{"id":1632,"date":"2024-05-26T11:39:55","date_gmt":"2024-05-26T11:39:55","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1632"},"modified":"2024-05-27T07:32:22","modified_gmt":"2024-05-27T07:32:22","slug":"ilimi-tsanin-kaiwa-ne-ga-nasara-gwamana-dauda-lawal","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ilimi-tsanin-kaiwa-ne-ga-nasara-gwamana-dauda-lawal\/","title":{"rendered":"Ilimi Tsanin Kaiwa Ne Ga Nasara &#8211; Gwamana Dauda Lawal"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana ilimi a matsayin wani tsani, matakala ta kaiwa ga samun duk wani abin nema a duniyar nan.<\/p>\n<p>Gwamnan ya halarci taron yaye \u0257alibai karo na uku da na hu\u0257u na Jami&#8217;ar tarayya, wanda ya gudana a filin taro na Jami&#8217;ar da ke Gusau a jiya Asabar.<\/p>\n<p>Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Gusau cewa, Gwamna Lawal ya shelanta bayar da gurbin karatu ga duk wanda ya zo na \u0257aya a Jami&#8217;ar.<\/p>\n<p>Cikin jawabin sa a wurin taron, Gwamnan ya yaba wa shugabannin Jami&#8217;ar game da yadda suka iya ririta \u0257an abin da suke da shi, duk da \u0257imbin \u0199alubalen da suke fuskanta.<\/p>\n<p>Ya ce, &#8220;Ina matu\u0199ar farin cikin kasancewa da ku yau a wannan bikin yaye \u0257alibai karo na uku da na hu\u0257u a wannan jajirtacciyar Jami&#8217;a, Jami&#8217;ar gwamnatin tarayya ta Gusau. Ina taya jami&#8217;ar nan murnar samun wannan nasara, duk kuwa da matsalolin da suke fuskanta tun lokacin da aka kafa ta. Ina kuma yaba wa iyaye da \u0257alibai bisa sadaukarwar da suka nuna har zuwa wannan matsayi.<\/p>\n<p>Muna sa ran samun makoma mai kyau kuma mai albarka duk da tarin \u0199alubalen da muke fuskanta a matsayinmu na jiha kuma al&#8217;umma. Muna yin addu&#8217;a kuma muna aiki ba dare ba rana don samar da makoma mai kyau. Duk wa\u0257annan matsaloli za su wuce da izinin Allah Ma\u0257aukakin Sarki.\u201d<\/p>\n<p>Gwamnan ya yi \u0199arin haske kan \u0199o\u0199arin gwamnatinsa na gyara harkar ilimi a Jihar Zamfara bayan kafa dokar ta-\u0253aci a bara.<\/p>\n<p>\u201cA matsayinmu na gwamnati, mun \u0199uduri aniyar ilimantar da duk \u2019ya\u2019yan Zamfara. Ilimi shi ne ginshi\u0199in da ke haskaka ruyuwar \u0257an adam.<\/p>\n<p>\u201cMun ware ma\u0199udan ku\u0257a\u0257e ga \u0253angaren ilimi a cikin kasafin ku\u0257inmu na 2024 kuma muna fatan za mu kai ga babban matsayi a 2025, 2026, da 2027. Muna fatan cimma kashi 25 zuwa 30 na ha\u0253aka tsarin ilimi. Tare da samar da ingantaccen tsari a fannin da sarrafa albarkatun da ya \u0199unsa, muna da \u0199warin gwiwar cewa za mu farfa\u0257o da ababen more rayuwa, \u0257aukar \u0199wararrun malamai, horarwa da sake horar da wa\u0257anda ake da su.<\/p>\n<p>\u201cZa kuma mu \u0199ara yawan masu karatu a makarantun firamare da na gaba da firamare ta hanyar wayar da kan jama\u2019a da samar da ingantattun wuraren koyo da koyarwa. Ilimi kyauta ne, kuma muna fatan ya zama wajibi ga kowa.<\/p>\n<p>\u201cMun kuma yi wa manyan makarantunmu da ke jihar kason ku\u0257i mai yawa don fara aikin gyara su zuwa matakai masu inganci. A karon farko Jami\u2019ar Jihar Zamfara na shirye-shiryen amincewa da shirin Hukumar Kula da Jami\u2019o\u2019i ta \u0198asa. Mun umurci \u2019yan kwangilar da gwamnatin da ta shu\u0257e ta tilastawa barin wuraren aiki da su koma bakin aiki, kuma muna fatan nan da watanni masu zuwa, rukunin dindindin na jami\u2019ar zai fara aiki. A lokaci guda, NUC za ta amince ga duk kwasa-kwasai.<\/p>\n<p>\u201cMun kar\u0253i mulki a jihar da gwamnati ta \u0199i biyan ku\u0257a\u0257en jarrabawar WEAC da NECO har na biliyoyin Naira fiye da shekaru uku. Dole muka yi shiri na musamman da hukumomin, kuma tun daga lokacin an fara biyan ku\u0257i a kan kari kuma za a kammala su a kan lokaci.<\/p>\n<p>\u201cA cikin \u0199arancin albarkatunmu, za mu ci gaba da bayar da taimako ga jami\u2019a. Burinmu shi ne mu \u0199ara ha\u0253aka ilimi a jiharmu ta yadda za a samu damarmaki ga \u0257aukacin matasanmu da za a horar da su don kai ga \u0199ololuwar da ilimi ke samarwa.\u201d<\/p>\n<p>Dutsinma\/Wababe<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana ilimi a matsayin wani tsani, matakala ta kaiwa ga samun duk wani abin nema a duniyar nan. Gwamnan ya halarci taron yaye \u0257alibai karo na uku da na hu\u0257u na Jami&#8217;ar tarayya, wanda ya gudana a filin taro na Jami&#8217;ar da ke Gusau a jiya Asabar. Mai magana [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":1633,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1],"tags":[115],"class_list":["post-1632","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240526-WA0018.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1632","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1632"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1632\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1650,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1632\/revisions\/1650"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1633"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1632"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1632"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1632"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}