{"id":10199,"date":"2026-10-27T09:05:17","date_gmt":"2026-10-27T09:05:17","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10199"},"modified":"2026-10-27T09:53:38","modified_gmt":"2026-10-27T09:53:38","slug":"ba-za-a-amince-da-raba-kafa-ba-zabukan-2027-ministan-yada-labarai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ba-za-a-amince-da-raba-kafa-ba-zabukan-2027-ministan-yada-labarai\/","title":{"rendered":"Ba Za a Amince da Raba Kafa a Zabukan 2027 Ba \u2014 Ministan Yada Labarai"},"content":{"rendered":"<p>Daga Aliyu Lawal, Minna<\/p>\n<p>Ministan Ya\u0257a Labarai da Wayar da Kan Al\u2019umma, Mohammed Idris, ya bu\u0199aci mambobin jam\u2019iyyar APC da su tabbatar sun za\u0253i dukkan \u2019yan takarar jam\u2019iyyar da ke neman mu\u0199aman za\u0253e a matakai daban-daban, daga sama har \u0199asa, a babban za\u0253en shekarar 2027, domin tabbatar da nasarar jam\u2019iyyar.<\/p>\n<p>Sai dai ya garga\u0257e su kan raba kafa ta hanyar za\u0253ar \u0257an takarar APC a wani mataki, sannan su za\u0253i \u0257an wata jam\u2019iyyar siyasa a wani matakin. Ya ce hakan ba daidai ba ne, kuma jam\u2019iyyar ba za ta amince da irin wannan hali ba.<\/p>\n<p>Ministan, Mohammed Idris, wanda ya yi magana a madadin Kwamitin Ya\u0199in Neman Za\u0253en Shugaban \u0198asa na APC, ya bayyana hakan ne a Abuja yayin bikin rantsar da Kwamitin Ya\u0199in Neman Za\u0253en Shugaban \u0198asa da Gwamna na APC a Minna, babban birnin Jihar Neja.<\/p>\n<p>Ya ce APC za ta yi nasara a babban za\u0253en 2027 bisa la\u2019akari da ayyukan da jam\u2019iyyar ta gudanar domin samar wa \u2019yan Najeriya ribar dimokura\u0257iyya, musamman a matakin \u0199ananan hukumomi da sauran al\u2019ummomin \u0199asa.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa jam\u2019iyyar za ta yi kamfen ne bisa nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu cikin shekaru uku da rabi, wa\u0257anda suka ha\u0257a da bun\u0199asa ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, noma da kuma farfa\u0257o da tattalin arzikin Najeriya, da sauran ayyukan da gwamnatin ta gudanar.<\/p>\n<p>A cewar Idris Malagi, za\u0253en Ambasada Ahmed Musa Ibeto da Gwamna Mohammed Umar Bago ya yi a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Ya\u0199in Neman Za\u0253en Shugaban \u0198asa da Gwamna na APC ya dace kuma ya zo a kan lokaci, kasancewar yana daga cikin \u2019yan siyasar da suka fi \u0199warewa a mu\u0199aman siyasa daban-daban.<\/p>\n<p>Ya kuma bu\u0199aci mambobin kwamitin da su gudanar da ayyukansu cikin himma da gaskiya domin cimma manufofin da aka tsara.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jihar za ta samar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu \u0199uri\u2019u miliyan biyu a za\u0253en 2027.<\/p>\n<p>Mohammed Umar Bago ya amince cewa Shugaba Tinubu yana ba su isassun ku\u0257a\u0257e, yana mai cewa yana son al\u2019ummar Jihar Neja su za\u0253i Tinubu domin jihar ta ci gaba da samun \u0199arin ku\u0257a\u0257en da za su taimaka wajen kammala ayyukan raya \u0199asa da ake gudanarwa.<\/p>\n<p>Gwamnan ya kuma bayyana shirinsa na gudanar da bikin \u0199addamar da wani babban kwamitin ya\u0199in neman za\u0253en shugaban \u0199asa da gwamna na APC a Minna a mako mai zuwa. Ya ce ko dai shugaban \u0199asa, mataimakinsa, shugaban Majalisar Dattawa, shugaban Majalisar Wakilai ko kuma shugaban jam\u2019iyyar APC na \u0199asa ne zai jagoranci \u0199addamarwar.<\/p>\n<p>A jawabinsa, Darakta-Janar na Kwamitin Ya\u0199in Neman Za\u0253en Shugaban \u0198asa da Gwamna na APC, Ambasada Ahmed Musa Ibeto, ya gode wa Gwamna Bago bisa amincewar da ya nuna masa.<\/p>\n<p>Sai dai ya yi al\u0199awarin ba zai yi wasa da wannan amana ba, yana mai jaddada cewa \u0199arfin kowane kwamitin ya\u0199in neman za\u0253e yana dogara ne da ha\u0257in kai da aiki tare domin tabbatar da nasarar jam\u2019iyya. Ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun cimma burinsu.<\/p>\n<p><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aliyu Lawal, Minna Ministan Ya\u0257a Labarai da Wayar da Kan Al\u2019umma, Mohammed Idris, ya bu\u0199aci mambobin jam\u2019iyyar APC da su tabbatar sun za\u0253i dukkan \u2019yan takarar jam\u2019iyyar da ke neman mu\u0199aman za\u0253e a matakai daban-daban, daga sama har \u0199asa, a babban za\u0253en shekarar 2027, domin tabbatar da nasarar jam\u2019iyyar. Sai dai ya garga\u0257e su [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10205,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2155],"class_list":["post-10199","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-raba-kafa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/f868779d-52b8-49f5-8e68-a9703c187fc7-1.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10199","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10199"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10199\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10210,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10199\/revisions\/10210"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10205"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10199"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10199"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10199"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}