Labarai
Jam’iyyar APC Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni a Jihar Kano
Daga Abdullahi Jalaluddeen
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Kano ta zaɓi sabbin shugabanni domin jagorantar harkokin jam’iyyar.
Zaɓen, wanda aka gudanar a ranar Talata, ya fitar da Umar Haruna Doguwa a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar na Jiha.
Doguwa ya ajiye muƙaminsa na Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Kano domin tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar.
Salisu Maje Ahmad Gwangwazo ya zama Mataimakin Shugaban Jiha, yayin da Farfesa Yusuf Muhammad Sabo Bichi aka zaɓe shi a matsayin Sakataren jam’iyyar na jiha.
Haka kuma, an zaɓi Abdul Adamu Fagge a matsayin Mai Ba da Shawara kan Harkokin Shari’a, tare da Bashir Yusuf Tudun Wuzirci a matsayin Mataimakin Mai Ba da Shawara kan Shari’a.
Kabiru Sule Rogo ya samu muƙamin Ma’aji, yayin da Umar Yusuf Umar ya zama Mataimakin Ma’aaji. An kuma zabi Ma’aruf Abdullahi Garo a matsayin Sakataren Kuɗi, sai kuma Mustafa Muhammad Kalwa a matsayin Mataimakin Sakataren Kuɗi.
Hakazalika, Dakta Kabiru Hussaini Zawaciki ya zama Sakataren Tsare-tsare, tare da Abdussalam Umar a matsayin mataimakinsa.
Auwalu Abdullahi ya zama Sakataren Yaɗa Labarai, wanda Sani Fata zai taimaka masa a matsayin mataimaki.
Yayin da Bashir Mai Sango ya zama Sakataren Jin Daɗin Mambobi, tare da Garba Hussaini a matsayin mataimaki. Abubakar Salisu zai riƙe muƙamin Mai Binciken Kuɗi, yayin da Nura Muhammad ya zama Mataimakin Mai Binciken Kuɗi.
-
Ilimi6 days agoGwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Inganta Hanyoyi, Ruwa da Wutar Lantarki a Jami’ar FUD
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Amince Da Shirin Gaggawa Na Kwana 120 Domin Farfaɗo Da Ilimi
-
Labarai6 days agoTinubu: Sabbin Dokokin Haraji Za Su Kawo Wadata Yayinda Tsofaffi Suka Talauta ‘Yan Najeriya
-
Labarai7 days agoHezbollah Da Isra’ila Za Su Yi Ganawar Gaba Da Gaba A Karon Farko
-
Labarai3 days agoƘungiyar Ci gaban Al’ummar Saminaka Ta Bai Wa ‘Yan Sanda Injin Hilux Don Ƙarfafa Tsaro
-
Labarai6 days agoAn Yi wa Yara Sama da 66,000 Rigakafin Cutar Shan Inna a Tarauni
-
Kasuwanci6 days agoMajalisar Neja ta Amince da Dokar Hana Ayyukan Baban Bola a Unguwanni
-
Labarai6 days agoHarin Shanga: Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafawa Iyalan Jama’an Tsaro da Aka Kashe
