{"id":10391,"date":"2026-11-24T21:09:13","date_gmt":"2026-11-24T21:09:13","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10391"},"modified":"2026-11-24T21:09:13","modified_gmt":"2026-11-24T21:09:13","slug":"gwamna-namadi-ya-bukaci-alummar-jihar-jigawa-su-cigaba-da-mara-masa-baya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-namadi-ya-bukaci-alummar-jihar-jigawa-su-cigaba-da-mara-masa-baya\/","title":{"rendered":"Gwamna Namadi Ya Bukaci Al\u2019ummar Jihar Jigawa Su Cigaba Da Mara Masa Baya"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman MZ\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci al\u2019ummar jihar da su ci gaba da amincewa da gwamnatinsa gabanin babban zaben shekarar 2027, yana mai tabbatar musu cewa za a saka musu da kyakkyawan shugabanci bisa goyon bayan da suke bayarwa.<\/p>\n<p>Gwamnan ya yi wannan kiran ne a yayin wani gangamin yakin neman zaben jam\u2019iyyar APC a karamar hukumar Gwiwa, inda ya nuna godiyarsa bisa dimbin jama\u2019ar da suka halarta.<\/p>\n<p>Ya ce karuwar goyon bayan da jam\u2019iyyar ke samu a yayin gangamin da take gudanarwa a matakin kasa ya nuna irin amincewar da al\u2019umma suke da ita ga APC, yana mai alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin tabbatar da wannan amana.<\/p>\n<p>Da yake kwatanta tarbar da aka yi masa a Gwiwa da wadda aka yi masa a karamar hukumar Roni a ranar Lahadi, Gwamna Namadi ya ce yawan jama\u2019ar da suka halarta ya ba shi mamaki matuka.<\/p>\n<p>Ya tabbatar wa al\u2019ummar cewa gwamnatinsa ba za ta ba su kunya ba, yana mai kira gare su da su ci gaba da kasancewa tare da jam\u2019iyyar.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-10393\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261124-WA0003-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261124-WA0003-300x200.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261124-WA0003-1024x682.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261124-WA0003-768x511.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261124-WA0003.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/>Gwamnan ya kuma karbi sama da mambobi 850 daga jam\u2019iyyun ADC da PDP, wadanda suka sauya sheka zuwa APC daga dukkanin mazabu 11 na karamar hukumar Gwiwa.<\/p>\n<p>Da yake tarbar wadanda suka sauya shekar, Namadi ya tabbatar musu da cewa za a ba su dama da kulawa yadda yakamata, ba tare da la\u2019akari da lokacin da suka shiga ba.<\/p>\n<p>Ya kuma bukace su da su yi amfani da kwarewarsu ta siyasa da alakar da suke da ita da al\u2019umma wajen jawo karin mambobin jam\u2019iyyun adawa zuwa APC.<\/p>\n<p>Da yake magana a madadin wadanda suka sauya shekar, Malam Tijjani, tsohon mamban PDP, ya ce sun yanke shawarar shiga APC ne sakamakon kyakkyawan shugabancin da suka ce Gwamna Namadi yake yi.<\/p>\n<p>Ya kuma tabbatar wa gwamnan da shugabannin APC cewa za su himmatu wajen wayar da kan jama\u2019a da neman goyon baya ga jam\u2019iyyar domin samun nasara a babban zaben 2027.<\/p>\n<p>Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa gwamnan ya kuma kaddamar da fara aikin gina wata hanya da karamar hukumar Gwiwa ta bayar da kwangilarta.<\/p>\n<p>Fassara: Safiyah Abdulkadir<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman MZ\u00a0 Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci al\u2019ummar jihar da su ci gaba da amincewa da gwamnatinsa gabanin babban zaben shekarar 2027, yana mai tabbatar musu cewa za a saka musu da kyakkyawan shugabanci bisa goyon bayan da suke bayarwa. Gwamnan ya yi wannan kiran ne a yayin wani gangamin yakin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":10392,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_hide_featured_image":false,"_jetpack_featured_image_duplicate_dismissed":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[59,2183,411],"class_list":["post-10391","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-jigawa","tag-mamadi","tag-zabe"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261124-WA0002.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10391","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10391"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10391\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10394,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10391\/revisions\/10394"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10392"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10391"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10391"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10391"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}