{"id":1060,"date":"2024-04-18T12:15:53","date_gmt":"2024-04-18T12:15:53","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=1060"},"modified":"2024-04-18T12:15:53","modified_gmt":"2024-04-18T12:15:53","slug":"ambaliyar-ruwa-ta-shafe-manyan-titunan-birnin-dubai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ambaliyar-ruwa-ta-shafe-manyan-titunan-birnin-dubai\/","title":{"rendered":"Ambaliyar Ruwa ta Shafe Manyan Titunan Birnin Dubai"},"content":{"rendered":"<div class=\"intro intro--bold\">\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ambaliyar ruwa ta rufe manyan titunan birnin Dubai kuma babban filin jirgin samansa ya kasance cikin rudu yayin da cibiyar hada-hadar kudi ta Gabas ta Tsakiya din ta kasance a kulle a ranar Laraba, kwana guda bayan da aka yi ruwan sama mai tsananin gaske da ba a taba irinsa ba.<\/p>\n<\/div>\n<div id=\"article-content\" class=\"content-floated-wrap fb-quotable\">\n<div class=\"wsw\">\n<p>A kalla mutum daya ya mutu, wani dattijo mai shekaru 70 da haifuwa, a cikin motarsa a Ras Al-Khaimah, daya daga cikin masarautun kasar bakwai masu arzikin man fetur, in ji \u2018yan sanda.<\/p>\n<p class=\"elementtoproof\">An samu katsewar wutar lantarki a kusa da birnin Dubai, wanda ke cike da ambaliyar ruwa da ya nitsar da motocin da aka bari.<\/p>\n<p class=\"elementtoproof\">An ga irin wannan al&#8217;amuran a kusa da yankunan da suka hada da Sharjah, makwabciyar Dubai, inda mazauna yankin suka yi ta ratsa manyan tituna tare da kai komo a cikin kwale-kwale na wucin gadi.<\/p>\n<p class=\"elementtoproof\"><em>&#8220;Wannan shi ne lamari mafi muni da na taba fuskanta,&#8221; in ji wani dan kasar Dubai mai shekaru 30, wanda ya so a sakaya sunansa, bayan wata tafiyar tsawon mintuna 15, ya koma sa&#8217;o&#8217;i 12 a kan tituna da ambaliyar ruwa ta mamaye.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>&#8220;Na san cewa idan motata ta lalace zata nutse ni ma kuma zan nutse da ita.&#8221;<\/p>\n<p>Makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe a Dubai har zuwa mako mai zuwa, in ji hukumomi, wanda ke nuna irin wahalar tsaftace muhallin.<\/p>\n<p>A halin da ake ciki, ayyuka suna yi tafiyar hawainiya a filin jirgin sama na Dubai, mai tasha mafi yawan zirga-zirgar jiragen sama a duniya, yayin da ma&#8217;aikatan suka kasa isowa aiki sakamakon ambaliyar ruwa, sannan kuma aka dakatar da akasarin motocin zirga-zirgar jama&#8217;a.<\/p>\n<p class=\"elementtoproof\">Yayin da aka jinkirta kusan kowane jirgi akai-akai, an gaya wa fasinjoji su nisanci filin &#8220;sai dai idan ya zama dole,&#8221; in ji ma\u2019aikatan Filin jirgin saman Dubai.<\/p>\n<p class=\"elementtoproof\">An kuma jinkirta tashin jirage da dama, an soke da kuma karkatar da su a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Talata, lokacin da jiragen suka ce su na yunkurin tashi cikin ruwa mai zurfi.<\/p>\n<p class=\"elementtoproof\">Guguwar ta afka wa kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain ne da daren jiya litinin da kuma ranar Talata bayan da a baya suka afka wa kasar Oman, inda mutane 19 suka mutu ciki har da kananan yara.<\/p>\n<p class=\"elementtoproof\">Maryam Al Shehhi, babbar jami\u2019ar hasashen yanayi a cibiyar nazarin yanayi ta UAE, ta musanta rahoton da ke cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi shukar gajimare inda ta fesa sinadarai don kara yawan ruwan sama.<\/p>\n<p><em><strong>VOA<\/strong><\/em><\/p>\n<\/div>\n<\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Ambaliyar ruwa ta rufe manyan titunan birnin Dubai kuma babban filin jirgin samansa ya kasance cikin rudu yayin da cibiyar hada-hadar kudi ta Gabas ta Tsakiya din ta kasance a kulle a ranar Laraba, kwana guda bayan da aka yi ruwan sama mai tsananin gaske da ba a taba irinsa ba. A kalla mutum [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":1061,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,12],"tags":[320,319,323,321,322],"class_list":["post-1060","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-ketare","tag-ambaliya","tag-dubai","tag-filin-jirgi","tag-ruwa","tag-tituna"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/01000000-0aff-0242-dd67-08dc5ee6ee04_cx3_cy0_cw93_w1080_h608_s.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1060","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1060"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1060\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1062,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1060\/revisions\/1062"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1061"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1060"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1060"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1060"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}