{"id":10027,"date":"2026-09-29T10:52:09","date_gmt":"2026-09-29T10:52:09","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10027"},"modified":"2026-09-29T10:52:09","modified_gmt":"2026-09-29T10:52:09","slug":"an-yi-kiran-karfafa-hadin-gwiwa-don-magance-cutar-haukan-kare-a-zamfara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-yi-kiran-karfafa-hadin-gwiwa-don-magance-cutar-haukan-kare-a-zamfara\/","title":{"rendered":"An Yi Kiran Karfafa Hadin Gwiwa Don Magance Cutar Haukan Kare A Zamfara"},"content":{"rendered":"<h3>Daga Aminu Dalhatu, Gusau<\/h3>\n<p>Hukumar Bun\u0199asa Kiwo ta Jihar Zamfara ta yi kira da a \u0199ara \u0199arfafa ha\u0257in gwiwa da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki domin ya\u0199i da cutar hauka tare da hana mace-macen da cutar ke haddasawa.<\/p>\n<p>Babban Daraktan Hukumar, Dakta Isma\u2019ila Usman Gusau, ya yi kiran ne a lokacin bikin Ranar Cutar hauka ta Duniya ta shekarar 2026 a Gusau, wanda ya \u0199unshi jerin gwanon wayar da kai da kuma \u0199addamar da shirin rigakafin cutar kyauta a Fadar Mai Martaba Sarkin Gusau.<\/p>\n<p>\u0198ungiyar Likitocin Dabbobi ta Najeriya, NVMA, reshen Jihar Zamfara ce ta shirya gangamin wayar da kan jama\u2019a, wanda ya ha\u0257a \u0199wararrun likitocin dabbobi, jami\u2019an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin \u0199ara wayar da kan jama\u2019a da kuma inganta ha\u0257in gwiwar ya\u0199i da cutar.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen taron, Babban Daraktan Hukumar Bun\u0199asa Kiwo ta Jihar Zamfara, Dakta Isma\u2019ila Usman Gusau, ya ce an shirya gangamin ne domin neman goyon bayan Masarautar Gusau da sauran hukumomin gargajiya wajen ya\u0199i da cutar.<\/p>\n<p>Dakta Gusau ya bayyana cewa sarakunan gargajiya na da muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al\u2019umma da kuma \u0199arfafa masu kiwon dabbobi su ri\u0199a kula da dabbobinsu yadda ya kamata tare da tabbatar da yi musu rigakafi akai-akai.<\/p>\n<p>Shi ma da yake jawabi, Mai Kula da Shirin L-PRESS na Jihar Zamfara, Nasiru Mohammed, ya yi al\u0199awarin cewa shirin zai ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen bun\u0199asa kiwo da kula da lafiyar dabbobi a jihar.<\/p>\n<p>Nasiru Mohammed ya ce lafiyar dabbobi na daga cikin muhimman abubuwan da shirin L-PRESS ya mayar da hankali a kai, musamman a \u0199ar\u0199ashin \u0253angare na \u0257aya, \u0199aramin \u0253angare na 1.3, wanda ya mayar da hankali kan \u0199arfafa ayyukan kula da lafiyar dabbobi.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Daraktan Ayyukan Kula da Lafiyar Dabbobi na Jihar Zamfara, Dakta Aminu Abdulrazak, ya bayyana cutar hauka a matsayin wata mummunar cuta da ke iya ya\u0257uwa daga dabbobi zuwa mutane, yana mai jaddada cewa rigakafi na da matu\u0199ar muhimmanci wajen kare mutane daga cutar.<\/p>\n<p>Dakta Abdulrazak ya bayyana cewa karnukan da suka kamu da cutar hauka na iya sauya halayensu, kamar rashin natsuwa da tashin hankali da yawan fitar yawu da cizon mutane ba tare da dalili ba da kuma tsoron ruwa.<\/p>\n<p>Daraktan ya shawarci jama\u2019a da su guji kusantar dabbobin da ake zargin sun kamu da cutar, tare da gaggauta neman kulawar likita idan dabba ta cije su ko kuma suka yi mu\u2019amala da dabbar da ake zargin tana \u0257auke da cutar.<\/p>\n<p>Tun da farko, Mai Martaba Sarkin Gusau, Dakta Abdulkadir Ibrahim Bello, ya tabbatar da cewa zai tattauna da sauran sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki kan bu\u0199atar ha\u0257a \u0199arfi wajen ilmantar da jama\u2019a da wayar da kansu game da illolin cutar hauka.<\/p>\n<p>Dakta Bello ya ce tun da cutar hauka cuta ce mai kisa wadda za ta iya haddasa asarar rayuka, ya zama wajibi sarakunan gargajiya su yi aiki kafada da kafada da hukumomin da abin ya shafa domin taimakawa wajen dakile cutar da kuma kawo \u0199arshenta.<\/p>\n<p>Jerin gwanon wayar da kan jama\u2019ar ya fara ne daga Hukumar Bun\u0199asa Kiwo ta Jihar Zamfara, inda ya \u0199are a Fadar Mai Martaba Sarkin Gusau, Dakta Abdulkadir Ibrahim Bello, inda aka \u0199addamar da shirin rigakafin cutar haukan kare kyauta a hukumance.<\/p>\n<p><strong>Fasara; Shafii Abubakar Wababe<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Bun\u0199asa Kiwo ta Jihar Zamfara ta yi kira da a \u0199ara \u0199arfafa ha\u0257in gwiwa da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki domin ya\u0199i da cutar hauka tare da hana mace-macen da cutar ke haddasawa. Babban Daraktan Hukumar, Dakta Isma\u2019ila Usman Gusau, ya yi kiran ne a lokacin bikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10028,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[719],"class_list":["post-10027","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-gusau"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/33054edf-55f9-43ce-be2d-ddae7743a39d.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10027","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10027"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10027\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10029,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10027\/revisions\/10029"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10028"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10027"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10027"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10027"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}