{"id":10214,"date":"2026-10-28T14:09:23","date_gmt":"2026-10-28T14:09:23","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10214"},"modified":"2026-10-28T14:09:23","modified_gmt":"2026-10-28T14:09:23","slug":"katsina-dalibai-64-sun-jikkata-bayan-an-musu-rigakafin-cutar-tsargiya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/katsina-dalibai-64-sun-jikkata-bayan-an-musu-rigakafin-cutar-tsargiya\/","title":{"rendered":"Katsina: Dalibai 64 Sun Jikkata Bayan An Musu Rigakafin Cutar Tsargiya"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Isma\u2019il Adamu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>A\u0199alla dalibai 64 na makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke Batagarawa, a jihar Katsina, aka garzaya da su asibiti biyo bayan rigakafin cutar Tsargiya da jami\u2019an lafiya suka musu.<\/p>\n<p>Rahotanni sun bayyana cewa daliban sun yi fama da amai, ciwon ciki, jiri da rashin jin da\u0257in jiki, lamarin da ya sa mahukuntan makarantar garzayawa da su asibitin \u0199ashi na Amadi Rimi da kuma asibitin mata da yara na Turai Yar\u2019Adua da ke Katsina.<\/p>\n<p>Cutar Tsargiya, wacce aka fi sani da Bilharzia a Turance, cuta ce da \u0199wayoyin cuta masu ala\u0199a da tsutsotsi ke haddasawa, kuma galibi ana kamuwa da ita ta hanyar hul\u0257a da gurbataccen ruwan sha ko na wasu hanyoyin ruwa.<\/p>\n<p>Yayin da wasu jami\u2019an asibitoci suka bayyana alamomin da daliban suka nuna a matsayin abubuwan da kan faru bayan shan maganin.<\/p>\n<p>Wasu likitoci biyu da suka zanta da\u00a0 Rediyon Najeriya bisa shara\u0257in \u0253oye sunayensu, sun danganta lamarin da yiwuwar an ba daliban magani fiye da kima.<\/p>\n<p>\u018aaya daga cikin likitocin ya ce ya ziyarci asibitin, inda ya ga dalibai da dama cikin mawuyacin hali.<\/p>\n<p>Wani likita a asibitin Turai Yar\u2019Adua kuwa, ya yi zargin cewa an \u0199ayyade adadin alluran maganin Praziquantel da za a ba daliban ne bisa tsayinsu, maimakon shekarunsu, lamarin da ya haifar da tambayoyi kan ko an bi \u0199a\u2019idojin bayar da maganin yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Wasu daliban sun bayyana cewa an ba su allura daga \u0257aya zuwa hu\u0257u, yayin da aka yi zargin cewa ba a sanar da iyayensu ba kafin ba su maganin.<\/p>\n<p>Masana lafiya sun kuma nuna damuwa kan dalilin da ya sa ba a tantance lafiyar kowane dalibi ba kafin ba shi maganin ba. Sun jaddada muhimmancin yin binciken lafiya da ya dace domin tabbatar da bu\u0199atar shan maganin da kuma tabbatar da cewa an ba da shi cikin aminci.<\/p>\n<p>Binciken Rediyon Najeriya ya kuma nuna cewa an ba dalibai da dama maganin ne ba tare da sun ci abinci ba, bayan dawowarsu makaranta daga hutu da misalin \u0199arfe 11 na safe. Dalibai da iyaye da aka zanta da su sun ce ba a ba daliban abinci ba kafin ko bayan shan allunan maganin.<\/p>\n<p>A nata \u0253angaren, \u0199ungiyar ha\u0257in gwiwar \u0199ungiyoyin fararen hula ta jihar Katsina ta bu\u0199aci gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tana mai bayyana shi a matsayin babban yanayi na gaggawar lafiya.<\/p>\n<p>Shugaban \u0199ungiyar, AbdurRahman Abdullahi, ya ce ya kamata hukumomin da abin ya shafa su binciki yadda aka bada maganin, ciki har da amfani da tsayi wajen \u0199ayyade adadinsa, yadda aka kula da batun abinci da kuma matakan da aka tanada domin magance yiwuwar illolin maganin.<\/p>\n<p>Ya bu\u0199aci ma\u2019aikatun ilimin firamare da sakandare da na lafiya na jihar su gano hakikanin abin da ya faru, su tabbatar da duk wani sakaci da aka yi, sannan su \u0257auki matakan da za su hana sake faruwar irin wannan lamari.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar \u2019yan sandan jihar Katsina, SP Abubakar-Sadiq Aliyu, ya sanya wa hannu, rundunar ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta musanta rahotannin da ake ya\u0257awa a kafafen sada zumunta na cewa wasu dalibai sun mutu.<\/p>\n<p>Rundunar \u2019yan sandan ta ce lamarin ya biyo bayan wani rahoton zargin barkewar cutar Tsargiya da shugaban makarantar, Sanusi Maude, ya kai asibitin makarantar. A cewar sanarwar, jami\u2019an lafiya sun ba dalibai sama da 700 maganin Praziquantel, a rukuni biyu.<\/p>\n<p>Rukunin farko da aka ba maganin ranar Juma\u2019a, 24 ga Oktoba, ba su nuna wata matsala ba, yayin da daliban rukuni na biyu, wa\u0257anda aka ba maganin ranar Litinin, suka fara nuna alamomin rashin lafiya. Yawancin daliban da abin ya shafa sun samu kulawar likitoci, kuma an sallame su daga asibiti.<\/p>\n<p><em>Fassara: Safiyah Abdulkadir<\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Isma\u2019il Adamu\u00a0 A\u0199alla dalibai 64 na makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke Batagarawa, a jihar Katsina, aka garzaya da su asibiti biyo bayan rigakafin cutar Tsargiya da jami\u2019an lafiya suka musu. Rahotanni sun bayyana cewa daliban sun yi fama da amai, ciwon ciki, jiri da rashin jin da\u0257in jiki, lamarin da ya sa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":10218,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[248,145,2159],"class_list":["post-10214","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-dalibai","tag-katsina","tag-tsargiya"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261028-WA0009.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10214","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10214"}],"version-history":[{"count":4,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10214\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10219,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10214\/revisions\/10219"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10218"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10214"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10214"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10214"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}