{"id":10030,"date":"2026-09-29T10:53:35","date_gmt":"2026-09-29T10:53:35","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10030"},"modified":"2026-09-29T10:53:35","modified_gmt":"2026-09-29T10:53:35","slug":"remasab-ta-bayyana-damuwarta-game-da-tsaftar-muhalli-a-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/remasab-ta-bayyana-damuwarta-game-da-tsaftar-muhalli-a-kano\/","title":{"rendered":"REMASAB Ta Bayyana Damuwarta Game Da Tsaftar Muhalli A Kano"},"content":{"rendered":"<h3>Daga Khadijah Aliyu, Kano<\/h3>\n<p>Hukumar Kula da Shara da Tsaftar Muhalli ta Jihar Kano, REMASAB, ta \u0199ara tsaurara sa ido kan tsaftar muhalli a fa\u0257in jihar, inda ta tura wata tawaga ta musamman domin duba manyan da \u0199ananan hanyoyi da kuma wasu muhimman wurare.<\/p>\n<p>Hakan na \u0199unshe ne cikin wata sanarwa da Jami\u2019in Hul\u0257a da Jama\u2019a na REMASAB, Abubakar Ahmad, ya sanya wa hannu, inda ya ce an \u0257auki matakin ne domin inganta tsaftar muhalli, sarrafa shara, yanayin magudanan ruwa da kuma tabbatar da bin \u0199a\u2019idojin tsaftar muhalli da aka gindaya.<\/p>\n<p>Sanarwar ta ce an kuma \u0257ora wa tawagar alhakin sa ido kan ayyukan ma\u2019aikatan REMASAB, domin tabbatar da cewa suna gudanar da ayyukan da aka \u0257ora musu cikin inganci da \u0199warewa, ciki har da amfani da kayan kariya na musamman.<\/p>\n<p>A wani \u0253angare na ayyukan da take gudanarwa a wurare daban-daban, tawagar sa ido ta ziyarci <strong><span style=\"font-weight: normal\">Gadar Dangi<\/span><\/strong><b>,<\/b> inda ta duba yanayin tsaftar muhalli a yankin tare da nazarin ayyukan tsaftar da ake gudanarwa.<\/p>\n<p>Hukumar ta ce binciken da aka gudanar ya gano cewa wasu maza, mata da yara sun mayar da yankin \u0199ar\u0199ashin gadar da kuma kewayenta a matsayin wurin zama na wucin gadi.<\/p>\n<p>REMASAB ta kuma ce an gano wasu sassan gadar da ake amfani da su wajen yin bayan gida a fili.<\/p>\n<p>Hukumar ta bayyana cewa wannan yanayi na haifar da damuwa game da lafiyar jama\u2019a, tsaftar muhalli da kuma tsaro, musamman ganin cewa wurin yana kusa da muhimman ababen more rayuwa na jama\u2019a.<\/p>\n<p>Ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su \u0257auki matakin da ya dace cikin ha\u0257in gwiwa domin magance matsalar cikin mutunta mutanen da abin ya shafa da tsari da kuma hanyar da za ta dore.<\/p>\n<p>Hukumar ta kuma jaddada bu\u0199atar kare wuraren jama\u2019a da muhimman ababen more rayuwa daga ayyukan da ka iya yin illa ga lafiyar muhalli da tsaron jama\u2019a.<\/p>\n<p>Binciken na daga cikin \u0199o\u0199arin da Manajan Daraktan REMASAB, Dakta Muhammad S. Khalil, ke yi na \u0199arfafa sa ido kan ayyukan hukumar da inganta ayyukan sarrafa shara da kuma \u0257aga matsayin tsaftar muhalli a fa\u0257in Jihar Kano.<\/p>\n<p>Hukumar ta bu\u0199aci mazauna jihar da al\u2019ummomi da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafa wa \u0199o\u0199arin tsaftar muhalli, ta hanyar tsaftace muhallinsu da amfani da wuraren da aka ware domin zubar da shara da kuma guje wa duk wasu ayyuka da ka iya haifar da lalacewar muhalli.<\/p>\n<p><strong>Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Khadijah Aliyu, Kano Hukumar Kula da Shara da Tsaftar Muhalli ta Jihar Kano, REMASAB, ta \u0199ara tsaurara sa ido kan tsaftar muhalli a fa\u0257in jihar, inda ta tura wata tawaga ta musamman domin duba manyan da \u0199ananan hanyoyi da kuma wasu muhimman wurare. Hakan na \u0199unshe ne cikin wata sanarwa da Jami\u2019in Hul\u0257a da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10031,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[39],"class_list":["post-10030","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kano"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/6675019b-bd4d-4112-9e91-fae21c23b2bf.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10030","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10030"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10030\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10032,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10030\/revisions\/10032"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10031"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10030"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10030"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10030"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}