{"id":1415,"date":"2024-05-15T15:07:35","date_gmt":"2024-05-15T15:07:35","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1415"},"modified":"2024-05-15T16:09:22","modified_gmt":"2024-05-15T16:09:22","slug":"jirgin-farko-na-alhazan-najeriya-ya-tashi-zuwa-kasa-mai-tsarki","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jirgin-farko-na-alhazan-najeriya-ya-tashi-zuwa-kasa-mai-tsarki\/","title":{"rendered":"Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki"},"content":{"rendered":"<p>A yau Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne jirgin Najeriya na farko ya tashi da Alhazan Jihar Kebbi 423 daga filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi zuwa kasar Saudiyya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake kaddamar da jigilar Alhazan na farko, mataimakin shugaban kasa Kashim Shetima, ya ce duk da tabarbarewar tattalin arzikin da kasar nan ta shiga saboda faduwar darajar Naira, shugaba Tinubu ya bayar da Naira biliyan 90 domin tallafa wa aikin hajjin bana.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mataimakin shugaban kasar, ya bukaci maniyyatan da su dage da yi wa\u00a0 shugabanninsu da malaman\u00a0 addini da ma al\u2019umma baki daya addu\u2019a domin kawo karshen matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.<\/p>\n\n\t\t<style>\n\t\t\t#gallery-1 {\n\t\t\t\tmargin: auto;\n\t\t\t}\n\t\t\t#gallery-1 .gallery-item {\n\t\t\t\tfloat: left;\n\t\t\t\tmargin-top: 10px;\n\t\t\t\ttext-align: center;\n\t\t\t\twidth: 33%;\n\t\t\t}\n\t\t\t#gallery-1 img {\n\t\t\t\tborder: 2px solid #cfcfcf;\n\t\t\t}\n\t\t\t#gallery-1 .gallery-caption {\n\t\t\t\tmargin-left: 0;\n\t\t\t}\n\t\t\t\/* see gallery_shortcode() in wp-includes\/media.php *\/\n\t\t<\/style>\n\t\t<div id='gallery-1' class='gallery galleryid-1415 gallery-columns-3 gallery-size-thumbnail'><dl class='gallery-item'>\n\t\t\t<dt class='gallery-icon landscape'>\n\t\t\t\t<a href='https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jirgin-farko-na-alhazan-najeriya-ya-tashi-zuwa-kasa-mai-tsarki\/img-20240515-wa0059\/'><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"150\" height=\"150\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240515-WA0059-150x150.jpg\" class=\"attachment-thumbnail size-thumbnail\" alt=\"\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240515-WA0059-150x150.jpg 150w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240515-WA0059-80x80.jpg 80w\" sizes=\"auto, (max-width: 150px) 100vw, 150px\" \/><\/a>\n\t\t\t<\/dt><\/dl>\n\t\t\t<br style='clear: both' \/>\n\t\t<\/div>\n\n<p>Yayin da yake shawartar mahajjatan da su gudanar da ayyukansu kamar yadda dokokin hukumomin Saudiyya suka tanadar, mataimakin shugaban kasar ya yabawa Gwamna Nasir Idris bisa yadda ya bayar da dukkanin goyon bayan da ya dace wajen tabbatar da nasarar\u00a0 tashin jirgin farko daga jiharsa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Gwamna Nasir Idris na jihar ta Kebbi ya ce, a shekarar da ta gabata an yi jigilar Alhazan jihar zuwa kasa mai tsarki ne daga Sakkwato, sakamakon wasu matsaloli da aka samu a filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbin, inda ya bayyana cewa a halin yanzu an shawo kan matsalar, za kuma a ci gaba da\u00a0 jigilar Alhazan jihar.<\/p>\n<p>Daga nan sai ya umurci masu rike da mukaman siyasa da shugabannin kananan hukumomi da su bayar da tallafin kudi ga maniyyatan mazabarsu a lokacin da suke kasa mai tsarki domin su samu damar gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali.<\/p>\n<p>Shi ma da yake jawabi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa\u2019ad Abubakar III, ya bayyana aikin Hajji a matsayin ibada da mutum zai tsarkake zuciyarsa, don haka ya bukaci Alhazan da kada su dauki haramtattun kayayyaki da kayan da za su hana su cimma manufar. aikin hajji.<\/p>\n<p>Tun da farko a jawabinsa shugaban Hukumar Alhazai ta kasa Jalal Ahmad Arabi, ya ce hukumar ta samar da mafi kyawun masauki a Madina domin jin dadin Alhazai baya ga yin tsare-tsare masu muhimmanci tsakanin hukumomin Saudiyya da hukumar domin jin dadinsu.<\/p>\n<p><strong><em>Abdullahi Tukur<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A yau Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne jirgin Najeriya na farko ya tashi da Alhazan Jihar Kebbi 423 daga filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi zuwa kasar Saudiyya. &nbsp; Da yake kaddamar da jigilar Alhazan na farko, mataimakin shugaban kasa Kashim Shetima, ya ce duk da tabarbarewar tattalin arzikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1423,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[433,382,159,432],"class_list":["post-1415","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-2024-hajj","tag-hajji","tag-jihar-kebbi","tag-jirgin-farko"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240515-WA0058.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1415","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1415"}],"version-history":[{"count":4,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1415\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1428,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1415\/revisions\/1428"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1423"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1415"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1415"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1415"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}