{"id":1786,"date":"2024-05-30T21:20:54","date_gmt":"2024-05-30T21:20:54","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1786"},"modified":"2024-05-30T21:20:54","modified_gmt":"2024-05-30T21:20:54","slug":"gwamna-dauda-na-gwangwaje-zamfarawa-da-ayukka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-dauda-na-gwangwaje-zamfarawa-da-ayukka\/","title":{"rendered":"Gwamna Dauda Na Gwangwaje Zamfarawa Da Ayukka"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa ayyukan samar wa al&#8217;umma mafita da gwamnatinsa ke yi na samun tagomashi sosai, kuma an samu gagarumin sakamako cikin shekara guda.<\/p>\n<p>Gwamnan ya \u0199addamar da manyan ayyuka a \u0198ananan Hukumomi takwas, wanda aka fara a \u0198aramar Hukumar Gummi a ranar Lahadi, 27 ga watan Mayu.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu a Gusau ranar Alhamis \u0257in nan, ya bayyana cewa an \u0199addamar da wasu ayyuka hu\u0257u a babban birnin jihar, Gusau da \u0198aramar Hukumar \u0198auran Namoda.<\/p>\n<p>A sanarwar ta ce, gwamnatin Dauda Lawal ta \u0199addamar da \u0257aya daga cikin ayyukan tituna a Gusau: gyaran sakatariyar J.B. Yakubu ta jihar da kuma makarantar Tsangaya ta zamani da ke \u0198ananan Hukumomin Gusau da \u0198auran Namoda.<\/p>\n<p>\u201cA ranar Talata, 28 ga watan Mayu, Gwamna Dauda Lawal ya \u0199addamar da babbar hanyar da ta ha\u0257a shataletalen UBA zuwa Freedom Square da ke \u0199waryar garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.<\/p>\n<p>\u201cHanyar wani \u0253angare ne na aikin sabunta biranen da gwamnatin ke ci gaba da yi, kuma Ambasada Umar Iliya Damagum, mu\u0199addashin shugaban jam\u2019iyyar PDP na \u0199asa ne ya \u0199addamar da shi.<\/p>\n<p>A ranar Talata, 28 ga watan Mayu ne Gwamna Lawal ya \u0199addamar da Makarantar Tsangaya ta zamani a \u0198auran Namoda.<\/p>\n<p>\u201cMakarantar Tsangaya da ke Kauran Namoda ce za ta \u0257auki nauyin kula da yankin Zamfara ta Arewa, bayan kwana biyu da \u0199addamar da wata a Gummi, da nufin yi wa al\u2019ummar maza\u0253ar Zamfara ta Yamma hidima. Makarantar Tsangaya ta uku kuma tana Gusau ne a gundumomin Zamfara ta tsakiya.\u201d<\/p>\n<p>A jiya, 29 ga watan Mayu, Gwamna Lawal ya \u0199addamar da wani muhimmin aiki, ginin Sakatariyar J. B. Yakubu, wadda ita ce babbar sakatariyar gwamnatin jihar Zamfara.<\/p>\n<p>Da yake gabatar da jawabinsa a wajen bikin ranar 29 ga watan Mayu, Gwamna Lawal ya jaddada cewa a cikin watanni 12 da suka gabata gwamnatinsa ta samu ci gaba sosai. \u201cMun hada \u0199arfi da \u0199arfe wajen ya\u0199i da \u2019yan bindiga da sauran laifuka, mun yi gyara a sassa masu muhimmanci na ilimi, kiwon lafiya, da noma, mun \u0199addamar da ayyukan sabunta birane, da gyara tsarin ma\u2019aikatun gwamnati, da inganta hanyoyin samun ku\u0257a\u0257en shiga a jihar, da kuma samar da ingantaccen tsarin gudanarwa a ma\u2019aikatun gwamnati\u201d.<\/p>\n<p>A lokacin da yake \u0199addamar da Makarantar Tsangaya ta zamani da ke Gusau, Gwamna Lawal ya \u0199ara jaddada cewa, makarantun Tsangaya da aka sabunta, an tsara ta ne domin ha\u0257a abubuwan da suka shafi ilimin zamani na Boko da koyarwar addinin Musulunci a lokaci guda.<\/p>\n<p>\u201cKamar yadda na ambata a Gummi da \u0198aura Namoda, tsarin karatun Tsangaya ta kasance wani \u0253angare na al\u2019adunmu shekaru aru-aru. Ta kasance tushen ilimi da tarbiyya a cikin al&#8217;ummomin Musulmi a arewacin Nijeriya. Kusan kowane yaro \u0257an Musulmi da ya girma a wannan yanki ya sami irin wannan nau&#8217;in ilimi.<\/p>\n<p>\u201cWannan shiri zai taimaka matu\u0199a wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, \u0199alubalen da jihar Zamfara ta samu matsayi mafi girma. Ta hanyar bu\u0257e wa wa\u0257annan yara sabbin damarmaki, muna fatan za mu zaburarwa da yawa daga cikinsu da \u0199warin gwiwar ci gaba da neman ilimi a nan gaba, ta yadda za su inganta rayuwarsu da kuma bayar da gudunmawar ci gaban jiharmu.\u201d<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa ayyukan samar wa al&#8217;umma mafita da gwamnatinsa ke yi na samun tagomashi sosai, kuma an samu gagarumin sakamako cikin shekara guda. Gwamnan ya \u0199addamar da manyan ayyuka a \u0198ananan Hukumomi takwas, wanda aka fara a \u0198aramar Hukumar Gummi a ranar Lahadi, 27 ga watan Mayu. A wata [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":1787,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[506,115],"class_list":["post-1786","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ayukka","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240530-WA0272.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1786","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1786"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1786\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1788,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1786\/revisions\/1788"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1787"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1786"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1786"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1786"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}