Labarai
NAPTIP ta Kama ‘Yan Safarar Mutane a Abuja, ta Kuɓutar da Mutane 24
Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane ta Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama aƙalla mutum biyar da ake zargi da safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jiragen saman ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe International Airport, da ke Abuja.
Jami’in watsa labaran hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ya bayyan a ranar Laraba cewa a cikin waɗanda aka kama akwai wani mutum da ya yi yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi.
Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello.
Adekoye ya ce aikin, wanda aka yi bisa bayanan sirri da aka samu, ya samu jagorancin babbar daraktar hukumar, Binta Adamu Bello.
Ya bayyana cewa a cikin waɗanda ake zargin akwai wani babban jami’in tsaro, wanda ke cikin masu safarar mutane a kudu maso yammacin Nijeriya.
Adekoye ya ce waɗanda aka kuɓutar ɗin yara ne da matasa waɗanda shekarunsu ke tsakanin shekara 15 zuwa 26 waɗanda aka ɗauko daga jihohin Kano da Katsina da Oyo da Ondo da kuma Ribas, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa ƙasashen Iraƙi da Sudan da Masar da Saudiyya da Bahrain da kuma Afghanistan.
Ɗaya daga cikinsu ta sha alwashin cewa sai ta tabbatar an gurfanar da mahafinta a gaban kotu kan yunƙarin safararta da ya yi zuwa iraƙi, in ji jami’in.
Ya ƙara da cewa wata cikin waɗanda aka yi ƙoƙarin safarar ta ce mahafiyarta ce ta rinjaye ta ta yarda da cewa za ta tafi Turai domin yin aiki ta samu daloli.
-
Labarai7 days agoGwamnan Kano Ya Mika Sunayen Sabbin Kwamishinoni 2 Ga Majalisa Domin Tantancewa
-
Labarai7 days agoGwamnatin Neja Ta Jaddada Ƙudurinta Na Farfaɗo Da Kamfanin Buga Takardun Gwamnati
-
Labarai7 days agoAn Ceto Wani Mutum da Ya Fada Kududdufi a Kano
-
Labarai7 days agoTsangayar Kimiyyar Kula Da Lafiya Ta BUK Ta Lashe Zinare A Gasar Kwallon Ƙafa Ta Tsangayu Karo Na 19
-
Labarai5 days agoJigawa: Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Kafa Kwamitin Tantance Bayanan Maniyyatan 2027
-
Labarai7 days agoDan Takarar Gwamnan Sokoto Na ADC Ya Tsalleke Rijiya da Baya Daga Yunkurin Hallaka Shi
-
Labarai7 days agoShugaban Majalisar Wakilai Ya Jaddada Muhimmancin Samar Da Ilimi, Lafiya Da Tsaro Ga Al’umma
-
Labarai7 days agoDurumbun Gusau Ya Bukaci Haɗin Gwiwa Wajen Magance Matsalar Tsaro
