{"id":1734,"date":"2024-05-29T05:40:02","date_gmt":"2024-05-29T05:40:02","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1734"},"modified":"2024-05-29T05:40:02","modified_gmt":"2024-05-29T05:40:02","slug":"hajjin-bana-gwamnan-zamfara-ya-kaddamar-da-jigilar-maniyyatan-jihar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hajjin-bana-gwamnan-zamfara-ya-kaddamar-da-jigilar-maniyyatan-jihar\/","title":{"rendered":"Hajjin Bana: Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Jigilar Maniyyatan Jihar"},"content":{"rendered":"<p>Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya kaddamar da jigilar maniyyata kashin farko\u00a0 zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin 2024.<\/p>\n<p>Gwamna Dauda Lawal wanda ya kaddamar da fara gudanar da aikin a sansanin Alhazai na jihar da ke Samaru Gusau, babban birnin jihar, ya kuma yi kira ga alhazan\u00a0 da su\u00a0 bin dokokin Saudiyya sau da kafa, kuma su guji duk wani abu da zai iya bata sunan su da na jiharsu da ma Najeriya\u00a0 baki daya.<\/p>\n<p>Dauda Lawal ya kuma bukace su da su yi amfani da kudaden su yadda ya dace, tare da gujewa sayayya barkatai.<\/p>\n<p>Ya sanar da bayar da kykyautar Dala dari ga kowane mahajjaci daga jihar, inda\u00a0 ya kara da cewa,\u00a0 ita ma mai dakinsa Hajia Huriya Dauda Lawal ta shiryabayar da irin wannan kyauta ga Alhazan.<\/p>\n<p>Gwamnan ya kuma yi kira ga maniyyatan jihar da su yi addu\u2019ar samun dauwamammen zaman lafiya a jihar Zamfara da yankin Arewa da ma Najeriya baki daya.<\/p>\n<p>Tun da farko, a jawabinsa na maraba, Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Zamfara, Malam Musa Mallaha, ya ce maniyyata dubu daya da dari bakwai da sha biyu ne ake sa ran za su yi aikin Hajjin bana.<\/p>\n<p>Jirgin farko na jihar ya kunshi mahajjatan daga kananan\u00a0 hukumomi hudu na jihar wadanda suka hada da Bakura, Bukuyum, Gummi da Shinkafafi, kuma ana sa ran zai tashi daga filin jirgin saman Sultan Abubakar III da sanyin safiyar yau Laraba 29 ga watan Mayu, 2024.<\/p>\n<p><em><strong>Sani Haruna Dutsinma<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya kaddamar da jigilar maniyyata kashin farko\u00a0 zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin 2024. Gwamna Dauda Lawal wanda ya kaddamar da fara gudanar da aikin a sansanin Alhazai na jihar da ke Samaru Gusau, babban birnin jihar, ya kuma yi kira ga alhazan\u00a0 da su\u00a0 bin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1735,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[382,115],"class_list":["post-1734","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hajji","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240529-WA0000.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1734","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1734"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1734\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1736,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1734\/revisions\/1736"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1735"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1734"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1734"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1734"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}