{"id":1229,"date":"2024-05-02T11:50:33","date_gmt":"2024-05-02T11:50:33","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1229"},"modified":"2024-05-02T11:50:33","modified_gmt":"2024-05-02T11:50:33","slug":"gwamnatin-jigawa-za-ta-samar-da-tarakta-300-ga-manoma-daga-amurka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jigawa-za-ta-samar-da-tarakta-300-ga-manoma-daga-amurka\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka"},"content":{"rendered":"<p>A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta \u0199ulla wata yarjejeniyar ha\u0257in gwiwa da wasu manyan kamfanoni da suka yi fice a fannin dabarun bincike da samar da kayan aikin gona na zamani domin bun\u0199asa harkar noma a jihar.<\/p>\n<p>Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Jigawa, Hamisu Mohammed Gumel ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.<\/p>\n<p>Ya yi bayanin cewar, an \u0199ulla wannan yarjejeniyar ha\u0257in gwiwa ne a wani zaman tattaunawa da aka yi a birnin Washington DC na Kasar Amurka tsakanin tawagar \u0199wararru daga Jihar Jigawa \u0199ar\u0199ashin jagorancin Gwamna Umar Namadi da kuma wakilan shugabannin kamfanonin da abin ya shafa.<\/p>\n<p>A cewar sa, tattaunawar da ta gudana tsakanin \u0253angarorin biyu ta ta\u2019alla\u0199a ne kan yadda za a samar da kuma bun\u0199asa dabarun noma tare da shigar da matasa cikin harkar noma domin ganin an \u0257aga matsayi da inganta rayuwar al\u2019ummar jihar Jigawa ta hanyar noma.<\/p>\n<p>Hamisu Mohammed Gumel ya yi nuni da cewar, daga cikin kyawawan sakamakon da wannan tattaunawar ta haifar shine \u0199uduri na ha\u0257in gwiwa da aka zartas na samar da wani shiri da a cikinsa za a siyo tarakta guda 300.<\/p>\n<p>Yana Mai cewar nan bada jimawa ba za&#8217;a kawo su don ci gaba da inganta harkar noma a jihar ta Jigawa.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-1231\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240502-WA0006-300x168.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"168\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240502-WA0006-300x168.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240502-WA0006-1024x575.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240502-WA0006-768x431.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240502-WA0006.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ya ce wannan zai taimaka matu\u0199a wajen bun\u0199asar samun amfanin gona mai kyau da inganci a tsakanin \u0199ananan manoman jihar.<\/p>\n<p>Hamisu Mohammed ya ce a \u0199ar\u0199ashin wannan shiri ana sa ran za a horas da matasa sama da dubu daya da dari biyu kan harkar kasuwancin sayarwa da ba da hayar kayan aikin gona da kuma sarrafawa tare da gyaran taraktoci da sauran na\u2019urorin aikin da za a samar.<\/p>\n<p>Babbar manufar wannan shiri ita ce jawo matasa su shiga cikin harkar noma, wanda a yau ita ce hanyar samar da isasshen abinci da bun\u0199asar tattalin arziki a jiha da kuma \u0199asa baki \u0257aya.<\/p>\n<p>Kazalika, yace hakan wani \u0253angare na manufofin da Gwamna Umar Namadi ya \u0199uduri aiwatarwa don inganta fannin noma da sauran fannonin rayuwa a Jigawa da ya zayyana a cikin \u0199udurori 12 na gwamnatinsa.<\/p>\n<p>Da yake magana kan \u0199ulla wannan ha\u0257in gwiwa, Gwamna Umar Namadi ya \u0199ara jaddada muhimmancin yin amfani da dabaru da kayan aikin gona na zamani tare da jawo matasa cikin harkar, domin ta hakan ne za a tabbatar an inganta wannan fannin na noma a nan gaba.<\/p>\n<p>Namadi, ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafawa manoma, musamman matasa da a yanzu suka fara ganin muhimmancin wannan fanni, ta hanyar samar da kayan aiki da dabarun noma na zamani don ci gaban al\u2019umma.<\/p>\n<p><strong><em>Usman Mohammed Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta \u0199ulla wata yarjejeniyar ha\u0257in gwiwa da wasu manyan kamfanoni da suka yi fice a fannin dabarun bincike da samar da kayan aikin gona na zamani domin bun\u0199asa harkar noma a jihar. Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Jigawa, Hamisu Mohammed Gumel ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1232,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,10],"tags":[59,41,389,388],"class_list":["post-1229","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma","tag-jigawa","tag-noma","tag-tarakta","tag-yarjejeniya"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240502-WA0007.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1229","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1229"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1229\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1233,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1229\/revisions\/1233"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1232"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1229"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1229"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1229"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}