 Makka da Madina. Alhazan da a halin yanzu suke shirin fara aikin Hajji a ranar Juma\u2019a ta makon gobe, sun bayyana gamsuwarsu da inganci da wadataccen abinci da ake basu a kullum. Wakilinmu Dauda Iliya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1873,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[53,382],"class_list":["post-1871","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-borno","tag-hajji"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/IMG-20240608-WA0008.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1871","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1871"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1871\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1874,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1871\/revisions\/1874"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1873"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1871"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1871"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1871"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}