Labarai
Matasa sun fara hakura da shan miyagun kwayoyi: – NDLEA

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kwara, ta ce za ta kara karfafa matasa su shiga wasannin motsa jiki domin rage sha da safarar miyagun kwayoyi a tsakanin su.
Kwamandan NDLEA na jihar, Mohammed Ibrahim ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da mambobin kungiyar marubuta wasanni (SWAN) a Ilorin babban birnin jihar Kwara.
A cewarsa, sun dauki matakin bayan kalubalen da ake fuskanta a baya-bayan nan na aikin ‘yan masu safarar miyagun kwayoyi a jihar.
Ya ce kamar yadda matasa ke amfani da muggan kwayoyi yana sa su kara kaimi wajen yaki da wannan mummunan dabi’a.
Kwamanda Ibrahim ya nuna damuwarsa kan zargin da ake yi na sayar da miyagun kwayoyi da da masu kula da ‘yan wasa ke yi.
Ya kuma ce hukumarsa ta samu a nasara a baya-bayan nan ne na samun hukuncin daurin rai da rai kan wani koci da aka kama yana sayar da kwayoyi ga matasa ‘yan wasa da yake kula da su.
A nasa jawabin shugaban kungiyar marubuta wasanni ta Najeriya SWAN reshen jihar Kwara, Ayodeji Ismail ya bayyana cewa marubutan wasanni suna da masaniya kan illolin da shan miyagun kwayoyi ke haifarwa.
Ya kuma bada tabbacin cewa kungiyar zata sake horas da ‘ya’yan kungiyar domin bayar da rahoton illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
COVALI MUHAMMAD RABIU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
