{"id":1726,"date":"2024-05-28T09:12:01","date_gmt":"2024-05-28T09:12:01","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1726"},"modified":"2024-05-28T09:12:01","modified_gmt":"2024-05-28T09:12:01","slug":"gwamnan-zamfara-ya-kaddamar-da-manyan-ayukka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnan-zamfara-ya-kaddamar-da-manyan-ayukka\/","title":{"rendered":"Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Manyan Ayukka"},"content":{"rendered":"<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-1727\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/5c401e00-6e26-4d7d-aed7-537b7caf237c-300x200.jpeg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/5c401e00-6e26-4d7d-aed7-537b7caf237c-300x200.jpeg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/5c401e00-6e26-4d7d-aed7-537b7caf237c-1024x682.jpeg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/5c401e00-6e26-4d7d-aed7-537b7caf237c-768x512.jpeg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/5c401e00-6e26-4d7d-aed7-537b7caf237c-1536x1024.jpeg 1536w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/5c401e00-6e26-4d7d-aed7-537b7caf237c-2048x1365.jpeg 2048w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>A ciki gaba da gudanar da bukukuwan cika shekara \u0257aya a karagar mulkin jihar Zamfara, ranar Litinin ne Gwamna Dauda Lawal ya \u0199addamar da wasu manyan ayyuka guda biyu a \u0198ananan Hukumomin Bakura da Maradun da ke yankin Zamfara ta Yamma.<\/p>\n<p>\u0198addamarwar na \u0257aya daga cikin manyan ayyukan da Gwamnatin Dauda Lawal ta aiwatar cikin shekara guda.<\/p>\n<p>A wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa gwamnan ya ziyarci \u0199ananan hukumomi uku: Mafara, Bakura, da Maradun.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa, a \u0199aramar hukumar Talatan Mafara, gwamna Lawal ya nuna matu\u0199ar damuwarsa kan yadda ya sami babban asibitin \u0199aramar hukumar Talata Mafara a lalace.<\/p>\n<blockquote><p>\u201cA yau, a ci gaba da \u0199addamar da wasu ayyuka da aka kammala a shekarar farko da Gwamna Lawal ya yi kan mulki, Gwamnan tare da rakiyar tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, sun \u0199addamar da sabuwar Kwalejin Noma da Fasaha da aka gyara a garin Bakura.\u201d<\/p><\/blockquote>\n<p>A jawabinsa wajen \u0199addamar da kwalejin, Gwamna Lawal ya ce; sama da shekaru ashirin da kafa Kwalejin Noma ta Bakura, tsarinta ya lalace, inda ba za a iya koyo ko koyarwa a muhallin ba.<\/p>\n<blockquote><p>\u201cA matsayinmu na gwamnatin da ta bayyana ilimi da noma a cikin manyan abubuwan da ta sa a gaba, mun ga ya dace a gyara kwalejin tare da adana mata muhimman abubuwan da za a samar da ingantaccen ilimin aikin gona.<\/p>\n<p>\u201cMun kuma \u0257aga darajar Cibiyar daga Kwalejin Noma da Kimiyyar Dabbobi zuwa Kwalejin Noma da Fasaha ta Bakura. Hikimar da ke tattare da wannan ita ce baiwa kwalejin damar gabatar da wasu fasahohi a matsayin abin da ake bu\u0199ata don sauye-sauyen \u0257aga fasahar zamani a kwalejin.<\/p>\n<p>\u201cSaboda haka, a yau mun taru a nan domin \u0199addamar da ayyukan gyare-gyaren da aka gudanar a kwalejin. Wa\u0257annan sun ha\u0257a da gyara \u0253angaren masu gudanarwa, \u0257akin gwaje-gwajen iri da sauran abubuwan da suka shafi noma, \u0257akin gwaje-gwajen \u0199wayoyin halitta, \u0257akin gwaje-gwajen abubuwan da suka shafi kimiyya, babban \u0257akin lakca da \u0257akunan kwanan \u0257alibai. Har ila yau, an gina wasu bankunan manyan ba\u0199i guda biyar tare da inganta tsarin ruwa na kwalejin.&#8221;<\/p><\/blockquote>\n<p>Yayin da yake a \u0199aramar hukumar Maradun, Gwamna Lawal ya yi dubi da yadda ake gudanar da aikin gyaran babban asibitin Maradun.<\/p>\n<p>\u201cKwangilar aikin ta ha\u0257a da gyaran \u0253angaren masu gudanarwa, \u0257akunan majiyyata maza da mata, \u0257akunan kwana na ma\u2019aikata, \u0257akin ajiyar gawa, babban \u0257akin tiyata, da ban\u0257akuna guda biyu. Sauran ayyukan sun ha\u0257a da katange asibitin, samar da isasshen ruwa na asibitin, hanyoyin tafiya da kayan aiki gaba \u0257aya.\u201d<\/p>\n<p>A \u0199aramar hukumar Talatan Mafara, gwamna Lawal ya nuna rashin gamsuwa da rashin jin da\u0257in sa a kan halin da babban asibitin Talatan Mafara yake, inda nan take ya bada umarnin gyara da inganta shi.<\/p>\n<blockquote><p>\u201cAkwai matu\u0199ar tada hankali ganin halin da babban asibitin Talatan Mafara ke ciki. Ba zan lamunci irin halin da na ga asibiti a ciki ba a lokacin bincike na. Abin da ke nuni da yadda \u2019yan siyasarmu ke karkatar da dukiyar \u0199asa, wa\u0257anda galibi suke aiwatar da al\u2019amura marasa muhimmanci.<\/p>\n<p>\u201cNa bada umarnin gyara da inganta asibitin nan take. Za mu samar da kayan aikin asibitin don samar da gyara da kuma zama babban jigo ga sauran cibiyoyin kiwon lafiya a yammacin jihar. Inganta yanayin sa zai samar da tsayayyen kiwon lafiya a yankin.<\/p><\/blockquote>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>COV\/ DUTSINMA\/Khalifa\/Wababe<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ciki gaba da gudanar da bukukuwan cika shekara \u0257aya a karagar mulkin jihar Zamfara, ranar Litinin ne Gwamna Dauda Lawal ya \u0199addamar da wasu manyan ayyuka guda biyu a \u0198ananan Hukumomin Bakura da Maradun da ke yankin Zamfara ta Yamma. \u0198addamarwar na \u0257aya daga cikin manyan ayyukan da Gwamnatin Dauda Lawal ta aiwatar cikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":1728,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[506,115],"class_list":["post-1726","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-ayukka","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/8efdf775-a996-4b10-8390-614780b2a5ae.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1726","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1726"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1726\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1729,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1726\/revisions\/1729"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1728"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1726"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1726"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1726"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}