{"id":165,"date":"2024-02-26T12:53:50","date_gmt":"2024-02-26T12:53:50","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=165"},"modified":"2024-02-26T12:53:50","modified_gmt":"2024-02-26T12:53:50","slug":"gwamnatin-borno-ta-samar-da-gidaje-sama-da-400-ga-yan-gudun-hijira-a-dalori","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-borno-ta-samar-da-gidaje-sama-da-400-ga-yan-gudun-hijira-a-dalori\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Borno Ta Samar Da Gidaje  Sama Da 400 Ga \u2018Yan Gudun Hijira A Dalori"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Borno ta fara rabon gidaje 447 na sake tsugunar da \u2018yan gudun hijira a yankin Dalori dake karamar hukumar Konduga a jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamna Babagana Zulum wanda ya kaddamar da atisayen, ya kuma raba kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi ga iyalan da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce an zabo wadanda suka ci gajiyar tallafin ne daga sansanin &#8216;yan gudun hijira da ke Kawar Maila, inda iyalai 197 suka sami gidaje, yayin da iyalai 250 daga sansanin Dalori suka amfana.<\/p>\n<p>Ya ce an samar wa al\u2019ummar da aka sake tsugunar da su asibiti da makaranta da\u00a0 ruwan sha.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta kuma samar da kayayyakin noma da\u00a0 tallafa ga \u2018yan kasuwa domin \u2018yan gudun hijirar da suka dawo su samu saukin ababen more rayuwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Kowanne daga cikin gidajen 447, wadanda\u00a0 suka kunshi mutane kusan dubu biyu da dari biyar\u00a0 sun sami kayan abinci, da\u00a0 tabarmi, da barguna da tufafi.&#8221; In ji Gwamna Zulum.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Zulum ya kuma yi tsokaci kan shirin sake ginawa da kuma tsugunar da al\u2019ummar Dalwa da Sandiya da \u2018yan ta\u2019addan Boko Haram suka raba da muhallansu a karamar hukumar Konduga.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hakazalika, Gwamna Babagana Zulum ya kuma bayar da umarnin rufe dukkan sansanonin \u2018yan gudun hijira da ba\u00a0 hukuma\u00a0 ta kafa su ba\u00a0 a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce ba za a ci gaba da ajiye mutane a sansanoni ba, yana mai jaddada cewa za a rufe dukkan sansanoni da ke Maiduguri kafin ranar 29 ga Mayun 2024.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Muna so a sami kamulallun\u00a0 mutane\u00a0 a cikin al&#8217;ummoma daban-daban domin bayar da gudummawar ci gaban jihar, don haka za mu mayar da su gidajensu domin su ci gaba da gudanar da al&#8217;amuran su na yau da kullun&#8221;. Inji\u00a0 shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan ya bayyana cewa an rufe dukkanin sansanonin \u2018yan gudun hijira da gwamnati ta kafa a birnin Maiduguri da kewaye tun shekarar da ta gabata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daga Dauda Iliya<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Borno ta fara rabon gidaje 447 na sake tsugunar da \u2018yan gudun hijira a yankin Dalori dake karamar hukumar Konduga a jihar. &nbsp; Gwamna Babagana Zulum wanda ya kaddamar da atisayen, ya kuma raba kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi ga iyalan da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu. &nbsp; Ya ce [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":166,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[55,54,53],"class_list":["post-165","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-yan-gudun-hijira","tag-an-samar-da-gidaje-447","tag-borno"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/02\/IMG-20240226-WA0001.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/165","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=165"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/165\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":167,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/165\/revisions\/167"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/166"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=165"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=165"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=165"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}