{"id":1490,"date":"2024-05-20T14:15:38","date_gmt":"2024-05-20T14:15:38","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1490"},"modified":"2024-05-20T14:15:38","modified_gmt":"2024-05-20T14:15:38","slug":"majalisar-dokokin-kano-ta-bukaci-gwamnati-ta-tallafawa-wadanda-harin-masallaci-ya-shafa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/majalisar-dokokin-kano-ta-bukaci-gwamnati-ta-tallafawa-wadanda-harin-masallaci-ya-shafa\/","title":{"rendered":"Majalisar Dokokin Kano Ta Bukaci Gwamnati Ta Tallafawa Wadanda Harin Masallaci Ya Shafa"},"content":{"rendered":"<p>Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar\u00a0 da ta taimaka wa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a harin masallaci da ya faru\u00a0 a karamar hukumar Gada Gezawa.<\/p>\n<p>Wannan dai ya biyo bayan zaman tattaunawa ne da aka yi a zauren majalisar wanda shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma&#8217;il Falgore ya jagoranta.<\/p>\n<p>A wani kudiri na gaggawa wanda dan majalisa mai wakiltar mazabar Gezawa Alhaji Abdullahi Yahaya ya gabatar ga\u00a0 majalisar, ya bayyana cewa mutane 17 ne suka rasu,\u00a0 yayin da wadanda ke raye ke cikin mawuyacin hali, wanda\u00a0 a halin yanzu suke samun kulawa a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.<\/p>\n<p>Dan majalisar ya bayyana cewa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata na bukatar tallafi daga gwamnatin tarayya da na jihohi.<\/p>\n<p>Abdullahi ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya bukaci hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gurfanar da wanda ya aikata laifin.<\/p>\n<p>Sauran wadanda suka goyi bayan kudirin sun hada da wakilan Kiru da Madobi Usman da Sulaiman Mukhtar.<\/p>\n<p>Tun da farko kakakin majalisar Alhaji Jibril Isma\u2019il Falgore ya jajantawa gwamnati da iyalai da daukacin al\u2019ummar jihar bisa wannan mummunan lamari da ya faru,\u00a0 inda ya yi addu\u2019ar Allah ya ji kan wadanda suka rasu ya kuma ba sauran lafiya.<\/p>\n<p>A wani labarin kuma, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi gyaran fuska ga kudirin gudanar da kasafin kudi a karatu na biyu.<\/p>\n<p>Shugaban masu rinjaye wanda dan kuma shi ne dan\u00a0 majalisa mai wakiltar, Dala Alhaji Lawan Hussaini Dala ya yi nuni da cewa dokar tana neman tabbatar da \u2018yancin cin gashin kai ga majalisar dokokin Kano kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus-alawus, daukar ma\u2019aikata, karin girma da sauransu.<\/p>\n<p>Da yake goyan bayan kudurin, mataimakin shugaban majalisar Alhaji Muhammad Bello Butu Butu ya jaddada cewa, bayan an yi nazari an lura akwai banbance-banbance tsakanin kudurin kula da kudade na majalisar dokokin Kano\u00a0 da na majalisar\u00a0 kasar, don haka akwai bukatar gyara.<\/p>\n<p>Majalisar ta dage zamanta zuwa washegari a wani kudiri da shugaban masu rinjaye Lawan Hussaini Dala ya gabatar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>Khadija Aliyu<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar\u00a0 da ta taimaka wa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a harin masallaci da ya faru\u00a0 a karamar hukumar Gada Gezawa. Wannan dai ya biyo bayan zaman tattaunawa ne da aka yi a zauren majalisar wanda shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma&#8217;il Falgore ya jagoranta. A [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1491,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1],"tags":[459],"class_list":["post-1490","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","tag-harin-masallacin-kano"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Kano-Assembly.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1490","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1490"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1490\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1492,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1490\/revisions\/1492"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1491"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1490"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1490"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1490"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}