{"id":173,"date":"2024-02-27T13:14:48","date_gmt":"2024-02-27T13:14:48","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=173"},"modified":"2024-02-27T13:17:39","modified_gmt":"2024-02-27T13:17:39","slug":"gwamna-namadi-ya-kaddamar-da-hukumar-yaki-da-cin-hanci-da-rashawa-a-jigawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-namadi-ya-kaddamar-da-hukumar-yaki-da-cin-hanci-da-rashawa-a-jigawa\/","title":{"rendered":"Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Jigawa"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya kaddamar da hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa a jihar.<\/p>\n<p>Yayin jawabinsa a wajen bikin kaddamar da hukumar, Gwamna Umar Namadi ya jaddada mahimmancin\u00a0 hukumar wajen\u00a0 yaki da cin hanci da rashawa domin tsaftace ayyuku a jihar.<\/p>\n<p>Ya kuma bukaci mambobin hukumar da su yi aiki bisa doka ba tare da tsoro ko nuna son kai ba.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Kada ku bari bukatun ku su yi tasiri a ayyukanku, haka kuma babu wanda zai tsoma baki cikin ayyukanku daga bangaren gwamnati.&#8221; Inji Gwamnan<\/strong><\/em><\/p>\n<p>Malam Umar Namadi ya kuma bukaci hukumar da ta kiyaye ka\u2019idojin aiki, tare da yin\u00a0 adalci dm wajen magance korafe-korafen da aka kawo mata.<\/p>\n<p>A jawabinsa, shugaban\u00a0 hukumar Barista Salisu Abdu, ya nuna jin dadinsa ga Gwamna Namadi bisa bashi damar jagorantar hukumar.<\/p>\n<p>Ya kuma tabbatar wa da al\u2019umma kudurin hukumar na tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen gudanar da ayyukanta.<\/p>\n<p>&#8220;<strong><em>Hukumar za ta tabbatar da manufar Gwamna Namadi na samar da sabuwar Jihar Jigawa ba tare da cin hanci da rashawa ba, mun yi alkawarin yin aiki bisa gaskiya da amana ba tare da son zuciya ba.&#8221;<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Gidan Rediyon Najeriya Kaduna ya ruwaito cewa, an dorawa\u00a0 hukumar korafe-korafen al&#8217;umma da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar alhakin binciken\u00a0 ma&#8217;aikatu da hukumomin gwamnati na jiha da kananan hukumomi da ma ma&#8217;aikatan jihar baki daya.<\/p>\n<p>An rantsar da sabon shugaban hukumar Barista Salisu Abdu tare da sauran mambobin hukumar na dindindin da suka hada da Musa Kallamu Uba Auyo da Hassan Hashim, a zauren majalisar da ke gidan gwamnati a Dutse.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Usman Muhammad Zaria<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya kaddamar da hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa a jihar. Yayin jawabinsa a wajen bikin kaddamar da hukumar, Gwamna Umar Namadi ya jaddada mahimmancin\u00a0 hukumar wajen\u00a0 yaki da cin hanci da rashawa domin tsaftace ayyuku a jihar. Ya kuma bukaci mambobin hukumar da su [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":180,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[60,59],"class_list":["post-173","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hukumar-yaki-da-cin-hanci-da-rashawa","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/IMG-20240227-WA0014.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/173","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=173"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/173\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":177,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/173\/revisions\/177"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/180"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=173"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=173"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=173"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}