{"id":10036,"date":"2026-09-29T10:59:04","date_gmt":"2026-09-29T10:59:04","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10036"},"modified":"2026-09-29T10:59:04","modified_gmt":"2026-09-29T10:59:04","slug":"gwamnatin-kebbi-ta-yaba-wa-sojoji-kan-kafa-sabbin-rundunoni-uku","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-kebbi-ta-yaba-wa-sojoji-kan-kafa-sabbin-rundunoni-uku\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Kebbi Ta Yaba Wa Sojoji Kan Kafa Sabbin Rundunoni Uku"},"content":{"rendered":"<p class=\"isselectedend\"><strong>Daga Sani Haruna Dutsin-ma\/ B\/Kebbi<\/strong><\/p>\n<p class=\"isselectedend\">Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce matakin da Hedikwatar Rundunar Sojin Najeriya ta \u0257auka na \u0199arfafa kasancewar sojoji a jihar, ta hanyar kafa da kuma fara aiki da rundunonin soji guda uku masu muhimmanci, abin farin ciki ne kuma abin maraba.<\/p>\n<p class=\"isselectedend\">Kwamishinan Ya\u0257a Labarai da Al\u2019adu na jihar, Yakubu Ahmed BK, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Kebbi, inda ya ce wannan mataki ya nuna \u0199udirin Rundunar Sojin Najeriya na tunkarar matsalolin tsaro da ke addabar Jihar Kebbi musamman da kuma \u0199asar baki \u0257aya.<\/p>\n<p class=\"isselectedend\">Ya bayyana kafa <strong>Brigade mai lamba 28 da Garrison a Birnin Kebbi<\/strong> a matsayin wani muhimmin mataki na \u0199arfafa ayyukan tsaro da inganta \u0199arfin gudanar da ayyukan soji da kuma tabbatar da \u0257aukar matakin gaggawa kan barazanar tsaro da ka iya tasowa, ba a Jihar Kebbi ka\u0257ai ba, har ma da yankunan da ke makwabtaka da ita na jihohin da ke kusa.<\/p>\n<p class=\"isselectedend\">Ahmed BK ya kuma yaba wa gudummawar da sauran hukumomin tsaro ke bayarwa, ciki har da Rundunar \u2019Yan Sandan Najeriya da Hukumar DSS da Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) da mafarauta da sauran \u0199ungiyoyin sa-kai na al\u2019umma, wajen ha\u0257a \u0199arfi don kare rayuka da dukiyoyin jama\u2019a a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p class=\"isselectedend\">Ya ce baya ga Hedikwatar Brigade da ke Birnin Kebbi, fara aiki da <strong>Bataliyar Tankoki mai lamba 281 a Yauri<\/strong> da kuma <strong>Makaman Atillari a Kaoje<\/strong>, zai \u0199ara \u0199arfafa da kuma daidaita ayyukan ya\u0199i da \u2019yan ta\u2019adda da sauran ayyukan soji a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p class=\"isselectedend\">A cewarsa, sabbin matakan da aka \u0257auka na \u0199arfafa ayyukan tsaro sun samo asali ne daga \u0199o\u0199arin da Gwamna Nasir Idris ke yi ba tare da gajiyawa ba, da kuma dagewarsa wajen neman \u0199arin tura jami\u2019an tsaro, tare da samar da isassun ma\u2019aikata, kayan aiki da makamai domin tunkarar matsalolin tsaro na musamman da ke fuskantar jihar, wa\u0257anda kuma suke ci gaba da sauyawa.<\/p>\n<p class=\"isselectedend\">Ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kebbi za ta ci gaba da bai wa dukkan hukumomin tsaro da ke gudanar da ayyukansu a jihar goyon baya da ha\u0257in kai da ya dace, domin su sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya \u0257ora musu na kare rayuka da dukiyoyi da kuma ya\u0199i da aikata laifuka.<\/p>\n<p class=\"isselectedend\">Alhaji Yakubu Ahmed ya yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa salon shugabancinsa mai sauraron jama\u2019a da kuma mai mayar da hankali kan samar da sakamako, wanda ya ce ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban da ake samu a sassa daban-daban na jihar.<\/p>\n<p class=\"isselectedend\">Kwamishinan ya yi kira ga al\u2019ummar Jihar Kebbi da su ci gaba da ba hukumomin tsaro cikakken ha\u0257in kai, ta hanyar gaggauta kai musu sahihan bayanai masu amfani game da ayyuka, wuraren da suke da kuma zirga-zirgar \u2019yan bindiga, \u2019yan tada \u0199ayar baya da sauran masu aikata laifuka.<\/p>\n<p><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Sani Haruna Dutsin-ma\/ B\/Kebbi Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce matakin da Hedikwatar Rundunar Sojin Najeriya ta \u0257auka na \u0199arfafa kasancewar sojoji a jihar, ta hanyar kafa da kuma fara aiki da rundunonin soji guda uku masu muhimmanci, abin farin ciki ne kuma abin maraba. Kwamishinan Ya\u0257a Labarai da Al\u2019adu na jihar, Yakubu Ahmed BK, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10037,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[139],"class_list":["post-10036","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kebbi"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/7b76934b-c67f-494d-ae99-4fb283e06583.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10036","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10036"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10036\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10038,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10036\/revisions\/10038"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10037"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10036"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10036"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10036"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}