{"id":1222,"date":"2024-05-01T22:24:19","date_gmt":"2024-05-01T22:24:19","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1222"},"modified":"2024-05-01T22:24:19","modified_gmt":"2024-05-01T22:24:19","slug":"an-samar-da-masauki-kusa-da-harami-ga-alhazan-jihar-jigawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-samar-da-masauki-kusa-da-harami-ga-alhazan-jihar-jigawa\/","title":{"rendered":"An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa"},"content":{"rendered":"<p>Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa\u00a0 ta samar da katafaren masauki\u00a0 kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah na kasar Saudiyya ga Alhazan jihar da za su sauke farali a bana.<\/p>\n<p>Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga wakilin gidan rediyon Najeriya a Dutse babban birnin jihar.<\/p>\n<p>Ya ce hukumar ta samar da masauki mai daraja da zai yi gogayya da na sauran kasashen duniya kusa da masallacin Harami, domin baiwa Alhazan jihar damar zuwa masallacin ba tare da wata wahala ba.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa, Gwamna Umar Namadi\u00a0 ya kudiri aniyar bai wa\u00a0 hukumar duk wani tallafin da ya dace domin\u00a0 samun damar kulawa da Alhazan jihar yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Dangane da ciyarwa yayi aikin Hajji kuwa, Ahmed Labbo ya bayyana cewa, hukumar ta kulla yarjejeniya da wani kamfani don samar da ingantaccen abinci ga\u00a0 Alhazan jihar\u00a0 yayin gudanar da aikin Hajjin.<\/p>\n<p>Ya ce, hukumar na da kwarin gwiwar cewa kamfanin zai cimma yarjejeniyar da suka kulla.<\/p>\n<p>Shugaban ya yi nuni da cewa, za su rika bada kulawa ta musamman ga mahajjatan da ke fama da lalurar rashin lafiya don ganin su ma an samar musu abincin da ya dace da su.<\/p>\n<p>Yayin da ya yaba wa ma\u2019aikatan hukumar kan kwazon su, ya kuma\u00a0 umarce su da su sake sadaukar da kansu don ganin an samu nasarar aikin Hajjin bana.<\/p>\n<p>Labbo ya bayyana godiya ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Umar Namadi da kuma hukumar Alhazai ta kasa NAHCON bisa goyon bayan\u00a0 da suke\u00a0 bai wa hukumar jin dadin alhazai ta jihar jigawa.<\/p>\n<p><strong><em>Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa\u00a0 ta samar da katafaren masauki\u00a0 kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah na kasar Saudiyya ga Alhazan jihar da za su sauke farali a bana. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga wakilin gidan rediyon Najeriya a Dutse babban birnin jihar. Ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1223,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[382,283,383],"class_list":["post-1222","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hajji","tag-jihar-jigawa","tag-masauki"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/IMG-20240501-WA0013.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1222","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1222"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1222\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1224,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1222\/revisions\/1224"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1223"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1222"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1222"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1222"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}