Labarai
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano Ja Jajanta Wa Waɗanda Gobarar Kasuwar Singa Ta Shafa
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore, ya miƙa ta’aziyyarsa ga Gwamnatin Jihar Kano, ’yan kasuwa da mazauna birnin Kano da gobarar da ta auku a shahararriyar Kasuwar Singa ta shafa a birnin Kano.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kamaluddeen Sani Shawai, ya sanya wa hannu, Kakakin ya bayyana lamarin a matsayin abin tausayi da takaici, yana mai cewa gobarar ta lalata shaguna da kayayyaki da darajarsu ta kai biliyoyin naira.
Falgore ya nuna matuƙar alhini kan asarar da ’yan kasuwa da iyalansu suka yi, tare da jaddada cewa Majalisar Dokokin Jihar Kano na tare da su cikin wannan mawuyacin lokaci.
Ya ce: “Cikin baƙin ciki mai zurfi da kuma jin nauyin asara, a madadin Majalisar Dokokin Jihar Kano, muna miƙa ta’aziyyarmu ga waɗanda lamarin ya shafa, iyalansu da dukkan sauran da gobarar ta shafa.”
Ya kuma bukaci mambobin al’ummar ’yan kasuwa da jama’a gaba ɗaya da su kwantar da hankalinsu tare da ba da cikakken haɗin kai ga jami’an agajin gaggawa da ke aiki don shawo kan illolin gobarar.
Kakakin ya yaba wa jami’an kashe gobara da hukumomin tsaro bisa saurin daukar mataki wajen kashe wutar, yana mai cewa gaggawar shigarsu cikin lamarin ta taimaka matuƙa wajen takaita barnar.
Sai dai Falgore ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta samar da kayan kashe gobara na zamani tare da ƙarfafa tsarin ba da agajin gaggawa, domin hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba da kuma shawo kansa yadda ya kamata idan ya auku.
Ya ƙara da cewa: “A madadin Majalisar Dokokin Jihar Kano, muna yi wa dukkan waɗanda wannan mummunan lamari ya shafa addu’ar juriyar zuciya, samun taimako da ƙarfi.”
Gobarar Kasuwar Singa ita ce ta baya-bayan nan cikin jerin gobarar kasuwanni da ke faruwa a Kano, lamarin da ke ƙara tayar da hankula game da matakan kare gobara da shirye-shiryen gaggawa a manyan cibiyoyin kasuwanci a faɗin jihar.
Khadijah Aliyu
-
Labarai6 days agoRamadan: Sarkin Kauru Ya Bukaci a Kara Karfafa Tsaro Tare da Tallafawa Marasa Galihu
-
Labarai5 days agoKaramar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
-
Labarai5 days agoSojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam
-
Labarai2 days agoRanar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata
-
Labarai5 days agoTsarin Kundin Shirin Bunkasa Samarda Abinci Mai Gina Jiki
-
Labarai6 days agoKungiyoyin Alumma a Jigawa Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Gwamna Namadi Kan Lamarin Walida Abdulhadi
-
Labarai4 days agoGwamnatin Zamfara Ta Ayana Dokar Ta-baci Kan Shan-Inna a Karamar Hukumar Gummi
