{"id":10172,"date":"2026-10-21T13:05:01","date_gmt":"2026-10-21T13:05:01","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10172"},"modified":"2026-10-21T13:05:01","modified_gmt":"2026-10-21T13:05:01","slug":"jihar-naija-ta-dauki-matakan-gaggawa-sakamakon-bullar-cutar-ebola-a-abuja","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jihar-naija-ta-dauki-matakan-gaggawa-sakamakon-bullar-cutar-ebola-a-abuja\/","title":{"rendered":"Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja"},"content":{"rendered":"<p>Daga Aliyu Lawal<\/p>\n<p>Ma&#8217;aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama&#8217;a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana, biyo bayan tabbatar da bullar cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya Abuja.<\/p>\n<p>Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Murtala Muhammad Bagana ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Minna, inda ya ce matakan da jihar ta \u0257auka na rigakafi ne, domin \u0199arfafa sa-ido, gano masu \u0257auke da cutar da wuri, da kuma \u0257aukar matakan gaggawa idan an samu wanda ake zargi da kamuwa da ita.<\/p>\n<p>Dakta Bagana ya tabbatar wa al&#8217;ummar jihar cewa har yanzu ba a gano ko da mutum \u0257aya da ya kamu da cutar Ebola a Jihar Nijar ba.<\/p>\n<p>Wannan mataki ya biyo bayan sanarwar da Gwamnatin Tarayya ta fitar a ranar Talata, 20 ga Oktoban 2026, inda ta tabbatar da samun wacce\u00a0 ta kamu da cutar Ebola, wadda ta shigo Najeriya daga Uganda. A halin yanzu, an ke\u0253e ta, inda take samun kulawar jinya, yayin da hukumomin lafiya ke sa-ido kan mutane 44 da aka gano sun yi mu&#8217;amala ta kusa da shi.<\/p>\n<p>Kwamishinan ya ce yawan zirga-zirgar mutane da harkokin kasuwanci tsakanin Jihar Nijar da Babban Birnin Tarayya Abuja ya sa ya zama wajibi jihar ta \u0199ara tsaurara matakan sa-ido da shirin ko-ta-kwana.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa ma&#8217;aikatar na aiki tare da Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Ya\u0257uwa ta Najeriya (NCDC), Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauran abokan hul\u0257a na \u0199asa da \u0199asa domin tabbatar da shirye-shiryen tunkarar cutar a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p>Dakta Bagana ya ce an umurci dukkan cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu a Jihar Nijar da su gaggauta kai rahoton duk wanda ake zargin ya kamu da cutar Ebola domin a gudanar da bincike tare da \u0257aukar matakan da suka dace.<\/p>\n<p>Ma&#8217;aikatar ta fitar da lambobin wayar gaggawa da za a kira domin kai rahoton wa\u0257anda ake zargin sun kamu da cutar kamar haka: Daraktan Kiwon Lafiyar Jama&#8217;a, 0703 458 3079; Masanin Cutar Annoba na Jiha, 0807 721 3070; Jami&#8217;in Sa-Ido da Sanar da Cututtuka na Jiha (DSNO), 0807 529 1989; da kuma layin kyauta na NCDC na \u0199asa, 6232.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aliyu Lawal Ma&#8217;aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama&#8217;a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana, biyo bayan tabbatar da bullar cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya Abuja. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Murtala Muhammad Bagana ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Minna, inda ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":10174,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[2104,532],"class_list":["post-10172","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-ebola","tag-naija"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/Niger-state.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10172","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10172"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10172\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10175,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10172\/revisions\/10175"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10174"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10172"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10172"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10172"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}