{"id":10097,"date":"2026-10-05T08:28:18","date_gmt":"2026-10-05T08:28:18","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10097"},"modified":"2026-10-05T08:28:18","modified_gmt":"2026-10-05T08:28:18","slug":"gwamna-kefas-ya-zargi-jamian-gwamnatinsa-da-taimaka-wa-ha%c6%99ar-ba-bisa-kaida-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-kefas-ya-zargi-jamian-gwamnatinsa-da-taimaka-wa-ha%c6%99ar-ba-bisa-kaida-ba\/","title":{"rendered":"Gwamna Kefas Ya  Zargi Jami\u2019an Gwamnatinsa Da Taimaka Wa Ha\u0199ar Ba Bisa Ka\u2019ida Ba"},"content":{"rendered":"<p><strong>Daga Sani Sulaiman, Jalingo<\/strong><\/p>\n<p>Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya zargi wasu jami\u2019an gwamnati da hannu wajen taimaka wa ayyukan ha\u0199ar ma\u2019adinai ba bisa ka\u2019ida ba a sassa daban-daban na jihar, inda ya sha alwashin tsaftace harkar ta hanyar samar da sabon tsarin ha\u0199ar ma\u2019adinai cikin gaskiya da bin \u0199a\u2019ida.<\/p>\n<p>Gwamna Kefas ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tattaunawa da masu ha\u0199ar ma\u2019adinai da \u0199anana da matsakaita, wanda aka gudanar a Banquet Hall na TY Danjuma House da ke Jalingo.<\/p>\n<p>Taron mai taken <strong>\u201c<\/strong><strong><span style=\"font-weight: normal\">Ayyukan Ha\u0199ar Ma\u2019adinai \u0198anana da Matsakaita, Tasirinsu Ga Muhalli da Al\u2019ummomin Masu Ha\u0199ar Ma\u2019adinai, da Hanyar Samun Ci Gaba Mai \u0257orewa a Jihar Taraba\u201d<\/span><\/strong><b>,<\/b> ya samu halartar jami\u2019an gwamnati da \u0199ungiyoyin masu ha\u0199ar ma\u2019adinai da wakilan al\u2019ummomin da ake gudanar da ayyukan ha\u0199ar ma\u2019adinai.<\/p>\n<p>Gwamnan ya ce ayyukan ha\u0199ar ma\u2019adinai na \u0199anana da matsakaita na dogaro da rayuwar dubban iyalai a Taraba, don haka ba za a iya haramta su gaba \u0257aya ba, sai dai akwai bu\u0199atar tsara su yadda za a tabbatar da tsaro, bin doka da kuma kare muhalli.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta samar da <strong>\u201cTaraba Responsible Artisanal Mining and Community Health Standards\u201d<\/strong>, wato \u0199a\u2019idojin da za su taimaka wajen kare hanyoyin samun ruwan sha da horar da masu ha\u0199ar ma\u2019adinai da ma\u2019aikatan lafiya, tare da samar da ingantaccen tsarin bayar da rahoton ayyukan da ka iya zama ha\u0257ari.<\/p>\n<p>Kefas ya bu\u0199aci shugabannin \u0199ungiyoyin masu ha\u0199ar ma\u2019adinai da su tallafa wa gwamnati wajen wayar da kan mambobinsu game da manufofi masu aiki da sau\u0199in aiwatarwa, yayin da ya yi garga\u0257in cewa gwamnatinsa ba za ta \u0199ara lamuntar jami\u2019an da ke taimaka wa ayyukan ha\u0199ar ma\u2019adinai ba bisa ka\u2019ida ba.<\/p>\n<p>Tun da farko, Babban Sakataren Hukumar Kula da Ma\u2019adinan \u0198asa, Mista Matsai David Angye, ya bayyana taron a matsayin wanda ya zo a kan lokaci, yana mai cewa manufar gwamnati ba ita ce hana masu ha\u0199ar ma\u2019adinai \u0199anana da matsakaita samun abin dogaro da kai ba, sai dai horar da su da kuma \u0199arfafa musu gwiwa domin gudanar da ayyukansu cikin aminci da inganci.<\/p>\n<p>Wakilan masu ha\u0199ar ma\u2019adinai daga sassa daban-daban na jihar su ma sun gabatar da jawabai tare da mi\u0199a bu\u0199atunsu ga Gwamna Kefas.<\/p>\n<p>A yayin taron, an kuma karrama Gwamna Kefas da lambar yabo ta <strong>\u201cGwamnan Da Ya Fi Son Masu Ha\u0199ar Ma\u2019adinai.\u201d<\/strong><\/p>\n<p><b>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/b><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Sani Sulaiman, Jalingo Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya zargi wasu jami\u2019an gwamnati da hannu wajen taimaka wa ayyukan ha\u0199ar ma\u2019adinai ba bisa ka\u2019ida ba a sassa daban-daban na jihar, inda ya sha alwashin tsaftace harkar ta hanyar samar da sabon tsarin ha\u0199ar ma\u2019adinai cikin gaskiya da bin \u0199a\u2019ida. Gwamna Kefas ya bayyana hakan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10098,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[431],"class_list":["post-10097","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-maadinai"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/18cce3c0-4280-4def-a3f4-7d04f30f0b7c.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10097","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10097"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10097\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10099,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10097\/revisions\/10099"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10098"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10097"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10097"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10097"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}