{"id":10252,"date":"2026-11-03T17:03:20","date_gmt":"2026-11-03T17:03:20","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10252"},"modified":"2026-11-03T18:55:44","modified_gmt":"2026-11-03T18:55:44","slug":"jigawa-hukumar-jin-dadin-alhazai-ta-kafa-kwamitin-tantance-bayanan-maniyyatan-2027","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jigawa-hukumar-jin-dadin-alhazai-ta-kafa-kwamitin-tantance-bayanan-maniyyatan-2027\/","title":{"rendered":"Jigawa: Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Kafa Kwamitin Tantance Bayanan Maniyyatan 2027"},"content":{"rendered":"<h3><strong><em>Daga Usman Muhammad<\/em><\/strong> Zaria<\/h3>\n<p>Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta \u0199addamar da wani kwamiti da zai tattara, tare da yin nazari da kuma tantance bayanan maniyyata aikin Hajjin shekarar 2027.<\/p>\n<p>Daraktan Janar na Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan yayin \u0199addamar da kwamitin a hedikwatar hukumar da ke Dutse.<\/p>\n<p>Ya jaddada muhimmancin tattara sahihan bayanai da tantance su domin tabbatar da ingantaccen shiri da kuma gudanar da aikin Hajjin cikin tsari.<\/p>\n<p>Alhaji Labbo ya bayyana cewa jami&#8217;an gudanarwa uku na hukumar ne za su jagoranci aikin kwamitin, wa\u0257anda suka ha\u0257a da Daraktan Ayyuka, Alhaji Muhammad Garba; Daraktan Gudanarwa da Ku\u0257i, Alhaji Mohammed Umar Sambo; da Babban Akanta, Alhaji Muntari Mohammed.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa dukkan shugabannin shiyyoyin hukumar da mataimakansu a fa\u0257in jihar za su kasance mambobin kwamitin, domin tabbatar da kyakkyawan ha\u0257in gwiwa da tantance bayanan maniyyata yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Daraktan Janar \u0257in ya bayyana cewa wannan aiki na daga cikin muhimman matakan shirye-shiryen Hajji, musamman ganin cewa ana sa ran fara aikin bayar da biza nan ba da jimawa ba.<\/p>\n<p>Ya bu\u0199aci mambobin kwamitin da su gudanar da aikinsu bisa \u0199wazo da gaskiya, tare da tabbatar da cewa an tattara dukkan bayanan da ake bu\u0199ata kuma an tantance su yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Alhaji Labbo ya bayyana cewa hukumar ta kammala kusan kashi 40 cikin 100 na shirye-shiryen aikin Hajjin 2027, tare da cewa yana da yakinin za a kammala sauran ayyukan bisa jadawalin da aka tsara.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa hukumar za ta fitar da jadawalin wayar da kan maniyyata da kuma shirye-shiryen horas da su nan ba da jimawa ba, a dukkan shiyyoyi da \u0199ananan hukumomi 27 na jihar.<\/p>\n<p>Daraktan Janar \u0257in ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa ci gaba da tallafa wa hukumar da kuma jajircewarsa wajen kula da jin da\u0257in Alhazai a jihar.<\/p>\n<p>Ya sake jaddada aniyar hukumar na tabbatar da ingantaccen shiri, kyakkyawan tsari da kuma inganta ayyukan hidima ga maniyyata aikin Hajjin 2027.<\/p>\n<p><em>Fassara: Safiyah Abdulkadir<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta \u0199addamar da wani kwamiti da zai tattara, tare da yin nazari da kuma tantance bayanan maniyyata aikin Hajjin shekarar 2027. Daraktan Janar na Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan yayin \u0199addamar da kwamitin a hedikwatar hukumar da ke Dutse. Ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":10250,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_hide_featured_image":false,"_jetpack_featured_image_duplicate_dismissed":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2113,59,935],"class_list":["post-10252","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hajj2027","tag-jigawa","tag-kwamiti"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/IMG-20261103-WA0009.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10252","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10252"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10252\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10257,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10252\/revisions\/10257"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10250"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10252"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10252"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10252"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}