{"id":10156,"date":"2026-10-20T09:48:37","date_gmt":"2026-10-20T09:48:37","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10156"},"modified":"2026-10-20T09:48:37","modified_gmt":"2026-10-20T09:48:37","slug":"2027-ombugadu-ya-yi-al%c6%99awarin-kawo-%c6%99arshen-rashin-tsaro","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/2027-ombugadu-ya-yi-al%c6%99awarin-kawo-%c6%99arshen-rashin-tsaro\/","title":{"rendered":"2027: Ombugadu Ya Yi Al\u0199awarin kawo \u0198arshen Rashin Tsaro"},"content":{"rendered":"<p>Daga ALIYU MURAKI, LAFIA<\/p>\n<p>\u018aan takara a za\u0253en gwamnan Jihar Nasarawa na jam\u2019iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi al\u0199awarin kawo \u0199arshen matsalar rashin tsaro da kuma bai wa bun\u0199asa ababen more rayuwa fifiko a fa\u0257in jihar, idan aka za\u0253e shi a matsayin gwamna a shekarar 2027.<\/p>\n<p>Dr. Emmanuel Ombugadu ya bayyana hakan ne yayin \u0199addamar da rangadin ya\u0199in neman za\u0253en jam\u2019iyyar PDP na babban za\u0253en shekarar 2027, wanda aka gudanar a \u0198aramar Hukumar Awe ta jihar.<\/p>\n<p>Ya ce gwamnatinsa za ta bai wa tsaro fifiko, yana mai cewa dole ne al\u2019ummar jihar, wa\u0257anda mafi yawansu manoma ne, su samu damar zuwa gonakinsu, su kwana cikin kwanciyar hankali, tare da gudanar da harkokin rayuwarsu ba tare da fargaba ba.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen bun\u0199asa ababen more rayuwa, ciki har da ginawa da gyaran hanyoyi domin sake ha\u0257a al\u2019ummomi da bun\u0199asa harkokin tattalin arziki.<\/p>\n<p>Dr. Emmanuel Ombugadu ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da gina hanyoyin da suka ha\u0257a Akiri da Jihar Filato, da sauran muhimman hanyoyi. Ya kuma yi al\u0199awarin ha\u0257a jihohin Binuwai da Nasarawa da Taraba da Filato ta hanyoyin da za su sau\u0199a\u0199a zirga-zirga da \u0199arfafa ha\u0257in kai da bun\u0199asa kasuwanci.<\/p>\n<p>Da yake nasa jawabin, Shugaban PDP na jihar, Dr. Daniel Gimba, ya ce \u0199addamar da ya\u0199in neman za\u0253en ya nuna aniyar jam\u2019iyyar ta kawo \u0199arshen wahalhalu tare da samar da shugaba na gari wanda zai kai jihar ga ci gaba.<\/p>\n<p>Shi ma da yake magana a madadin sauran \u2019yan takara, \u0257an takarar sanatan Nasarawa ta Kudu na PDP, Dr. Mike Omeri, ya nuna godiyarsa ga magoya baya da mambobin jam\u2019iyyar bisa amincewar da suka nuna musu.<\/p>\n<p>A nasa \u0253angaren, Mukaddashin Shugaban Kwamitin Ya\u0199in Neman Za\u0253en PDP, Mark Ogbole, ya ce jam\u2019iyyar ta za\u0253i fara ya\u0199in neman za\u0253enta na lumana a Awe ne domin isar da sa\u0199onta ga dukkan sassan jihar.<\/p>\n<p>Ya yi al\u0199awarin cewa gwamnatin PDP za ta samar da ayyukan yi ga matasa tare da tallafa wa mata masu sana\u2019o\u2019i domin inganta rayuwarsu da ta iyalansu. Ya jaddada cewa jam\u2019iyyar na neman mulki ne ba domin ta ci za\u0253e ta gudu ba, sai dai domin ta yi aiki wa al\u2019ummar jihar.<\/p>\n<p><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga ALIYU MURAKI, LAFIA \u018aan takara a za\u0253en gwamnan Jihar Nasarawa na jam\u2019iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi al\u0199awarin kawo \u0199arshen matsalar rashin tsaro da kuma bai wa bun\u0199asa ababen more rayuwa fifiko a fa\u0257in jihar, idan aka za\u0253e shi a matsayin gwamna a shekarar 2027. Dr. Emmanuel Ombugadu ya bayyana hakan ne yayin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10157,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[23],"class_list":["post-10156","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-tsaro"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/0c315dbe-27f0-4b14-b857-1e934bc330d4.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10156","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10156"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10156\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10158,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10156\/revisions\/10158"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10157"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10156"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10156"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10156"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}