{"id":10100,"date":"2026-10-05T08:29:47","date_gmt":"2026-10-05T08:29:47","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10100"},"modified":"2026-10-05T08:29:47","modified_gmt":"2026-10-05T08:29:47","slug":"gwamna-dauda-lawal-ya-%c6%99addamar-da-gina-hanyar-kilomita-95-a-tsafe-don-%c6%99arfafa-ayyukan-tsaro","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-dauda-lawal-ya-%c6%99addamar-da-gina-hanyar-kilomita-95-a-tsafe-don-%c6%99arfafa-ayyukan-tsaro\/","title":{"rendered":"Gwamna Dauda Lawal Ya \u0198addamar Da Gina Hanyar Kilomita 95 A Tsafe Don \u0198arfafa Ayyukan Tsaro"},"content":{"rendered":"<h3><strong>Daga Aminu Dalhatu, Gusau<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya \u0199addamar da aikin gina sabuwar hanya mai tsawon kilomita 95 a \u0198aramar Hukumar Tsafe, yana mai cewa aikin zai inganta zirga-zirgar kayayyaki da ayyuka tare da \u0199arfafa ayyukan jami\u2019an tsaro a yankin.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>Gwamna Lawal ya \u0199addamar da aikin ne a ranar Lahadi, inda aka fara gina hanyoyin \u2019Yandoton Daji da Cediya da Doka da \u2019Yan Waren Daji da Hayin Alhaji Bedi da Unguwar Joji da \u2019Yankuzo zuwa Tsafe, tare da gina gadoji guda biyar a \u0198aramar Hukumar Tsafe.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>An raba aikin zuwa matakai biyu, inda kamfanin SKY Construction Company ya samu kwangilar matakin farko mai tsawon kilomita 47, yayin da Setraco Construction Company Limited zai gudanar da mataki na biyu mai tsawon kilomita 48.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>Da yake jawabi yayin \u0199addamar da aikin, Gwamna Lawal ya ce hanyar ta ratsa wasu al\u2019ummomi da galibinsu manoma ne, wa\u0257anda ke taka muhimmiyar rawa wajen bun\u0199asar tattalin arzikin Jihar Zamfara.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>Ya ce gwamnatin jihar ta \u0257auki alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama\u2019a da muhimmanci, shi ya sa ta sanya aikin hanyar cikin manyan ayyukan da za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Zamfara.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u201cGwamnatin da ke da alhaki ta himmatu wajen tabbatar da tsaro da walwalar al\u2019ummarta. Shi ya sa muka ba wannan aikin hanya muhimmiyar fifiko a matsayin wani babban mataki na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Zamfara,\u201d in ji shi.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>Gwamnan ya ce sake gina hanyar zai sau\u0199a\u0199a zirga-zirgar kayayyaki tare da inganta tafiye-tafiyen jami\u2019an tsaro, abin da zai \u0199ara musu \u0199arfin gudanar da ayyukansu da kuma saurin kai \u0257auki yayin fuskantar barazana ko hare-hare.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>Ya bayyana aikin a matsayin wani \u0253angare na babban shirin farfa\u0257o da ababen more rayuwa a fa\u0257in jihar.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>A cewarsa, daga hanyar Gusau\u2013Magami\u2013Dansadau zuwa hanyar Zurmi\u2013Rukudawa, da kuma hanyar Mallamawa\u2013Bukkuyum wadda ke da reshe zuwa Masamar Mudi, gwamnatin jihar na ci gaba da ha\u0257a al\u2019ummomi da juna tare da magance gibin ababen more rayuwa da aka da\u0257e ana fama da shi.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>Gwamna Lawal ya ce gwamnati ta fahimci muhimmancin ingantattun hanyoyi wajen tabbatar da zirga-zirga cikin aminci, sau\u0199a\u0199a safarar kayayyaki da bun\u0199asa tattalin arziki.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>Ya \u0199ara da cewa manufar aikin ba ta tsaya ga samar da hanyar sufuri ka\u0257ai ba, domin ana sa ran zai \u0199ara ha\u0253aka harkokin tattalin arziki, inganta tsaro da kuma kyautata rayuwar al\u2019ummomin da aikin ya shafa.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u201cMun fahimci irin gaggawar da ake da ita saboda mawuyacin halin da wa\u0257annan al\u2019ummomi ke ciki, kuma mun \u0199uduri aniyar bin jadawalin aikin yadda ya kamata domin tabbatar da kammala shi cikin lokaci,\u201d in ji Gwamnan.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>Gwamna Lawal ya kuma umarci Ma\u2019aikatar Ayyuka da Bun\u0199asa Ababen More Rayuwa da ta tabbatar da tsauraran matakan sa ido kan aikin, tabbatar da inganci da kuma bin \u0199a\u2019idojin aikin injiniya da aka amince da su a duk tsawon lokacin gudanar da aikin.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>Ya ce kamfanonin da suka samu kwangilar ayyukan gwamnati dole ne su fahimci cewa Gwamnatin Jihar Zamfara na bu\u0199atar a samu cikakken amfani da ku\u0257in da aka kashe, ingantaccen aiki da kuma ababen more rayuwa da za su iya \u0257orewa na dogon lokaci.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u00a0<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>\u201cIna fatan wannan hanya za ta inganta sufuri da tsaro, ta zama wata gada da za ta \u0199ara ha\u0257a al\u2019ummomi wuri guda, tare da zama alamar \u0199udirinmu na bun\u0199asa ababen more rayuwa domin ci gaba da wadata Jihar Zamfara,\u201d in ji Gwamna Lawal.<\/strong><\/h3>\n<h3><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/h3>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya \u0199addamar da aikin gina sabuwar hanya mai tsawon kilomita 95 a \u0198aramar Hukumar Tsafe, yana mai cewa aikin zai inganta zirga-zirgar kayayyaki da ayyuka tare da \u0199arfafa ayyukan jami\u2019an tsaro a yankin. \u00a0 Gwamna Lawal ya \u0199addamar da aikin ne a ranar Lahadi, inda aka [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10101,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[667],"class_list":["post-10100","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hanya"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/bccb3f64-cd7a-43e8-87c6-795c38a972d5.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10100","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10100"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10100\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10102,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10100\/revisions\/10102"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10101"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10100"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10100"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10100"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}