Ilimi
UNICEF Ta Ƙara Faɗaɗa Ayyukanta Domin Inganta Rayuwar Yara a Najeriya
Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, ta ƙara faɗaɗa ayyukanta a faɗin Najeriya domin inganta rayuwar yara, musamman waɗanda ke cikin mawuyacin hali da yankunan da rikice-rikice suka shafa.
Hakan na kunshe ne a wani rahoto da hukumar ta fitar kan ayyukan da ta ke gudanarwa, inda ta jaddada aniyarta ta ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen ƙarfafa muhimman bangarori.
A ɓangaren kiwon lafiya, UNICEF na faɗaɗa shirye-shiryen allurar rigakafi kan cututtuka kamar shan-inna da kyanda, tare da ƙarfafa ayyukan kula da lafiya a matakin farko da kuma inganta hanyoyin adana allurai.
Haka kuma, hukumar na tallafa wa ‘yan gudun hijira da sauran al’ummomi marasa galihu domin tabbatar da samun kulawar lafiya.
A ɓangaren ruwa, tsaftar jiki da ta muhalli, UNICEF na ƙara samar da ruwan sha mai tsafta ta hanyar gyara da gina rijiyoyi da sauran hanyoyin samar da ruwa ga al’umma, makarantu da cibiyoyin lafiya.
Haka zalika, ana ƙara wayar da kai kan muhimmancin wanke hannu da kuma kawar da yin bayan gida a fili, musamman a yankunan da cutar kwalara ke yawaita.
A ɓangaren ilimi kuwa, UNICEF na aiki tare da hukumomin da suka dace domin inganta samun ilimi mai inganci, tare da mai da hankali kan yara da ba sa zuwa makaranta, ‘yan mata da kuma waɗanda rikice-rikice suka shafa.
Shirye-shiryen sun haɗa da horar da malamai, samar da kayan koyo da kuma samar da hanyoyin koyo masu sassauci.
Game da abinci mai gina jiki, hukumar na ƙara faɗaɗa shirye-shiryen magance matsanancin ƙarancin abinci ga yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar, tare da ƙarfafa shayar da jarirai nonon uwa kaɗai da kuma inganta tsarin ciyar da yara.
UNICEF na kuma ƙarfafa tsarin kare haƙƙin yara domin magance matsalolin cin zarafi da cutarwa, ciki har da auren yara ƙanana, tare da faɗaɗa rajistar haihuwa.
Haka kuma ta yi kira da a ci gaba da haɗin gwiwa da saka jari domin tabbatar da kyakkyawar makoma ga yara a Najeriya.
-
Ilimi6 days agoGwamna Namadi Ya Dauki Malaman Makaranta 2,020 Aiki
-
Labarai3 days agoƊan Takarar Gwamnan Accord A Kebbi Ya Yi Alƙawarin Ƙara Albashin Ma’aikata Zuwa N500,000
-
Labarai3 days agoGwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Gina Hanyar Kilomita 95 A Tsafe Don Ƙarfafa Ayyukan Tsaro
-
Labarai3 days agoGwamna Kefas Ya Zargi Jami’an Gwamnatinsa Da Taimaka Wa Haƙar Ba Bisa Ka’ida Ba
-
Labarai1 day agoGwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Cibiyar Ayyukan Noma Da Samar Sa Kayayyakin Zamani
-
Labarai3 days agoUNILORIN Ta Zama Ta Farko A Najeriya Wajen Ingancin Bincike
-
Labarai1 day agoGwamnatin Jigawa Za Ta Biya Diyar Naira Miliyan 982 Ga Wadanda Aikin Hanya Ya Shafa
-
Labarai1 day agoGwamnatin Jigawa Ta Amince Da Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Miliyoyin Naira
