{"id":1690,"date":"2024-05-27T19:23:25","date_gmt":"2024-05-27T19:23:25","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1690"},"modified":"2024-05-27T19:23:25","modified_gmt":"2024-05-27T19:23:25","slug":"gwamnatin-jihar-kano-za-ta-yi-gwajin-tarin-fuka-kyauta-ga-kananan-yara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jihar-kano-za-ta-yi-gwajin-tarin-fuka-kyauta-ga-kananan-yara\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Yi Gwajin Tarin Fuka Kyauta Ga Kananan Yara"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Kano za ta yi wa yara 6,000 a cibiyoyin lafiya 1,346 gwajin cutar tarin fuka kyauta.<\/p>\n<p>Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai domin tunawa da makon gwajin cutar tarin fuka na kasa na shekarar 2024.<\/p>\n<p>A cewarsa bikin ya kasance na musamman, domin an hada shi da sauran ayyukan kiwon lafiya kamar su abinci mai gina jiki,\u00a0 cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV, wayar da kan al\u2019umma, da sauransu.<\/p>\n<p>Kwamishinan ya bayyana cutar tarin fuka a matsayin cuta mai saurin yaduwa, wacce ke bin iska kuma gaba daya tana shafar huhu da ma wasu\u00a0 gabobin jiki.<\/p>\n<p>Dr. Abubakar ya yi nuni da cewa, ana iya kamuwa da ita daga mai dauke da nau\u2019in cutar zuwa wani wanda akasari ta hanyar tari, atishawa, magana ko dariya, wanda alamomin ta suka hada da tari na tsawon makonni biyu ko fiye da zazzabi mai alaka da shi ko kuma ba tare da shi ba, rage nauyi ko zufa cikin dare.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Wasu alamomin da ke da ala\u0199a a jikin yara na iya ha\u0257awa da rashun kuzari, fitar jini yayin tari, da kumburin wasu gabobi da rashin cin abinci<\/em>&#8220;. Inji shi.<\/p>\n<p>Ya ci gaba da cewa yaran da ke dauke da cutar tarin fuka ko kuma wadanda ba a kula da su ba za su iya yada ta zuwa kusan mutane 10 zuwa 15 a cikin shekara guda, inda ya bukaci iyaye da su kai \u2019ya\u2019yansu don yin gwajin cutar kyauta.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Hakkin &#8216;ya&#8217;yanmu ne a yi musu gwajin cutar tarin fuka, ya zama wajibi a matsayinmu na iyaye mu tabbatar da lafiya da walwalar &#8216;ya&#8217;yanmu kuma ya zama wajibi\u00a0 ga gwamnatin jihar Kano ta samar da ababen\u00a0 da za su dakile yaduwar cutar&#8221;.<\/em><\/p>\n<p>Dokta Abubakar ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar ma\u2019aikatar lafiya ta tarayya ta shirya shirin yaki da cutar tarin fuka da kuturta, inda aka samar da kayan aiki da magunguna da kwararrun ma\u2019aikata da sauran kayayyakin da ake bukata.<\/p>\n<p>Ciki har da injinan yin hoton jiki na X-Ray guda 20 da\u00a0 na gwajin kwayoyin cututtuka wato microscopes\u00a0 guda 250, da na&#8217;urorin gwajin cutar HIV da ta tarin fuka, da sauransu.<\/p>\n<p>Kwamishinan ya bukaci \u2018yan jarida da su kara himma wajen wayar da kan jama\u2019a game da illar cutar tarin fuka da kuma muhimmancin kai\u00a0 \u2018ya\u2019yansu domin yi musu gwaji da kuma yi musu magani.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Khadijah Aliyu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Kano za ta yi wa yara 6,000 a cibiyoyin lafiya 1,346 gwajin cutar tarin fuka kyauta. Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai domin tunawa da makon gwajin cutar tarin fuka na kasa na shekarar 2024. A cewarsa bikin ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1691,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[39,501],"class_list":["post-1690","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-kano","tag-tarin-fuka"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240527-WA0056.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1690","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1690"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1690\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1692,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1690\/revisions\/1692"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1691"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1690"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1690"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1690"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}