{"id":10203,"date":"2026-10-27T09:11:09","date_gmt":"2026-10-27T09:11:09","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10203"},"modified":"2026-10-27T09:52:16","modified_gmt":"2026-10-27T09:52:16","slug":"najeriya-za-ta-fara-kera-makamai-da-kayayyakin-tsaro-masu-yawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/najeriya-za-ta-fara-kera-makamai-da-kayayyakin-tsaro-masu-yawa\/","title":{"rendered":"Nijeriya Za Ta Fara Kera Makamai Da Kayayyakin Tsaro Masu Yawa"},"content":{"rendered":"<p>Daga Shindong Bala, Kaduna<\/p>\n<p>Nijeriya za ta fara kera makamai da sauran kayayyakin tsaro , domin amfanin \u0199asar da kuma fitar da su zuwa \u0199asashen waje, musamman sauran \u0199asashen Afirka.<\/p>\n<p>Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, ne ya bayyana hakan a wajen bu\u0257e bikin baje kolin kayayyakin tsaro na farko a Afirka, wanda aka gudanar a Legas.<\/p>\n<p>Wata sanarwa da Babbar Jami\u2019ar Ya\u0257a Labarai ta Ma\u2019aikatar Tsaro, Queenet Iheoma-Hart, ta sanya wa hannu, ta ce ministan ya yi kira ga masu zuba jari na cikin gida da na \u0199asashen waje da su yi amfani da damar bikin wajen zuba jari a masana\u2019antar tsaro ta Najeriya.<\/p>\n<p>Janar Christopher Musa ya jaddada cewa kera kayayyakin tsaro a cikin gida zai \u0199arfafa \u0199arfin tsaron \u0199asar, tare da samar da damarmaki don bun\u0199asa tattalin arziki da ci gaba.<\/p>\n<p>Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya a shirye take ta kulla ha\u0257in gwiwa a fannin tsaro, bisa amincewa da juna da kuma mutunta juna.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya bayyana cewa barazanar tsaro na \u0199ara rincabewa, lamarin da ke bu\u0199atar \u0199arfafa ha\u0257in gwiwa tsakanin \u0199asashen Afirka da \u0199wararrun masu \u0199ir\u0199irar fasahohi a duniya.<\/p>\n<p>Ya yi kira ga abokan hul\u0257a a fannin tsaro da masu \u0199ir\u0199irar basirar <em>AI<\/em> da sauran sabbin fasahohi da su ha\u0257a kai da Najeriya wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a fa\u0257in nahiyar Afirka.<\/p>\n<p>Haka kuma, Shugaba Tinubu ya bu\u0199aci mahalarta taron da su yi amfani da bikin wajen musayar ilimi, gudanar da tattaunawar ha\u0257in gwiwa tsakanin \u0199asashe biyu, sanya hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna da kuma bincika damarmakin zuba jari a Najeriya.<\/p>\n<p>Darakta-Janar na Kamfanin Masana\u2019antar Tsaro ta Najeriya, Manjo Janar B. I. Alaya, ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa ci gaba da goyon bayan da yake bai wa kamfanin, tare da al\u0199awarin \u0199ara \u0199arfin samar da kayayyakin tsaro.<\/p>\n<p>Bayan kammala bikin bu\u0257e taron, ministan tsaron ya zagaya rumfunan baje kolin kayayyaki, inda aka nuna kayayyakin tsaro daga \u0199asashe daban-daban. Haka kuma, ya gudanar da wani babban taron tattaunawa da Kwamandan Rundunar Sojin Amurka mai kula da Afirka (<em>United States Africa Command<\/em>).<\/p>\n<p>Baje kolin, wanda ya ha\u0257a masu ruwa da tsaki a fannin tsaro daga Najeriya da sauran \u0199asashe, na da nufin inganta ha\u0257in gwiwa, \u0199ir\u0199ira da bun\u0199asa fasahohi, da kuma jawo zuba jari a fannin tsaro.<\/p>\n<p>Taron ya samu halartar Babban Hafsan Tsaron Najeriya, hafsoshin rundunonin soji masu kan aiki da wa\u0257anda suka yi ritaya, shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dokoki ta \u0198asa, da kuma wakilai daga \u0199asashen Afirka sama da 20.<\/p>\n<p><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Shindong Bala, Kaduna Nijeriya za ta fara kera makamai da sauran kayayyakin tsaro , domin amfanin \u0199asar da kuma fitar da su zuwa \u0199asashen waje, musamman sauran \u0199asashen Afirka. Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, ne ya bayyana hakan a wajen bu\u0257e bikin baje kolin kayayyakin tsaro na farko a Afirka, wanda [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10206,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[2157],"class_list":["post-10203","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-makamai"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/37e6b9bc-f57c-4c52-91ea-c326733718ac.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10203","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10203"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10203\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10209,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10203\/revisions\/10209"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10206"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10203"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10203"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10203"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}