{"id":10318,"date":"2026-11-11T13:07:59","date_gmt":"2026-11-11T13:07:59","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10318"},"modified":"2026-11-11T13:07:59","modified_gmt":"2026-11-11T13:07:59","slug":"kano-kotu-ta-umarci-a-lalata-buhunan-fulawa-sama-da-400","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kano-kotu-ta-umarci-a-lalata-buhunan-fulawa-sama-da-400\/","title":{"rendered":"Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Khadijah Aliyu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka lalace, wa\u0257anda Hukumar Kare Ha\u0199\u0199in Masu Sayen Kaya ta Jihar Kano (KCPC) ta \u0199wace saboda barazanar da suke yi ga lafiyar jama&#8217;a.<\/p>\n<p>Umarnin kotun ya biyo bayan shigar da \u0199ara da hukumar ta yi, bayan gano garin alkamar da ya lalace, wanda ake zargin an tanade shi ne domin sayar wa jama&#8217;a.<\/p>\n<p>Hukumar ta ce ta \u0199wace buhunan\u00a0 ne bayan samun bayanan sirri kan adana wasu buhuna masu yawa na fulawa da suka lalace, wa\u0257anda aka shirya rabawa da sayarwa ga masu saye.<\/p>\n<p>Da yake magana kan lamarin, Shugaban hukumar, Dakta Ibrahim Garba Muhammad, ya jaddada aniyar hukumar na tabbatar da bin dokokin kare ha\u0199\u0199in masu sayen kaya da kuma tilasta wa &#8216;yan kasuwa bin \u0199a&#8217;idojin kasuwanci.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa gurfanar da &#8216;yan kasuwar da suka karya dokokin kare masu saye yana da muhimmanci wajen kare al&#8217;ummar jihar daga amfani da kayayyakin da ba su da aminci ga lafiya da sauran harkokin kasuwanci marasa adalci.<\/p>\n<p>Dakta Garba ya bu\u0199aci &#8216;yan kasuwa da su ba hukumar ha\u0257in kai, yana mai cewa babban aikin hukumar shi ne tabbatar da bin doka da kare masu saye daga cutarwa.<\/p>\n<p>Ya kuma yaba wa al&#8217;umma bisa \u0199ara wayewa kan ayyukan hukumar, tare da \u0199arfafa musu gwiwar duba ingancin kaya, ranar \u0199arewar amfaninsu da bayanan da ke jikin marufinsu kafin saye.<\/p>\n<p>Shugaban Hukumar ya kuma gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ci gaba da tallafa wa hukumar, yana mai bayyana cewa ha\u0257in kan gwamnatin jihar na taimakawa wajen gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Ana sa ran umarnin kotun zai hana sake shigar da fulawar cikin kasuwa, tare da kare masu saye daga ha\u0257arin matsalolin lafiya.<\/p>\n<p><em>Fassara: Safiyah Abdulkadir<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Khadijah Aliyu\u00a0 Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka lalace, wa\u0257anda Hukumar Kare Ha\u0199\u0199in Masu Sayen Kaya ta Jihar Kano (KCPC) ta \u0199wace saboda barazanar da suke yi ga lafiyar jama&#8217;a. Umarnin kotun ya biyo bayan shigar da \u0199ara da hukumar ta yi, bayan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":10322,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_hide_featured_image":false,"_jetpack_featured_image_duplicate_dismissed":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2172,39,44,577],"class_list":["post-10318","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-fulawa","tag-kano","tag-kotu","tag-umurni"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261111-WA0005.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10318","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10318"}],"version-history":[{"count":4,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10318\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10323,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10318\/revisions\/10323"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10322"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10318"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10318"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10318"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}