{"id":10019,"date":"2026-09-28T16:26:57","date_gmt":"2026-09-28T16:26:57","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=10019"},"modified":"2026-09-28T16:26:57","modified_gmt":"2026-09-28T16:26:57","slug":"zamu-horas-da-manoma-kan-amfani-da-sinadaran-noma-nwdc","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/zamu-horas-da-manoma-kan-amfani-da-sinadaran-noma-nwdc\/","title":{"rendered":"Zamu Horas Da Manoma Kan Amfani Da Sinadaran Noma -NWDC"},"content":{"rendered":"<p>Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya na nazarin yiwuwar ha\u0257in gwiwa da Wani kamfani, Global Chemical Security and Safety Consultancy domin horar da manoma kan yadda za su yi amfani da sinadaran noma cikin aminci, tare da inganta samar da abinci a yankin.<\/p>\n<p>Manajan Daraktan Hukumar, Farfesa Shehu Abdullahi Ma\u2019aji, ne ya bayyana haka yayin da ya kar\u0253i tawagar shugabannin kamfanin, \u0199ar\u0199ashin jagorancin wanda ya kafa shi kuma Babban Jami\u2019in Gudanarwarsa, Dakta Mustapha Tijani Usman, a ziyarar ban-girma da suka kai masa.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-10020\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/IMG-20260928-WA0021-1-800x430-1-300x161.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"161\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/IMG-20260928-WA0021-1-800x430-1-300x161.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/IMG-20260928-WA0021-1-800x430-1-768x413.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/IMG-20260928-WA0021-1-800x430-1.jpg 800w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da Daraktan Ya\u0257a Labarai da Hul\u0257a da Jama\u2019a na Hukumar, Abdulrashid Yusuf Safana, ya fitar, tawagar ta gabatar da wani tsari na horar da manoma a aikace kan amfani da sinadaran noma cikin aminci domin samun ingantaccen amfanin gona a jihohin Arewa maso Yamma guda bakwai.<\/p>\n<p>Dakta Usman ya ce kamfanin na Bada matakan Kariya da bada shawarwari tare da ingantaccen tsari ga manoma don \u0257orewar amfani da sinadarai ta hanyar bayar da horo na \u0199warewa da gudanar da bincike da nazari da sa ido da tantance yadda ake amfani da sinadaran.<\/p>\n<ul>\n<li><\/li>\n<\/ul>\n<p>Ya ce ha\u0257in gwiwar da ake shirin yi zata \u0199arfafa manoma wajen amfani da sinadaran noma yadda ya kamata, tare da bun\u0199asa harkar noma, wadda ke da matu\u0199ar muhimmanci wajen samar da wadataccen abinci da tabbatar da zaman lafiya a yankin.<\/p>\n<p>Yayin gabatar da shirin, Daraktan Kula da Sinadarai da amfaninsu Cikin aminci, Mista Buba Shanu, ya ce shirin zai sake horas da manoma kan yadda ya kamata su yi amfani da magungunan kashe ciyawa dana kashe \u0199wari da takin zamani da sauran sinadaran noma.<\/p>\n<p>Mista Shanu ya bayyana raguwar ingancin \u0199asa da matsin lamba kan filayen noma da kuma rashin amfani da kayan aikin noma yadda ya kamata a matsayin manyan matsalolin da ke barazana ga manoma da muhalli.<\/p>\n<p>Ya ce manoma da dama ba su da isasshen ilimi kan adadin sinadaran da ya kamata su yi amfani da su da yadda ake sarrafawa da adanawa da lokacin da ya kamata a dakatar da amfani da sinadari kafin girbi, da kuma matakan kare lafiyar mutume.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa \u0199warewar kamfanin a fannin takin zamani, ciki har da aiki a tsohon Kamfanin Takin Zamani na \u0198asa (NAFCON), ce ta \u0199arfafa fafutukarta wajen wayar da kan jama\u2019a game da amfani da sinadaran noma cikin aminci.<\/p>\n<p>A cewarsa, horon zai taimaka wajen \u0199ara yawan amfanin gona da rage ha\u0257arin da ke tattare da lafiya da kare muhalli da kuma dakile amfani da sinadaran noma ba bisa \u0199a\u2019ida ba, wanda ka iya haifar da matsalolin tsaro.<\/p>\n<p>Ana sa ran shirin zai yi amfani da tsarin horo na aikace-aikace kai tsaye a gonaki, domin isa ga manoman karkara a sassan jihohin Arewa maso Yamma.<\/p>\n<p>Da yake mayar da jawabi, Farfesa Ma\u2019aji ya ce shirin ya yi daidai da manufofin Hukumar na bun\u0199asa noma da tabbatar da wadatar abinci da ha\u0253aka da kuma \u0199arfafa al\u2019umma.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa rashin tsaro da \u0199arancin yawan amfanin gona da kuma zaman kashe wando ko rashin aikin yi tsakanin matasa matsaloli ne da ke da ala\u0199a da juna, yana mai cewa shirye-shiryen da za su inganta aikin noma cikin aminci da \u0257orewa za su iya taimakawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.<\/p>\n<p>Farfesa Ma\u2019aji ya tabbatar wa tawagar cewa Hukumar za ta duba shirin tare da samar da tsarin da zai ba da damar gudanar da ha\u0257in gwiwa idan hakan ya samu kar\u0253uwa.<\/p>\n<p>Ya ce NWDC za ta ba da fifiko ga ha\u0257in gwiwar da ke samar da sakamako mai amfani da inganta tsaro da kuma samar da ayyukan yi ga matasa da mata a aikin gona.<\/p>\n<p>Gyarawa Yusuf Zubairu. Fassara: Shafii Abubakar Wababe<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya na nazarin yiwuwar ha\u0257in gwiwa da Wani kamfani, Global Chemical Security and Safety Consultancy domin horar da manoma kan yadda za su yi amfani da sinadaran noma cikin aminci, tare da inganta samar da abinci a yankin. Manajan Daraktan Hukumar, Farfesa Shehu Abdullahi Ma\u2019aji, ne ya bayyana haka [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":10021,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2132],"class_list":["post-10019","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-nwdc"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/09\/IMG-20260928-WA0024-768x578-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10019","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=10019"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10019\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":10022,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/10019\/revisions\/10022"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/10021"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=10019"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=10019"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=10019"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}