Connect with us

Ilimi

An Sace Ɗalibai 1,683 a Makarantu cikin Shekaru 8 – Rahoto

Published

on

Aƙalla yara da ɗalibai 1,683 ne aka sace a makarantu a Najeriya tsakanin shekarun 2014 zuwa 2022, sakamakon hare-haren da ƙungiyoyin ’yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya suka kai makarantu har sau 70 a cikin wannan lokaci.

Wani rahoto da ƙungiyar agaji ta ƙasa da ƙasa, Save the Children International (SCI), ta fitar domin bikin Ranar Ilimi ta Duniya ta 2026, ya kuma bayyana cewa ɗalibai 184 sun rasa rayukansu a yayin waɗannan hare-hare, yayin da gine-ginen makarantu 25 suka lalace.

Rahoton, wanda aka miƙa wa ’yan jarida a Jihar Katsina, ya nuna cewa rikicin ya fi muni a jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, inda hare-haren makarantu, sace-sacen jama’a gaba ɗaya, da ƙauracewar al’umma ke ci gaba da yawaita. Wannan na hana ƙoƙarin gwamnati da abokan hulɗa na inganta ingancin ilimi samun nasara.

Rahoton ya gargaɗi cewa, “ba tare da tabbatar da tsaron makarantu da kuma samar da isasshen kuɗaɗen da za a zuba a ɓangaren ilimi ba, ƙwarewa da baiwar matasan Najeriyawaɗanda suka haura kashi 60 cikin 100 na yawan alummaza su ci gaba da kasancewa a takure.”

Haka kuma, rahoton ya yi kira da a aiwatar da Dokar Kare Tsaron gaba ɗaya, tare da ɗaukar tsauraran matakan tsaro don kare yara a wuraren koyonsu. Ya bayyana matasa a matsayin “ba shugabannin gobe kaɗai ba, har ma manyan ginshiƙan sauyi a yau.

Rahoton ya ƙara da cewa ƙungiyar na ci gaba da jajircewa wajen ƙarfafa fafutukar matasa domin ganin an aiwatar da Shirin Kare Makarantu, tallafawa ilimi a lokutan gaggawa, da bunƙasa basira da ƙwarewar matasa da rikice-rikice da ƙauracewa suka shafa.

Isma’il Adamu

Labarai

Labarai18 hours ago

NEMA Da Masu Ruwa Da Tsaki Sun Kara Haɗa Gwiwa Don Hana Aukuwar Ambaliya Da Hadarin Tankar Mai

  By Adamu Yusuf   Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), tare da haɗin gwiwar masu ruwa da...

Labarai2 days ago

Kaduna Ta Kaddamarda Shirin Rabon Maganin Kariya Daga Cutar Dundumi

  Daga Khadija Kubau   Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna tareda haɗin gwiwar kungiyar Sightsavers sun kaddamar da shirin raba...

Ilimi2 days ago

Hukumar Ilimantar Da Makiyaya Ta Kasa Ta Horarda Ma’aikatanta Kan Yanda Za’a Mayarda ‘Ya’yan Makiyaya Makaranta 

  By Adamu Yusuf   Hukumar Ilimantar da Makiyaya Ta Kasa (NCNE) ta shirya taron horas da ma’aikatan ta kan...

Labarai2 days ago

NCAA ta Yaba wa Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi Bisa Kyakkyawan Tanadin Aikin Hajji

Daga Sani Dutsinma Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta yaba da kokarin Hukumar Jin Daɗin Alhazai...

Labarai2 days ago

Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 45 a Katsina

Rundunar sojin Najeriya ta kashe ’yan bindiga 45 a wani mummunan artabu da aka yi a yankin Danmusa na cikin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kebbi Ta Bukaci Malamai Su Yi Wa’azin Zaman Lafiya

Gwamnatin Jihar Kebbi ta karyata zargin cewa gwamnatin Gwamna Nasir Idris ba ta taka rawar gani wajen bunkasa harkokin addinin...

Labarai2 days ago

Ranar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata

Kwamishinar Harkokin Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman ta Jihar Kano, Amina Abdullahi, ta bukaci masu ruwa da tsaki...

Labarai2 days ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yi Kira Da A Karfafa Mata

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bukaci hukumomin gwamnati, abokan hulda na ci gaba, sarakuna, malamai da...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Kan Lalata Kayan Wutar Lantarki a Nasarawa

Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da lalata igiyoyi da sandunan wutar lantarki...

Labarai2 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Biyu Da Ake Zargin ’Yan Bindiga Ne a Kwara

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC a Jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da alaka...

Mafi Shahara