{"id":10228,"date":"2026-11-02T09:23:35","date_gmt":"2026-11-02T09:23:35","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10228"},"modified":"2026-11-02T09:23:35","modified_gmt":"2026-11-02T09:23:35","slug":"shugaban-majalisar-wakilai-ya-jaddada-muhimmancin-samar-da-ilimi-lafiya-da-tsaro-ga-alumma","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/shugaban-majalisar-wakilai-ya-jaddada-muhimmancin-samar-da-ilimi-lafiya-da-tsaro-ga-alumma\/","title":{"rendered":"Shugaban Majalisar Wakilai Ya Jaddada Muhimmancin Samar Da Ilimi, Lafiya Da Tsaro Ga Al\u2019umma"},"content":{"rendered":"<p>Daga Ibrahim Suleiman, Zaria<\/p>\n<p>Shugaban Majalisar Wakilai ta Nijeriya, Dakta Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa manufar shugabanci ita ce biyan muhimman bu\u0199atun al\u2019umma, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya da tsaron jama\u2019a.<\/p>\n<p>Shugaban ya bayyana hakan ne a \u0198aramar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna, yayin bikin aza harsashin ginin wasu ayyukan raya \u0199asa da kuma \u0199addamar da wasu ayyukan mazabarsa.<\/p>\n<p>A cewarsa, ya kamata kowane yaro da aka saka a makarantar firamare ta gwamnati ya samu aji mai kyau da zai ba shi damar karatu cikin yanayi mai dacewa. Haka kuma, duk macen da ta je neman magani a Chikaji ta samu damar gudanar da gwaje-gwajen lafiya ba tare da yin doguwar tafiya mai wahala ba, yayin da matasa a Bomo su samu damar koyon ilimi, rubuta jarabawa da samun takardun shaidar cancanta.<\/p>\n<p>Ya ce ginin sabon rukunin ajujuwa guda goma, tare da ofisoshi da bandakuna a Makarantar Firamare ta Sa\u2019idu, zai taimaka wajen samar wa yara ingantaccen yanayin karatu.<\/p>\n<p>Abbas ya \u0199ara da cewa sabuwar makarantar sakandare, Cibiyar Karatu ta Jami\u2019ar NOUN da kuma cibiyar rubuta jarabawar kwamfuta (CBT Centre) za su samar wa matasa damar ci gaba da karatu bayan firamare, tare da ba su damar yin gogayya da sauran matasa a wannan zamani na fasahar sadarwa.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa cibiyar kula da lafiya matakin farko mai gadaje 20 da cibiyar gwaje-gwajen lafiya na bu\u0199atar samar musu da kayan aiki da \u0199wararrun ma\u2019aikata, yana mai cewa ginin asibiti ba tare da ma\u2019aikata ba, zai sa marasa lafiya su ci gaba da jiran samun kulawa.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa sabon ofishin \u2019yan sanda da hedikwatar rundunar yankin za su taimaka wajen gaggauta kai \u0257auki, inda ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi bisa matakan da suke \u0257auka wajen kafa rundunar \u2019yan sandan jihohi.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, wanda Sakataren Gwamnatin jihar, Dakta Abdulkadir Mu\u2019azu Meyere, ya wakilta, ya yaba wa Shugaban Majalisar bisa jawo ayyukan ci gaba zuwa \u0199ananan hukumomi takwas na shiyyar Sanata ta \u018aaya. Ya kuma yi kira ga al\u2019ummar Sabon Gari da su za\u0253i \u2019yan takarar jam\u2019iyyar APC daga sama har \u0199asa.<\/p>\n<p>Haka kuma, \u0257an takarar Sanata na APC a Shiyyar Sanata ta \u018aaya, kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Mukhtar Ramalan Yero, ya bu\u0199aci al\u2019ummar Sabon Gari da su tabbatar da samun cikakkiyar nasara ga APC a za\u0253uka masu zuwa.<\/p>\n<p>Bikin aza harsashin gine-ginen ya samu halartar jiga-jigan jam\u2019iyyar APC da sarakunan gargajiya da kuma dimbin magoya bayan jam\u2019iyyar.<\/p>\n<h1><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/h1>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Ibrahim Suleiman, Zaria Shugaban Majalisar Wakilai ta Nijeriya, Dakta Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa manufar shugabanci ita ce biyan muhimman bu\u0199atun al\u2019umma, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya da tsaron jama\u2019a. Shugaban ya bayyana hakan ne a \u0198aramar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna, yayin bikin aza harsashin ginin wasu ayyukan raya \u0199asa da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10229,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_hide_featured_image":false,"_jetpack_featured_image_duplicate_dismissed":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1131],"class_list":["post-10228","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kakaki"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/11\/04e966b3-c9bd-412d-a2f8-ea9afc3567de.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10228","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10228"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10228\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10230,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10228\/revisions\/10230"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10229"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10228"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10228"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10228"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}