{"id":10193,"date":"2026-10-27T05:20:54","date_gmt":"2026-10-27T05:20:54","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10193"},"modified":"2026-10-27T08:38:26","modified_gmt":"2026-10-27T08:38:26","slug":"yan-sanda-sun-tabbatar-kashe-sheikh-yahaya-masussuka-a-dutsin-ma","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/yan-sanda-sun-tabbatar-kashe-sheikh-yahaya-masussuka-a-dutsin-ma\/","title":{"rendered":"Su Waye Suka Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma"},"content":{"rendered":"<p>Wasu \u2019yan bindiga da ake zargi da aikata laifuka sun kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a gidansa da ke \u0198aramar Hukumar Dutsin-Ma ta Jihar Katsina.<\/p>\n<p>An kai wa malamin harin ne da misalin \u0199arfe 9 na dare a \u0199ofar gidansa, inda maharan suka bu\u0257e wuta a kansa da wani mutum da ke tare da shi.<\/p>\n<p>Daga bisani, an garzaya da wa\u0257anda harin ya rutsa da su zuwa Babban Asibitin Dutsin-Ma domin ba su agajin gaggawa, amma bayan wasu mintuna aka tabbatar da rasuwarsu.<\/p>\n<p>Mazauna Dutsin-Ma sun bayyana cewa sunan mutum na biyu da harin ya rutsa da shi Malam Adamu ne, wanda ake kyautata zaton cewa harin ya same shi ne bisa kuskure.<\/p>\n<p>Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun isa wurin ne a kan babur, inda suka yi wa wa\u0257anda abin ya shafa kwanton \u0253auna jim ka\u0257an bayan kammala wani taro da aka gudanar a gidan Sheikh Masussuka.<\/p>\n<p>Ya zuwa lokacin ha\u0257a wannan rahoto, ba a bayyana cikakken bayani game da harin, ko su waye maharan, ko kuma dalilin da ya sa suka kai harin ba.<\/p>\n<p>A halin da ake ciki, kisan ya jefa mazauna yankin cikin jimami, musamman mabiyan malamin.<\/p>\n<p>Rundunar \u2019Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa tana ci gaba da \u0199o\u0199arin gano wa\u0257anda suka aikata laifin domin kamo su tare da gurfanar da su a gaban shari\u2019a.<\/p>\n<p>Wata sanarwa da Jami\u2019in Hul\u0257a da Jama\u2019a na rundunar, DSP Abubakar-Sadiq Aliyu, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa wasu mutane biyu \u0257auke da makamai, wa\u0257anda ke kan babur, sun bu\u0257e wuta tare da raunata mutanen biyu har lahira.<\/p>\n<p>Sanarwar ta ce: \u201cBayan samun rahoton faruwar lamarin, Jami\u2019in \u2019Yan Sanda na Sashen Dutsin-Ma ya jagoranci tawagar jami\u2019an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru. Nan take aka garzaya da wa\u0257anda abin ya shafa zuwa asibiti mafi kusa domin ba su kulawar gaggawa amma abin takaici, likitan da ya duba su ya tabbatar da rasuwarsu.<\/p>\n<p>\u201cKwamishinan \u2019Yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura jami\u2019an rundunonin musamman zuwa yankin.<\/p>\n<p>\u201cKwamishinan \u2019Yan Sandan ya mi\u0199a sa\u0199on ta\u2019aziyyarsa ga iyalai da abokai da mabiyan wa\u0257anda suka rasu, da kuma al\u2019ummar \u0198aramar Hukumar Dutsin-Ma, bisa wannan babban rashi.<\/p>\n<p>Isma\u2019il Adamu<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wasu \u2019yan bindiga da ake zargi da aikata laifuka sun kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a gidansa da ke \u0198aramar Hukumar Dutsin-Ma ta Jihar Katsina. An kai wa malamin harin ne da misalin \u0199arfe 9 na dare a \u0199ofar gidansa, inda maharan suka bu\u0257e wuta a kansa da wani mutum da ke [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10195,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2154],"class_list":["post-10193","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-masussuka"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/IMG-20261027-WA0009.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10193","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10193"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10193\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10198,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10193\/revisions\/10198"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10195"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10193"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10193"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10193"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}