{"id":1396,"date":"2024-05-14T13:39:34","date_gmt":"2024-05-14T13:39:34","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1396"},"modified":"2024-05-14T13:39:34","modified_gmt":"2024-05-14T13:39:34","slug":"gwamnatin-kano-ta-nada-ibrahim-garba-shugaban-tawagar-yan-jarida-a-hajjin-bana","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-kano-ta-nada-ibrahim-garba-shugaban-tawagar-yan-jarida-a-hajjin-bana\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Kano Ta Nada Ibrahim Garba Shugaban Tawagar &#8216;Yan Jarida A Hajjin  Bana"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin shugaban tawagar &#8216;yan jaridu a aikin Hajjin 2024.<\/p>\n<p>An bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na kaddamar da kwamitin gudanar da aikin Hajji na shekarar 1445AH\/2024 a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano da ke kwaryar birnin jihar.<\/p>\n<p>Taron ya samu halartar ma\u2019aikatan kafafen yada labarai da za su rika ba da rahoton abubuwan da ke gudana yayin\u00a0 aikin Hajji\u00a0 wanda\u00a0 \u00a0dubban maniyyata daga Najeriya da ma sauran sassan duniya baki daya ke halarta.<\/p>\n<p>Shuaibu, wanda a halin yanzu shi ne sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kware a harkar yada labarai da sadarwa.<\/p>\n<p>Ya kuma taba zama tsohon shugaban kungiyar \u2018yan jarida ta kasa (NUJ) Correspondents Chapel reshen jihar Kano, da kuma wakilin jaridar This Day.<\/p>\n<p>Nadin da aka yi masa a matsayin shugaban tawagar kafafen yada labarai wani gagarumin ci gaba ne, wanda ake sa ran zai yi amfani da\u00a0 kwarewarsa wajen tafiyar da harkokin yada labarai na aikin hajji.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sama da maniyyata 3,000 ne daga jihar Kano ake sa ran za su halarci aikin Hajjin 2024.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A ranar 15 ga watan Mayu ne daidake sa ran\u00a0 fara jigilar maniyyata daga kasar nan zuwa kasa mai tsarki.<\/p>\n<p>Gwamnatin jihar Kano ta shirya tsaf domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin kwanciyar hankali da nasara ga dukkan maniyyata, kuma nadin Shuaibu na daya daga cikin muhimman ayyukan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Khadija Aliyu<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Kano ta amince da nadin Ibrahim Garba Shuaibu a matsayin shugaban tawagar &#8216;yan jaridu a aikin Hajjin 2024. An bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na kaddamar da kwamitin gudanar da aikin Hajji na shekarar 1445AH\/2024 a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano da ke kwaryar birnin jihar. [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1397,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[294,39,423],"class_list":["post-1396","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hajj","tag-kano","tag-shugaban-tawagar-yan-jaridu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/FB_IMG_1686942236220-1-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1396","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1396"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1396\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1398,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1396\/revisions\/1398"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1397"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1396"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1396"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1396"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}