{"id":10279,"date":"2026-11-10T19:47:43","date_gmt":"2026-11-10T19:47:43","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10279"},"modified":"2026-11-10T19:47:43","modified_gmt":"2026-11-10T19:47:43","slug":"shettima-ya-bukaci-yan-najeriya-su-sake-zaben-tinubu-a-2027","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/shettima-ya-bukaci-yan-najeriya-su-sake-zaben-tinubu-a-2027\/","title":{"rendered":"Shettima Ya Bukaci \u2019Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Mataimakin Shugaban \u0198asa, Kashim Shettima, ya bukaci \u2019yan Najeriya da su goyi bayan sake za\u0253en Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban za\u0253en shekarar 2027, domin ba shi damar kammala ayyukan raya \u0199asa da kuma \u0199arfafa nasarorin da aka samu a \u0199ar\u0199ashin shirin Renewed Hope.<\/p>\n<p>Shettima ya yi wannan kira ne a wajen gangamin ya\u0199in neman za\u0253en shugaban \u0199asa na jam\u2019iyyar APC da aka gudanar a filin wasa na Township da ke Dutse, Jihar Jigawa.<\/p>\n<p>Ya ce gwamnatin Tinubu ta aza tubalin farfa\u0257o da tattalin arziki, bun\u0199asa ababen more rayuwa, \u0199arfafa matasa da sauya fasalin harkokin noma a cikin shekaru uku da suka gabata, don haka akwai bu\u0199atar ci gaba da tafiyar.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa nasarorin da aka samu zuwa yanzu mafari ne na babban sauyi da ake son samu, yana mai cewa Shugaba Tinubu na bu\u0199atar \u0199arin lokaci domin kammala shirye-shiryensa na ci gaban \u0199asa.<\/p>\n<p>Shettima ya ce ayyuka masu muhimmanci da darajarsu ta kai biliyoyin Naira da aka \u0199addamar yayin ziyarar shugaban \u0199asar, sun shaida \u0199o\u0199arin gwamnatin APC na inganta rayuwar al&#8217;umma, samar da ayyukan yi da kuma bai wa matasa \u0199warewar sana&#8217;o&#8217;i.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-10281\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261110-WA0014-300x287.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"287\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261110-WA0014-300x287.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261110-WA0014-1024x981.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261110-WA0014-768x736.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261110-WA0014.jpg 1280w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Shettima ya yi nuni da irin goyon bayan da Tinubu ya bai wa shugabannin Arewa da suka zama shugabannin \u0199asa a baya, yana mai bayyana hakan a matsayin hidima ta \u0199ashin kai ga Najeriya, tare da kira ga &#8216;yan Najeriya da su rama masa wannan alheri.<\/p>\n<p>A yayin ziyarar aiki ta yini guda, Shugaba Tinubu ya \u0199addamar da wasu ayyuka da gwamnatin Jihar Jigawa ta aiwatar \u0199ar\u0199ashin jagorancin Gwamna Umar Namadi, wa\u0257anda suka ha\u0257a da Cibiyar Renewed Hope Technical Services da ke Limawa, Dutse, wadda za ta samar da ayyukan \u0199era kayayyakin masana&#8217;antu, walda da sauran tallafin fasaha.<\/p>\n<p>Cibiyar za ta ha\u0257a gwiwa da Cibiyar Horar da Sana&#8217;o&#8217;i ta Bola Ahmed Tinubu, wadda aka gina domin magance matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa da bun\u0199asa masana&#8217;antu ta hanyar tsarin koyon ssana&#8217;o&#8217;i are da samun ku\u0257i daga aikin samar da kkayayyaki.Mataimakin Shugaban \u0199asar ya kuma \u0199addamar da Cibiyar Fasaha da \u0198ir\u0199ire-\u0198ir\u0199ire ta Renewed Hope, wadda aka tsara domin bun\u0199asa ilimin fasahar zamani da \u0199ir\u0199ire-\u0199ir\u0199ire tsakanin matasan jihar.<\/p>\n<p>A \u0253angaren noma kuwa, Tinubu ya \u0199addamar da kayan aikin noma na zamani da gwamnatin jihar ta saya, wa\u0257anda suka ha\u0257a da taraktoci 400 tare da kayan aikinsu, injinan girbin amfanin gona 60, injinan shuka iri\u00a0 150, injinan shuka shinkafa 150 da injinan feshin maganin kashe \u0199wari 80.<\/p>\n<p>Sauran ayyukan sun ha\u0257a da babbar hanyar mota da ta tashi daga Garu zuwa fadar Sarkin Dutse, wadda ake sa ran za ta rage cunkoson ababen hawa tare da \u0199awata babban birnin jihar.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-10283\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261110-WA0015-208x300.jpg\" alt=\"\" width=\"208\" height=\"300\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261110-WA0015-208x300.jpg 208w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261110-WA0015-710x1024.jpg 710w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261110-WA0015-768x1107.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261110-WA0015.jpg 888w\" sizes=\"auto, (max-width: 208px) 100vw, 208px\" \/><\/p>\n<p>Shettima ya yaba wa Gwamna Namadi bisa daidaita shirye-shiryen ci gaban jihar da manufofin Renewed Hope, ta hanyar zuba jari a fannin koyar da sana&#8217;o&#8217;i, noma na zamani da bun\u0199asa ababen more rayuwa.<\/p>\n<p>Manyan baki da suka halarci gangamin sun ha\u0257a da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; gwamnonin jihohin Zamfara, Borno, Sokoto, Imo, Yobe, Kano da Kwara; mambobin Majalisar Tarayya; tsohon Shugaban Jam&#8217;iyyar APC na \u0198asa, Abdullahi Umar Ganduje; manyan jami&#8217;an gwamnati, jiga-jigan jam&#8217;iyyar da dubban magoya bayanta daga sassa daban-daban na \u0199asar nan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em>Fassara: Safiyah Abdulkadir\u00a0<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria\u00a0 Mataimakin Shugaban \u0198asa, Kashim Shettima, ya bukaci \u2019yan Najeriya da su goyi bayan sake za\u0253en Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban za\u0253en shekarar 2027, domin ba shi damar kammala ayyukan raya \u0199asa da kuma \u0199arfafa nasarorin da aka samu a \u0199ar\u0199ashin shirin Renewed Hope. Shettima ya yi wannan kira ne a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":10282,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_hide_featured_image":false,"_jetpack_featured_image_duplicate_dismissed":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[59,1816,89,1878],"class_list":["post-10279","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-jigawa","tag-shettima","tag-tinubu","tag-zaben-2027"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261110-WA0013.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10279","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10279"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10279\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10284,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10279\/revisions\/10284"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10282"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10279"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10279"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10279"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}