{"id":10153,"date":"2026-10-20T09:46:39","date_gmt":"2026-10-20T09:46:39","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10153"},"modified":"2026-10-20T09:46:39","modified_gmt":"2026-10-20T09:46:39","slug":"tajudeen-zai-bayyana-rahoton-ayyukan-tinubu-cikin-kwanaki-14","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/tajudeen-zai-bayyana-rahoton-ayyukan-tinubu-cikin-kwanaki-14\/","title":{"rendered":"Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14"},"content":{"rendered":"<p>Daga BELLO WAKILI, Abuja<\/p>\n<p>Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu a Mazabar Tarayya ta Zariya, Jihar Kaduna, Arewa maso Yamma da Najeriya baki \u0257aya cikin kwanaki 14 masu zuwa.<\/p>\n<p>Dr. Abbas ya bayyana hakan ne yayin wani taro tsakanin Shugaba Tinubu da \u0199ungiyar City Boy Movement a Fadar Shugaban \u0198asa da ke Abuja.<\/p>\n<p>Ya ce rahoton da aka yi wa la\u0199abi da PBAT Stewardship Account zai \u0199unshi ayyukan da gwamnati ta aiwatar da wuraren da aka gudanar da su da ku\u0257a\u0257en da aka kashe da kuma matsayin kammala ayyukan, domin bai wa \u2019yan Najeriya damar tantance sahihancin bayanan.<\/p>\n<p>Shugaban Majalisar ya ba da misali da Asibitin Kwararru na Renewed Hope mai gadaje 100 da ke Zariya, wanda aka bu\u0257e a watan Mayun wannan shekara \u0199ar\u0199ashin shirin muradun ci gaba mai \u0257orewa na gwamnatin, sannan aka mi\u0199a shi ga Asibitin Koyarwa na Jami\u2019ar Ahmadu Bello domin gudanar da ayyukansa.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa asibitin, wanda aka samar wa da \u0257akunan tiyata, dakin gwaje-gwaje, na\u2019urar duban ciki da sauran kayan aikin ba da agajin gaggawa, zai inganta samun kiwon lafiya ga mazauna Zariya da yankunan da ke kewaye da ita.<\/p>\n<p>Haka kuma, Shugaban Majalisar ya bu\u0199aci \u0199ungiyar City Boy Movement da ta samar da tsari guda na bayar da rahoton ayyuka da shirya tarukan tattaunawa da al\u2019umma, tare da bai wa \u2019yan \u0199asa damar tantance ayyukan gwamnati da bayyana ra\u2019ayoyinsu kan yadda ake gudanar da mulki.<\/p>\n<p>Ya ro\u0199i Shugaba Tinubu da ya amince da amfani da tsarin PBAT Stewardship Account a matsayin ma\u2019aunin tantance ayyukan duk masu ri\u0199e da mu\u0199aman siyasa, yana mai jaddada cewa ya kamata a auna shugabanni bisa ayyukan da suke yi wa jama\u2019a, maimakon furucin nuna biyayya kawai.<\/p>\n<p>Dr. Abbas ya ce za a fara aiwatar da wannan shiri daga Zariya, da nufin \u0199arfafa gaskiya, ri\u0199on amana da bayyana yadda ake gudanar da mulki.<\/p>\n<p><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu a Mazabar Tarayya ta Zariya, Jihar Kaduna, Arewa maso Yamma da Najeriya baki \u0257aya cikin kwanaki 14 masu zuwa. Dr. Abbas ya bayyana hakan ne yayin wani taro tsakanin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10154,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2150],"class_list":["post-10153","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-taju"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/9f334b5c-1277-47b4-a783-d8112214691c.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10153","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10153"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10153\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10155,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10153\/revisions\/10155"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10154"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10153"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10153"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10153"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}