{"id":10274,"date":"2026-11-09T20:25:44","date_gmt":"2026-11-09T20:25:44","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10274"},"modified":"2026-11-09T20:58:01","modified_gmt":"2026-11-09T20:58:01","slug":"jigawa-ta-amfana-da-ayyukan-gwamnatin-tinubu-abdulaziz","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jigawa-ta-amfana-da-ayyukan-gwamnatin-tinubu-abdulaziz\/","title":{"rendered":"Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu \u2013 Abdulaziz"},"content":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria<\/p>\n<p>Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan jama\u2019a, Comrade Abdulaziz Abdulaziz, ya ce shugaban ya cika alkawuran da ya daukar wa al\u2019ummar Jihar Jigawa, don haka ya cancanci sake zabensa a zaben 2027.<\/p>\n<p>Abdulaziz ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Dutse, gabanin ziyarar da Shugaba Tinubu zai kai jihar a ranar Talata.<\/p>\n<p>Ya ce Tinubu ya dade yana da kyakkyawar alaka da manyan jagororin siyasar Jigawa, tare da girmama su da daukacin al\u2019ummar jihar. Yana mai cewa a ziyarar yakin neman zabensa a shekarar 2022, marigayi Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammadu Sunusi, ya bukaci a kammala aikin samar da ruwan sha na Greater Dutse, wanda a yanzu ake ci gaba da gudanarwa.<\/p>\n<p>Dangane da ayyukan more rayuwa, Abdulaziz ya ce gwamnatin tarayya na ci gaba da wasu ayyukan hanyoyi da aka gada daga gwamnatin baya, domin bunkasa zirga-zirgar jama\u2019a da jigilar kayayyaki. Ya ce daga ciki akwai hanyar Kwanar Danja zuwa Tsalle zuwa Hadejia, wadda ta kai kashi 75 cikin 100, da hanyar\u00a0 Kunya zuwa Kanya zuwa Babura, zuwa Babban Mutum, wadda ta kai kashi 82 cikin 100, da kuma hanyar\u00a0 Kano zuwa Maiduguri, baya ga layukan dogo na Kano.zuwa Maradi da Kano zuwa Shuwarin.<\/p>\n<p>Ya kuma lissafa ayyukan gidaje da suka hada da Renewed Hope Estates a Dutse da sauran kananan hukumomi, da gina gidaje 1,500 da ware filaye domin samar da gidaje masu saukin kudi.<\/p>\n<p>A bangaren noma, ya ce daruruwan dubban manoma a Jigawa sun amfana da shirye-shiryen gwamnatin tarayya, wadanda suka hada da noman dabino a hekta 1,042, noman alkama a lokacin rani a hekta 120,000, aikin magudanan ruwa da ban-ruwa na Jahun, da raba kayan aikin gona na Naira biliyan biyar, baya ga tallafin kayan noma.<\/p>\n<p>Dangane da tallafin jin kai, Abdulaziz ya ce shirin Renewed Hope Social Protection Scheme ya raba Naira biliyan 11 da rabi ga mutane sama da 178,000, yayin da shirin Renewed Hope Ward Development Programme ke tallafa wa iyalai masu karamin karfi ta hanyar tallafin kudi da sauran shirye-shiryen dogaro da kai.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-10276\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261109-WA0018-300x197.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"197\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261109-WA0018-300x197.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261109-WA0018-1024x671.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261109-WA0018-768x503.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261109-WA0018.jpg 1280w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ya kara da cewa sama da dalibai miliyan daya a manyan makarantun gaba da sakandare a Arewacin Najeriya suna cin gajiyar shirin lamunin karatu na NELFUND, wanda ya rage wa iyaye nauyin kudin makaranta da sauran bukatun karatu.<\/p>\n<p>Jami\u2019in shugaban kasar ya kuma ce Shugaba Tinubu ya amince da kafa Jami\u2019ar Noma a karamar hukumar Kirikasamma da Kwalejin Horar da \u2019Yan Sanda a Gwaram, baya ga samar da tashar wutar lantarki ta hasken rana mai darajar Naira biliyan daya a Jami\u2019ar Tarayya ta Dutse.<\/p>\n<p>Ya ce wadannan matakai na daga cikin kokarin gwamnati na inganta ilimi da samar da damar karatu ga yara, ba tare da la\u2019akari da halin tattalin arzikin iyayensu ko yankin da suke zaune ba.<\/p>\n<p>Abdulaziz ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta bullo da su sun kara wa jihohi kudaden shiga, lamarin da ya taimaka wa Gwamna Umar Namadi wajen aiwatar da ayyukan raya kasa a Jigawa.<\/p>\n<p>Ya yi kira ga al\u2019ummar jihar da kada su yarda a yaudare su da alkawuran da ba su da tushe, inda ya bukace su da su sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran \u2018yan takarar APC a zaben 2027, domin tabbatar da dorewar ayyukan raya kasa da samar da kyakkyawar makoma ga al\u2019umma.<\/p>\n<p><em>Fassara: Safiyah Abdulkadir<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan jama\u2019a, Comrade Abdulaziz Abdulaziz, ya ce shugaban ya cika alkawuran da ya daukar wa al\u2019ummar Jihar Jigawa, don haka ya cancanci sake zabensa a zaben 2027. Abdulaziz ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1040,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_hide_featured_image":false,"_jetpack_featured_image_duplicate_dismissed":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2168,59,89],"class_list":["post-10274","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ayyukan-tinubu","tag-jigawa","tag-tinubu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/President-Tinubu.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10274","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10274"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10274\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10278,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10274\/revisions\/10278"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1040"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10274"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10274"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10274"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}