{"id":10265,"date":"2026-11-08T16:31:09","date_gmt":"2026-11-08T16:31:09","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10265"},"modified":"2026-11-08T16:31:09","modified_gmt":"2026-11-08T16:31:09","slug":"namadi-ya-%c6%99addamar-da-kwamitin-ya%c6%99in-neman-za%c9%93en-apc-na-2027","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/namadi-ya-%c6%99addamar-da-kwamitin-ya%c6%99in-neman-za%c9%93en-apc-na-2027\/","title":{"rendered":"Namadi Ya \u0198addamar Da Kwamitin Ya\u0199in Neman Za\u0253en APC Na 2027"},"content":{"rendered":"<p style=\"text-align: left\"><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an ha\u0257a kwamitocin ya\u0199in neman za\u0253en shugaban \u0199asa da na gwamna ne wuri guda domin \u0199arfafa ha\u0257in kai da samar da tsari guda da jam\u2019iyyar APC za ta yi amfani da shi wajen ya\u0199in neman za\u0253en 2027.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan \u0199addamar da kwamitin ya\u0199in neman za\u0253en Jigawa na 2027 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Dutse, inda aka nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Namadi.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Namadi ya bayyana gamsuwarsa da yawan mutanen da suka halarci taron, yana mai cewa hakan ya nuna \u0199arfin jam\u2019iyyar APC da ci gaba da kasancewar ta a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Ya ce taron ya \u0199ara masa kwarin gwiwar cewa jam\u2019iyyar APC a shirye take ta samu nasara a dukkan matakan za\u0253en da ke tafe.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Gwamnan ya bu\u0199aci shugabannin jam\u2019iyyar da magoya bayanta su ha\u0257a kai domin ganin an sake za\u0253en Shugaba Tinubu da shi a matsayin gwamna, tare da za\u0253en \u2019yan takarar APC zuwa Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jihar Jigawa.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Namadi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, da yardar Allah, jam\u2019iyyar za ta samu nasara a dukkan za\u0253ukan.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Haka kuma, ya bayyana cewa Jihar Jigawa a shirye take ta cika burin samar wa Shugaba Tinubu \u0199uri\u2019u miliyan biyu a za\u0253en shugaban \u0199asa na 2027.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Gwamnan ya ce yawan mutanen da suka halarci taron \u0199addamar da kwamitin ya \u0199ara masa kwarin gwiwar cewa jihar za ta cimma wannan buri.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Kaddamar da kwamitin ya ha\u0257a manyan shugabannin jam\u2019iyyar da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa \u0199ar\u0199ashin tsari guda, domin tsara ayyukan wayar da kan masu za\u0253e da tattara goyon baya ga Shugaba Tinubu da Gwamna Namadi gabanin babban za\u0253en 2027.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Namadi ne shugaban kwamitin, yayin da aka na\u0257a Alhaji Lawan Ya\u2019u Roni a matsayin Darakta-Janar.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman; tsohon Gwamna, Barista Ali Sa\u2019adu Birnin Kudu; tsohon Gwamna, Sanata Ibrahim Saminu Turaki; da Shugaban APC na jihar, Alhaji Ahmad Garba MK, su ne mataimakan shugaban kwamitin.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Sauran manyan jami\u2019an kwamitin sun ha\u0257a da Sanata Muhammad Ibrahim da Sanata Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin mataimakan shugabanni na Arewa maso Gabas na \u0257aya da na biyu.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Haka kuma, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin da Alhaji Farouk Adamu Aliyu su ne mataimakan shugabanni na Kudu maso Yamma na \u0257aya da na biyu, yayin da Alhaji Isa Gerawa da Hajiya Rabi Ishaq za su kula da Arewa maso Yamma na \u0257aya da na biyu.<\/p>\n<p><em>Fassara: Safiyah Abdulkadir<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ce an ha\u0257a kwamitocin ya\u0199in neman za\u0253en shugaban \u0199asa da na gwamna ne wuri guda domin \u0199arfafa ha\u0257in kai da samar da tsari guda da jam\u2019iyyar APC za ta yi amfani da shi wajen ya\u0199in neman za\u0253en 2027. Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":10262,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_hide_featured_image":false,"_jetpack_featured_image_duplicate_dismissed":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[1205,59,2166,512],"class_list":["post-10265","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-apc","tag-jigawa","tag-kwamitin-neman-zabe","tag-namadi"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261108-WA0007.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10265","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10265"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10265\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10266,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10265\/revisions\/10266"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10262"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10265"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10265"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10265"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}