{"id":10094,"date":"2026-10-05T08:26:26","date_gmt":"2026-10-05T08:26:26","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10094"},"modified":"2026-10-05T08:26:26","modified_gmt":"2026-10-05T08:26:26","slug":"%c9%97an-takarar-gwamnan-accord-a-kebbi-ya-yi-al%c6%99awarin-%c6%99ara-albashin-maaikata-zuwa-n500000","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/%c9%97an-takarar-gwamnan-accord-a-kebbi-ya-yi-al%c6%99awarin-%c6%99ara-albashin-maaikata-zuwa-n500000\/","title":{"rendered":"\u018aan Takarar Gwamnan Accord A Kebbi Ya Yi Al\u0199awarin \u0198ara Albashin Ma\u2019aikata Zuwa N500,000"},"content":{"rendered":"<p><strong>Daga Sani Haruna Dutsin-ma, B\/Kebbi<\/strong><\/p>\n<p>\u018aan takarar jam\u2019iyyar Accord na kujerar gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sani Abdullahi Bunza, ya yi al\u0199awarin biyan ma\u2019aikatan gwamnati mafi \u0199arancin albashi na <strong>naira 500,000<\/strong> a jihar idan aka za\u0253e shi.<\/p>\n<p>Da yake jawabi ga manema labarai a Birnin Kebbi, yayin <strong>Taron Tattaunawa da \u2018Yan Takara<\/strong>, wanda \u0198ungiyar Masu aiko da rahotanno ta Najeriya, reshen Jihar Kebbi, ta shirya, Sani Abdullahi Bunza ya ce albashin da ma\u2019aikatan Najeriya ke kar\u0253a a gida bai yi daidai da halin da ake ciki a \u0199asa ba.<\/p>\n<p>\u018aan takarar ya koka kan yadda wasu manufofin gwamnati marasa farin jini suka jefa ma\u2019aikatan gwamnati cikin damuwa da wahalhalu, yana mai cewa irin wa\u0257annan manufofi na \u0199ara sa ma\u2019aikata zuwa aiki babu karsashi.<\/p>\n<p>Ya tabbatar da cewa ba ya neman kujerar gwamna domin biyan bu\u0199atun kansa ko tara dukiya, sai dai yana takara ne domin <strong>\u2018yantar da Jihar Kebbi da al\u2019ummarta<\/strong>.<\/p>\n<p>\u018aan takarar gwamnan ya bayyana tsaro a matsayin \u0257aya daga cikin manyan abubuwan da zai ba fifiko, yana mai cewa gwamnatocin yanzu a matakai daban-daban ba sa yin isasshen abin da ya kamata wajen kawo \u0199arshen ayyukan \u2018yan bindiga da satar mutane da sauran laifuffuka a jihar da ma \u0199asar baki \u0257aya.<\/p>\n<p>Ya lura cewa tsaron \u0199asa yana da ala\u0199a da mutanen da ke kan madafun iko da iyalansu, yana mai cewa babu wani lokaci da aka ta\u0253a sace gwamna ko Sanata ko \u0257an Majalisar Wakilai ko minista ko wani daga cikin iyalansu.<\/p>\n<p>\u018aan takarar ya yi al\u0199awarin tunkarar matsalar tsaro kai tsaye, domin bai wa al\u2019ummar Kebbi fata da zaman lafiya. Ya kuma ce za a ba \u0253angaren kiwon lafiya kulawa ta musamman, domin kawo \u0199arshen bu\u0199atar \u2018yan Najeriya na zuwa \u0199asashen waje neman magani.<\/p>\n<p>Saboda haka, \u0257an takarar ya yi kira ga masu za\u0253e a fa\u0257in Jihar Kebbi da su yi amfani da hikima wajen za\u0253ensu, tare da ka\u0257a \u0199uri\u2019unsu ga jam\u2019iyyar Accord.<\/p>\n<p><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Sani Haruna Dutsin-ma, B\/Kebbi \u018aan takarar jam\u2019iyyar Accord na kujerar gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sani Abdullahi Bunza, ya yi al\u0199awarin biyan ma\u2019aikatan gwamnati mafi \u0199arancin albashi na naira 500,000 a jihar idan aka za\u0253e shi. Da yake jawabi ga manema labarai a Birnin Kebbi, yayin Taron Tattaunawa da \u2018Yan Takara, wanda \u0198ungiyar Masu [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10095,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2144],"class_list":["post-10094","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-dubu500"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/10\/c95e5fbb-9dba-4895-b847-3b74aa14557c.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10094","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10094"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10094\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10096,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10094\/revisions\/10096"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10095"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10094"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10094"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10094"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}