Connect with us

Ilimi

UNICEF da Abokan Hulɗa Sun Kaddamar da Shirin Wayar da Kai Kan Rijistar Haihuwa a Yankin Gwarzo

Published

on

A wani sabon yunƙuri na inganta haƙƙin yara da walwalarsu, Hukumar kula da kananan yara ta MDD wato UNICEF tare da haɗin gwiwar Hukumar Wayarda kan jama’a da ta Ƙasa (NOA) da Hukumar kidayar Jama’a ta kasa (NPC), da Hukumar Kula da katin zama dan Ƙasa (NIMC), sun kaddamar da shirin wayar da kai na yini guda kan muhimmancin rijistar haihuwa ga sabbin jarirai a duk faɗin Yankin Gwarzo na Jihar Kano.

Wannan wani ɓangare ne na shirye-shiryen gwamnati da UNICEF ke tallafawa, domin ƙarfafa tsarin kare yara da kuma tabbatar da samun damar yin amfani da muhimman aikace-aikacen zamantakewa, musamman a yankunan karkara na jihar.

Wakilin NPC, Malam Abubakar Lawal, ya jaddada muhimmancin haddin kan al’umma wajen cimma nasarar cikakkiyar rijistar haihuwa. Ya yi kira ga sarakunan gargajiya, malamai da shugabannin al’umma da su jagoranci wayar da kan jama’a don tabbatar da cewa babu yaro ko ɗaya da bai samu rajista ba.

A nasa jawabin, Mai ba da shawara kan harkokin lafiya (SBC Health Consultant), Alhaji Usman Yahaya, ya bayyana rijistar haihuwa a matsayin matakin farko na shari’a da ke tabbatar da wanzuwar yaro, yana mai cewa wannan ne kofar shiga ga duk wasu haƙƙoƙin yara irin su lafiya, ilimi da kariya.

Ya nuna damuwa cewa har yanzu yara da dama a yankunan karkara ba su da takardar shaidar haihuwa ta hukuma, lamarin da ke iya hana su shiga cikin shirin gwamnati da tsare-tsaren ci gaban jama’a.

Masu halarta sun gudanar da tattaunawa, inda aka yi tambayoyi da tattaunawa da aikin ƙungiya domin samar da dabarun aiki a matakin ƙasa da za su taimaka wajen faɗaɗa rijistar haihuwa a duk faɗin Yankin Gwarzo.

Khadijah Aliyu/Kano

 

Labarai

Labarai2 hours ago

NHIA Ta Fara Daukar Jami’an Kula da Lafiya na Ƙasa a Jigawa

Usman Muhammad Zaria  Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) ta fara aikin daukar Jami’an Kula da Lafiya na...

Labarai7 days ago

Baragurbi a Aikin Jarida na Barazana ga Sahihancin Kafafen Yada Labarai – Shugaban NUJ-FRCN

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen FRCN Kaduna, Kwamared Umar Adamu Sarkinfada, ya bayyana cewa mummunan aikin jarida...

Labarai2 weeks ago

Ƙaruwa a Shan Abubuwan Sha Masu Ƙara Ƙarfi na Haddasa Damuwar Lafiya a Kano

Abubuwan sha masu ƙara ƙarfi, waɗanda aka fi sani da energy drinks ko energizers, na ƙara samun karɓuwa a faɗin...

Labarai2 weeks ago

Shugaba Tinubu Ya Taya CPSO Usman Shugaba Murnar Cika Shekara 45 da Haihuwa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Kwamishinan ‘Yan Sanda, Usman Musa Shugaba, wanda shi ne Babban Jami’in Tsaron ‘Yan...

Labarai2 weeks ago

TSARO: Gwamnan Jihar Neja Ya Nuna Alhini Kan Harin ‘Yan Ta’adda a Al’ummomin Borgu

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa kan harin ‘yan ta’adda da aka kai wa wasu...

Labarai2 weeks ago

Allah Ya Jikan Jarman Kauru Da Ke Jihar Kaduna

Mun sami labarin rasuwar tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, Malam Suleiman Lawal Jarman Kauru. Malam Suleiman Lawal, mai shekaru...

Labarai2 weeks ago

Gwamnatin Kano Ta Faɗaɗa Damar Tattalin Arziki ga Mata da Masu Buƙata Ta Musamman

An kammala kasuwar baje kolin mata ta tsawon kwanaki huɗu, wadda Ma’aikatar Harkokin Mata, Yara da Masu Buƙata Ta Musamman...

Labarai2 weeks ago

Rundunar Tsaro Ta Haɗin Gwiwa Ta Hallaka ’Yan Bindiga 150

Rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ta ƙunshi Sojojin Nijeriya, Hukumar Tsaron Farin Ciki (DSS), ’Yan Sanda da sauran hukumomin...

Ilimi2 weeks ago

Gwamnatin Neja Ta Amince da Sake Buɗe Makarantun Gwamnati da Masu Zaman Kansu daga 12 ga Janairu

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya amince da sake buɗe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a faɗin...

Ilimi2 weeks ago

Gwamnatin Nasarawa Ta Roki Malaman Jami’o’i Masu Yajin Aiki Su Koma Aji – SSA Ahemba

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi kira ga malaman manyan makarantu mallakar jihar da ke yajin aiki da su janye yajin...

Mafi Shahara