Connect with us

Labarai

Kano ta ƙaddamar da kwamitin OGP domin ƙarfafa gaskiya da riƙon amana

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da kwamitin jagoranci na Open Government Partnership (OGP) domin ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da kuma inganta shugabanci mai haɗa kowa da kowa.

An ƙaddamar da kwamitin ne a ma’aikatar kula da saye da kwangiloli da bibiyar ayyuka, tare da halartar wakilai daga gwamnati, ƙungiyoyin farar hula da kuma kafafen yaɗa labarai.

Babban sakataren ma’aikatar, Injiniya Garba Adamu, ya yabawa gwamnan jihar bisa goyon bayan da ya bayar wajen kafa kwamitin, yana mai cewa OGP wata hanya ce da ke haɗa gwamnati da ƙungiyoyin farar hula domin inganta gaskiya da riƙon amana.

Kwamishinan ma’aikatar kuma mataimakin shugaban OGP na gwamnati, Nura Ma’aji, ya bayyana cewa wannan tsari na duniya ne da ke ƙarfafa shiga ta jama’a da haɗin kai a harkokin mulki.

Ya ƙara da cewa kwamitin ya ƙunshi mambobi 16, rabinsu daga gwamnati da rabinsu daga ƙungiyoyin farar hula, domin tabbatar da wakilci da haɗin kai.

A nasa jawabin, shugaban OGP daga ɓangaren ƙungiyoyin farar hula, Abdulrazak Alkali, ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin Kano wajen aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi yaƙi da cin hanci, samun bayanai, shari’a da kuma sauyin yanayi.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa tana da tsarin aiki na shekarun 2024 zuwa 2026, tare da buƙatar ƙara ƙaimi wajen aiwatar da shi domin inganta ayyukan gwamnati da hidima ga jama’a.

Khadijah Aliyu/Kano

Labarai

Ilimi2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yaba wa Ministar Harkokin Mata Kan Inganta Rayuwar Al’umma

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa Ministar Harkokin Mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, bisa...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Wasu Sabbin Ka’idoji Kan Digirin Girmamawa

Daga Bello Wakili Gwamnatin Tarayya ta amince da wani sabon tsari game da bayar da digirin girmamawa (honorary degrees) a...

Labarai2 days ago

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Nadin Sabbin Ministoci Biyu

Daga Bashir Meyere  Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin ministoci biyu da Shugaban Ƙasa ya miƙa sunayensu domin tantance su...

Labarai2 days ago

Rukuni na Farko na Alhazan Jihar Kwara Ya Isa Kasar Saudiyya

Daga Ali Muhammad Rabi’u Rukuni na farko na Alhazan Jihar Kwara su 374 ya sauka ƙasar Saudiyya domin gudanar da...

Labarai2 days ago

Jihar Jigawa Ta Kammala Jigilar Alhazai Zuwa Kasa Mai Tsarki

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce rukuni na biyu kuma na ƙarshe na...

Labarai2 days ago

Gwamna Bago Ya Umurci SEMA Ta Gaggawata Kai Tallafi ga Wadanda Iftila’in Guguwa ya Shafa a Mokwa da Bida

Daga Aliyu Lawal Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya jajanta wa al’ummar yankunan ƙananan hukumomin Bida da Mokwa kan...

Kasuwanci2 days ago

BOA da Majalisar Wakilai za su Samar da Injinan Noma a Dukkan Mazabu

Daga Salihu Tsibiri Bankin Manoma na Kasa (BOA) zai hada gwiwa da Majalisar Wakilai ta Tarayya domin bunkasa amfani da...

Labarai2 days ago

Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ta Mayar da Rarar Kudade ga Alhazai

Daga Abdullahi Jalaluddeen Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta kammala biyan rarar kuɗaɗe ga maniyyata aikin Hajjin 2026....

Ilimi2 days ago

UNICEF Ta Ƙara Faɗaɗa Ayyukanta Domin Inganta Rayuwar Yara a Najeriya

Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, ta ƙara faɗaɗa ayyukanta a faɗin Najeriya domin inganta...

Labarai4 days ago

Gwamnan Jigawa Ya Bukaci Alhazai Su Yi Addu’ar Zaman Lafiya da Ci Gaban Najeriya

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya buƙaci Alhazan jihar da su kasance jakadu nagari yayin zamansu a ƙasa mai tsarki....

Mafi Shahara